Arba'in Da Uku

1.3K 221 49
                                    

Arba'in Da Uku
Tunda akayi abun nan kullum Ramlah cikin fargaba take kwana dashi take tashi. Tsoronta daya kar Allah ya kawo ranar da Rayyan zai budi baki ya cewa Lubnah wai ita yake so. Wai so? Ita abunma tsoro yake bata, kuma shi kanshi Rayyan din tausayi yake bata.
Saura sati daya bikinsu, amma tun ranar ko idonshi bata kara gani ba. Duk tabi ta fita hayyacinta, amma ya dameta batasan inda zata saka ranta ba. Gashi tana tsoron kiranshi, idan ta kira dinma me zatace mashi? Ta kira taji lafiyarshi ko mi? Wani lokacin har kuka take cikin dare haka kawai batasan dalili ba. Burinta Allah yasa yana cin abinci kar yaje yunwa ta mishi wata illar kuma.
Sai daga baya ta gane yama daina kwana gidan gaba daya. Wani itin tashin hankali ta shiga, kila shikenan ma bazata kara ganinshi ba dan ita ko aurensu akayi batasan ya zatayi ba dan ko gidansu bata iya zuwa. Kwata kwata batasan abunda yake mata dadi ba.
Mai dilkar da Mama ta dauko daga chadi ce ta iso yau, suna zaune tare tanawa Lubnah sai sakon waya ya shigo mata. Dagowa tayi ta kalli Ramlah tunda ita dai bata da halin tashi yanzu. "Ramlah," ta kira sunanta ganin ta fada duniyar tunani. Kwana biyun nan tana lura da ita ko wanda akace yau iyayenshi suka rasu baikai Ramlah shiga damuwa ba. Komai nata ya tsaya cak ita bama ta gane kanta.
"Na'am? Kinyi magana ne?"
A hankali Lubnah ta daga mata kai, "Ramlah nasha tambayrki idan da wani agun ne dan Allah ki gaya man. Me yake damunki ne wai? Kun samu matsala da Dr Aliyu ne?"
Dan murmushi Ramlah tayi yanda Lubnah zataga da gasken babu abunda yake damunta. "Haba, ko dazu bakiga ya biyo ba shifa Hafsah daya daukota islamiya? Lafiya lau wallahi, kawai tunanin rayuwa nake."
Ita dai Lubnah murmushi, saboda kawai akwai mutane wajen ne ysa bazatayi magana ba. "To yanzu Rayyan yamun message wai ya shigo zai ida kwashe kayanshi saboda yan biki yanaso na bada a kai mashi snacks da lemu zai dade yana hada kayan. Ko zaki kai mashi dan Allah? Kinga ni idan nace zan bawa cikin masu aikin nan sai na tashi, kin sanshi da kyama kuma."
Wani irin faduwa gabanta tayi, da kamar tace Aa sai kuma taga menene dalilin da zata bawa Lubnah? "Okay bari na kai mashi." Jiki a sabule ta tashi ta tafi. Tana hada yan tarkacen kayan gabanta na faduwa. Wani bangare kuma na zuciyarshi yanaso ya ganshi koda kallon karshe ne ta mishi amma kuma wani bangare na zuciyar tata tana tunani me zatace mashi to?
Da sallama ta tsaya tana kwankwasa kofar. Bataji takun tafiyarshi saidai taji ya bude kofa ya juya ya tafi, "Ban dauka ma keda kanki zaki kawo ba. Shigo dan Allah ki tayani banaso dare yamun sosai ne nan gidan."
Bataso ya gane itace, dukda bataga fuskarshi ba amma muryarshi ta nuna baya cikin wata mugun damuwa. Kamar ma ya saki ranshi ya bawa kanshi hakuri. Jiki a sabule ta bi bayanshi har cikin dakin taga kaya baje ga wasu uban takardu daga gani su yake dubawa.
Zama yayi daidai kujerun, yana dagowa yaga itace saidai gabanshi ya fadi. Kasa cewa komai yayi kawai ya tsaye yana kallonta kamar yayi kuka. Kallon juna suka koma sunayi babu wamda ya furta koda A. Sai a lokacin ta lura ya dan rame, kuma kallo daya zakama fuskarshi ka tabbatar ma kanka yana cikin damuwa.
Ganin shirun yayi yawa yasa a hankali ya sauke ajiyar zuciya, a lokaci daya kuma zuciyarshi na karanto mashi cewar nan da yan kwanaki shida Ramlah saidai kallo. Soyayyarta ma a cikin zuciyarshi zunubi ne. A hankali ya dauke idonshi daga fuskarta yana kallon tarin takardun dake gabanshi, "Gaba mukeyi ne?"
Ramlah batasan dalili ba sai taji hawaye sun tarar mata amma haka ta danne su. Tayi kewarshi bama yar kadan ba, tunda ko ba komai Rayyan abokinta ne. Saida ta hade wani irin yawu dan ita ji tayi ma ko tsayuwar bata iyawa tukunna ta samu waje ta aje tray din data kawo.
