Sha Ukku

1.6K 223 73
                                    

Daga zaunen da take ta dan juya dan ta kalli Lubnah a lokacin da take mata magana, "Kinga ko Ramlah, zan fara wucewa da Sumayyah, Idris ma yana kasa yana jiranmu sai muje gidan, kar ya zamana amarya tazo babu wanda zai dauketa pictures. Nasan kafin ma event din ya kankama kun gama makeup din ko?" Lubnah magana take tana riko hannun Sumayyah wacce itace Assistant din Ramlah sai kuma Idris da yake waje yana jiransu. Kallon makeup artist din tayi alamar ai zatayi saurin gama matan ko?

"Kiyi hakuri fa Lubnah, wallahi duk ni naja maku wannan delay din, kinsan yanzu lokacin biki ne dakyar na baro shagona mutane ne cika fal assistants dina ma har karanci sukayi." Makeup artist dince take fiddo kayan makeup wanda zai dace da kalar fatar Ramlah tana wannan bayanin.

"Babu komai fah, karki damu Allah. Ramlah, idan kin gama kawai ki kira Rayyan, nasan ko kin kirani bai zama lallai in dauka ba. Sai kun taho." Tun suna yara Lubnah suke kawance da Zainab, dan akwai lokutan da idan ya kama lokacin zab'e sai tayi tafiyarta Maiduguri gidansu Zainab har sai su Mama sun gama hayaniyarsu komai ya lafa sannan suke dawowa. Yan uwan Zainab babu wanda bai santa ba, kamar wata yaruwa haka suka dauketa. Dama duk tazo babansu Zainab akwai motar daya ware yace ta rika hawa, to ko da bikin saida aka bata amma ganin ta taho da Rayyan kuma namiji bai saba zama waje daya ba sai ta bashi. In tana san fita saidai kawai ta kira day daga cikin direbobin gidansu Zainab din a kaita, dan babu wanda bai santa ba.

Ramlah juyawa tayi da murmushi tana kallon makeup artist, "Tayi sosai ta Lubnah, sai kallonta nake kamar ba ita ba. Amma nidai bansan me hayaniya dan Allah, kiman wacce bama za'a gane nayi kwalliyar ba dan Allah."

Dariya matar tayi ta kama fuskar Ramlah tana yan shafe shafensu na kafin a fara kwalliya, "To ke yanzu ya za'ayi in maki wadda ma baza'a gane ba? Yadda kike da kyan nan ko hoda kadai na shafa maki ai sai an kalleki ballantana. Amma bari na maki nude to, zai masifan maki kyau."

Daga haka Ramlah tayi shiru. Tunda sukazo bikin nan a hotel suka sauka dan Baban su Zainab ba karamin attajiri bane amma gidan nan nasu ya cika makil. Batasan ko wannan hotel din Rayyan ya sauka ba, dan ita rabonta da ganinshi tun ranar da sukazo. Ana kwalliyar takan iya jiyo hayaniyar yan matan amarya suna shige da fice dan kusan floor biyu kila ma fin haka aka kama masu kowa da dakinshi, Lubnah ma ce tace saidai su rika kwana tare dan tana gudun wani abu ya samu Ramlah babu kowa kusa da ita.

Koda aka gama kwalliya matar bata yarda ta kalli madubi ba. Kayanta ta mika mata tace ta shiga toilet ta saka idan ta fito zata nad'a mata lafayar. Kamar wacce aka hana koda Ramlah ta shiga toilet bata kalli madubi ba har ta saka kayan ta fito matar ta daura mata dankwali kafin ta nada mata lafayar. Bata kalli kanta ba, amma daga yanda matar ke murmushi tana kiran Masha Allah tasan tayi kyau. Bata taba irin wannan kwalliyar ba balle tace tasan yanda take mata, ita ko powder ma rabon data shafa ta manta, tun Lubnah na complain har saida ta hakura, wannan ma saida ta nuna ranta ya baci kafin Ramlah ta yarda ayi mata.

"Zan iya kallon madubin?" Ramlah ta tambaya tana dan jin kunya ga wani kyakyawan murmushi kan fuskarta.

"In baki kalli wannan kyakyawar fuskar taki ba ai babu me kallon maki ita. Masha Allah wallahi, kai jama'a kinyi kyau." Ita yanda matar tayi magana ba dariya ta bata. Amma koda idanunta suka sauka saman madubi taga matar dake kallonta saida numfashinta ya tsaya. Anya kuwa? Hannu takai saman kuncinta taga ita dindai ce, kawai ta fashe da dariya.

"Yayi kyau, sosai ma kuwa." Daga nan ta dan juya kadan tana kallon yanda lafayar ta mata kai kace kanuriyar ce itama. Sai murmushi take ita kadai. "In tayaki kwashe kayan?" Tasan babu yanda za'ayi ta tafi, dole ta kulle masu daki idan matar ta fita.

"Kira wanda zaizo ya daukekin. Kafin ya iso nasan nagama ai. Ki tayani hada kayan wai? Ai yau in bacin kina daya daga cikin photographers din bikin nan da sai ince ban yarda ko plate ki daga ba. Kinsha kyanki abunki masha Allah." Dariya Ramlah tayi ta lalubo wayarta.

Saima data natsu ta tuna sunan data mashi saving, 'Rayyan Din Lubnah' abunda ta mashi saving kenan. A ranta tayi addu'ar Allah dai yasa abunda suke fata ya faru. Ganin missed calls din Dr Aliyu da kamar ta kira sai taga an dan jima daya kirata, idan sun dawo ko hankalinta ya dan natsu ta kiraki. Rayyan din ta kira, "Hello?"

"Hello, Ramlah?" Yana fadin haka bai kara cewa komai ba.

"Umm..." sai kuma ta fara inda inda kafin can kuma ta maze kamar me confidence din da gaske. "Lubnah ce tace idan nagama makeup na kiraka ka kaini wajensu. Ban sani ba ko kana kusa da hotel dinmu."

"Ta kirani tun dazu ai, ina hotel din taku ina jiranki." Saurin mikewa tayi tsaye wanda haka yaja dan kwalinta ya kusa kwancewa.

"Shine baka kirani... ahh!" Ta danyi ihu, "Dan kwalin zai kwance!" Tama manta waya takeyi. Matar dariya tayi ta karaso inda take.

"Naji kince kar in matse maki kar kanki yayi ciwo, bari in kara maki pins din yanda zai zauna sosai." Saida ta zauna za'a gyara ta lura da wayar hannunta, saurin kangawa tayi a kunnenta.

"Innalillahi, yi hakuri dan Allah. Gani nan fitowa yanzu." Toh kawai yace kafin ya kashe wayar. Dama ta gama hada kayanta, ana gama gyara dankwalin fita kawai sukayi. Batasan wace mota bace, har matar ta shiga tata motar sukayi sallama tana tsaye sai yan juye juye takeyi can ta jiyo horn din mota.

Juyawa tayi daidai lokacin ta wani murmushi ya subuce mata saman fuska, dama tunani take inhar bata game wace mota bace to saidai ta kira Rayyan. A haka ta taka ta isa motar tana murmushi, shikam Rayyan mutuwar zaune yayi kawai yana kallonta har ta shigo matar ta zauna.

"Ina yini?" Ta furta a hankali tana kaffa kaffa da lafayarta dan idan ta kwance to saidai su kira Lubnah ta kawo agaji. Dakyar ya samu ya dauke idanshi a kanta kafin yayi ma motar giya.

Kasa daurewa Rayyan yayi dan dole ya furta, "Kinyi kyau." Juyowa tayi tana kallonshi da wani murmushin saman fuskarta.

"Dan Allah da gaske? Ni koda me kyalliyar tace nayi kyau na jita ne kawai, tunda bazata kushe aikinta ba. Amma nima naga kamar yayi, amma sai naga kamar a idan sauran mutane zaiyi wani iri." Yasan heavy makeup ya dade da zama ruwan dare a wajen yan mata har ma wasu matan auren, amma tsakani da Allah bai taba ganin wacce ya taba yima balain kyau ba kamarta. Ji yake kamar yayi parking kawai yaita kallonta.

Dan mazewa yayi ya girgiza kai a hankali, "Baiyi komai ba fah, yayi sosai." Shi me zaice mata, sai yan kalle kalle take jikin side mirror tana juya fuska taga ko akwai wani waje da yake bukatar gyara, sai kace idan taga wajen iya gyarawa zatayi.

"Kalle kalle me kike?" Ya tambaya daidai lokacin da suka tsaya fikin traffic.

Bata juya ta kalleshi ba tace, "So nake inga ko wani waje baiyi ba, banso mutane suyita man wani kallo."

"To in akwai gyaran kin iya gyarawa ne?" Dan jim tayi ta juyo tana kallonshi, "Kasan kuwa ko powder banda ita cikin jakata. Bari na daina kallo kar na gano muni na." Dariya maganar ta bashi, har suka isa Rayyan yana satar kallonta ta wutsiyar ido, shidai bai taba ganin mace kamarta ba.

Dama bikin manya ba'a photographer daya, a tare suka fito motar dukda cewa ansan ba ita bace amaryar fara daukarta hoto sukayi, ita tsoro ma suka bata ta tsaya tana kallon Rayyan alamar ya ceceta. Takowa yayi har inda take yace "Muje ko?" Takawa sukeyi a tare suka shiga cikin gidan, katuwar harabar gidan a nan ne akeyin event din wushe wushe. Da hanzari Lubnah ta karaso gabansu.

Wata irin fara'a ce kwance kan fuskarta, "Ramlah?! Kinga kyan da kikayi kuwa? Innalillahi!" Yar dariya Ramlah tayi tayi hugging dinta. "Tun muna can nake fada maki kinyi kyau." Saida ta saita kunnenta kafin tayi magana, "Plan dinmu."

Lubnah najin haka ta dan bugi kafadarta kafin ta raba jikinsu. Tana dagowa taga Rayyan ita yake kallo, zuciyarta kamar ta fito waje. "Kinyi kyau." Abunda ya furta kenan. Kallonsu yake yaga sunyi kyau gaba dayansu kamar a daukesu hoto mutum yaita kallo. Amma shidai akwai wani abu tattare da Ramlah wanda baisan me yake nufi dashi ba.

"Bari naji wajen Sumayyah naji ya abubuwa suke tafiya." Tafiya take kamar wata dawisu cikin lafayarta har ta bace ma ganinsu sannan Rayyan ya jiyo ya kalli Lubnah.

"Duk yau ban ganka ba Rayyan. Ya kake?" Yar dariya yayi kafin a hankali suka fara takawa tare. Yar fira sukeyi a hankali suna tafiya har ta kaishi wajen abokan Ango tace ga amana nan a kular mata dashi, sai janta suke suna cewa kodai itama angon nata ne, dayake duk sun saba da ita. Itadai saidai tayi murmushi, a ranta kuwa fata take Allah yasa hakan ta kasance.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now