Bata zauna ba dan bata da niyyar hakan, saboda ta gama tabbatar ma kanta in har ta zauna to babu abunda zai hana hawayenta zuba. "Ina yini?" Abunda ta furta kenan ba tare data jira komai ba ta juya zata tafi.
"Bake ta turo ki tayani hada kayan ba?" Addua yake Allah yasa ta dawo ta zauna. Koda zaman karshe ne ya zamana sunyi tare. Yasan wani ciwo hakan zai tada mashi amma da ace sun rabu haka ya gwammaci daga baya yaji azabar.
Duk yanda Ramlah taso ta tsaida hawayenta saida suka zubo. Tanaso ta juya ta tafi amma kuma zuciyarta tanasan koda ganin karshe ne ta mishi. Juyowa tayi daidai da hawayenta na zubowa, "Banaso nayi hurting dinka ai, kuma kace ganina ma azabtar da zuciyarka yake ko?"
Yana zaunen shidai yana kallonta. A karo na farko yanda take kallonshi kuma hawayen nata na sauka a hankali Rayyan yaga abunda bai taba gani ba a cikin idonta. Amma yasan hakan ba wani amfani zai mashi ba. Kwana biyar kawai ya rage a daura mata aure da wani shima kuma da wata.
"Dukda azabar, inaso na ganki." Saida ta share hawayenta ta samu waje ta zaune ga tulin takardu a tsakaninsu. Kallonta yayi idanunshi har sunyi ja tsabar yanda wani irin kunci ya mamaye mashi zuciya. Shi baima san inda zaisa kanshi.
Share hawayenta tayi ta dago, "Akwai wadanda za'a ware ne ko duk waje daya suke?" Takardun da zai aika Lagos ya nuna mata wanda sune zata ware sai wanda zai aje wajenshi a gida sai wanda zai maida office.
Dukda cewar Ramlah tana sane da idanunshi dake kanta haka ta daure ta cigaba da aikin dake gabanta. Can dai da taji idanunshi a kanta sunyi yawa ga ita kuka ma ke cin zuciyarta yasa bata dago ba ta furta, "Ka daina kallona haka nan mana."
"Kallon naki ma bazan iyayi ba? Kwana nawa ya rage kallon naki ma ya zame man haram?" Maganar da yayi har kasan zuciyarta. Dagowa tayi a hankali ta kalleshi, a nan ne taga hawaye na sauka saman kuncinshi.
Kallonshi ta tsaya tanayi tanajin yanda zuciyarta ke wani yamutsawa kaman zata fito waje. Bai fasa kallonta ba kuma har lokacin hawayen nashi basu daina fita ba. "Rayyan ya kakeso nayi da raina?" Takure hawayenta takeso tayi amma duk yanda takeso tayi ta kasa dole suka sauka.
"So nake ranki ya soni, Ramlah. Bansan ya zanyi ba, zuciyata zafi take man ji nake kaman zan mutu saboda ke." Batayi kokarin share hawayenta ba dan tasan bazasu daina zuba ba. "To ai aure zanyi, zanso wanda ba mijina bane? Kaima aure zakayi, Lubnah bata kamaci haka daga wajenka ba."
"Auren ne banaso kiyi. Ramlah ki taimakawa zuciyata dan Allah." Kuka ta fashe dashi, ta rasa ina zata saka zuciyarta taji sauki a ranta. "Idan banyi aure ba haka kakeso naita zama? Tunda mu dukanmu munsan bazan taba auren ka ba. Kuma ana aure ne idan da soyayya to ni kuma Aliyu nakeso ko?" Abunda take fadawa zuciyarta kenan tun ranar daya furta mata yana santa. Batasan ya kawo mata rudani cikin alamuranta.
Girgiza kai yayi a hankali, "Amma kuma ni ke nakeso kuma na tabbata a zuciyarki baza'a rasa sona a ciki ba."
Kallonshi tayi wani shekeke. Mikewa tayi tsaye shima ya mike. "Ban gane abunda kake nufi ba. Na soka nace naso wa, Rayyan? Wai ko ka manta abunda ke tsakanina da Lubnah? Ko ka manta wacece ita a rayuwata da kuma irin rayuwar data taka a kaina? Idan na soka son amfanar dani zaiyi? Idan ka manta yanda na dauki Lubnah sai na tuna maka."
"Ban manta ba, ina sane da wacece ita a rayuwarki kuma da yanda kuke kaunar junanku. Amma ya kikeso nayi? Shin kinaso ne na auri Lubnah naje nida ita babu wanda zaiji dadin rayuwar auren? Tana sona, amma nikuma ke nakeso. Da mijin da baya kaunarta kikeso ta rayu? Duk yanda kika kai ga san Lubnah ta samu farin ciki bazata taba samunshi dani ba, saboda ke nakeso ba ita ba!" Tas! Kakeji ta wanke shi da wani lafiyayyan mari.
Saida ta mareshi kuma ta tsaya tana kallon hannunta, duk inda hankalinta yake yakai karshe wajen tashi. Kuka ta fara a hankali ta daga kuma tana kallon yanda yayi tsaye yana kallonta. Takawa tayi taje inda yake, a hankali duk tabi ta rude ta rike fuskarshi tana juyawa alamar taga idan taji mashi ciwo ko kuwa.
Hannayenta rike da fuskarshi ta dago tana kallonshi idanunsu cikin na juna. "Da zafi? Kaji ciwo? Sannu, bansan ya akai ba na mare ka." Kuka take sosai, ita dai burinta yace mata baiji ciwo ba, gaba daya ta gama fita hayyacinta dan bata taba dauka wadannan hannayen nata zasu iya marin Rayyan ba. "Kamun magana ba, ko muje asibiti?"
A da lokacin dayaji saukar tafin hannunta saman kuncin shi, bai taba jin zafi da radadi irin wanda yaji a cikin zuciyarshi ba. Amma kuma yanzu data nuna tashin hankali sai yayi farin ciki da hakan, dan idan bacin haka ta faru da bazai taba ganin abunda yagani cikin idonta da kuma actions dinta ba.
Hannayenta dake kan fuskarshi ya sauke, Ramlah ta dauka wani abun zaiyi sai taji a hankali ya janyota zuwa jikinshu ya rungumeta. Kokarin zarewa taki ya kwantar da kanshi saman kafafarta. "Kina sona, Ramlah." Wani irin duka taji zuciyarta ta mata, ko kafin tayi magana taji saukar hawayenshi a bayanta. Zuciyarta taji ta karaya, maganar da yayi ta karshe tana mata amsa kuwwa. Shiru tayi ta kwanta saman kirjinshi tana kara fashewa da kukan.
Idan da bai furta hakan ba, bazata taba lura da cewar hakan bane. Amma ko a hakan ba ma bazata taba yarda balle ta nuna mashi. Tana sane da irin wahalar da zasusha da kuma rashin amfanin hakan a yanzu. "Bana sanka, Rayyan. Banso ka a daba yanzu ma bazan soka ba yanzu." Bai saketa ba itama bata sakeshi ba. A haka a rike da juna suka sha kukansu har suka godema Allah. Kowannen su yasan abunda Rayyan ya fada gaski ne, amma basuso su amince da hakan saboda babu abunda hakan zai kara masu sai kunci.
A hankali ya raba jikinshi da nata yana kallon yanda tasha kuka. Hawayen dake kan kuncinta ya share mata kafin ya sakar mata dan guntun murmushi. "Kukan ya isa haka, kinji?" Dan daga mashi kai tayi, "To kaima ka daina."
Gaba daya ya saketa yayi taku biyu baya, wanda hakan yana tabbatar ma junansu daga wannan lokacin har zuwa karshen rayuwarsu dole wannan tazarar ta kasance tsakaninsu. Wanke fuskokinsu sukayi suka dawo suka zauna.
A hankali suke aikin kowa da abunda yake sakawa a ranshi. Dagowa yayi ya mata murmushi, koba komai su rabu lafiya. Shi yanzu ganin soyayyarshi da yayi cikin idanta ya rage mashi wani radadin da yakeji cikin ranshi. "Baza suce kin dade ba? Ko kije kawai na ida?"
"Kuma fa dilka za'a man. Amma da saura ai bari na tayaka ko kadan ne sai ka karasa."
"Wa za'awa dilkan?" Da yar harara tace "Mijina, bakasan anawa amare dilka ba?"
"Anwa Lubnah?" Kiran sunan Lubnah yasa Ramlah tayi murmushi, "Ita akewa dazu ai, bakaga kyan da tayi ba kaman ka saceta." Shiru sukayi na dan lokaci kafin Ramlah ta kara da, "Ka kular mani da ita dan Allah. Tana sanka, a hankali kaima zaka koyawa zuciyarka santa. Ka bata dukkan farin cikin da take bukata, dan Allah."
"Kin sadaukar mata dani kenan?"
Ramlah yar dariya tayi tana girgiza kai, "Aa, ban sadaukar mata da kai ba, dama tun asali kai din nata ne, Rayyan."
*
Tun bayan fitar Ramlah da baifi minti goma ba Dr Aliyu ya kira wayarta. Lubnah ce ta fito dan ta kawo mata, kawo yanzu tafi karfin awa daya tsaye tana sauraren duk abunda suke furtawa, nata hawayen kuwa tun tana sanin saukarsu yakai zuwa suke kawai ba tare data san suna sauka ba.
Bataso suji alamar tana wajen, cikinsu ko daya bataso yasan taji wannan abun. Da kyar take daga kafafunta har ta koma cikin gida. Me dilkan kawai ta kira a waya tace mata Ramlah batajin dadi bazata iyayi yau ba. Dakinta ta rufe ta fara wani irin kuka mai taba zuciyata. Batasan ya zatayi ba, ina zafa saka kanta? Ita soyayyar da take mashi ina zata kaita?

Wayyo Allah💔

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now