Arba'in Da Biyu

1.3K 212 16
                                    

Arba'in Da Biyu

Tun daga ranar Rayyan bai kara bi ta kansu ba. Koda Lubnah ta mashi magana nunawa yayi Ramlah sai tafi saurararta. Abun duniya duk yabi ya dameshi gashi yanzu biki saura sati biyu kuma har yanzu ba'asan inda suka dosa ba. Jiya koda ya dawo gida yaga motar Dr Aliyu amma shikam baibi ta kansu yayi shigewarshi bangarenshi.
Yana wajen aiki yaji karar wayarshi, koda ya dauka a hankali ya fara magana. Dan shi a yadda yake jinshi baya tunanin zai iya kaiwa sati biyun nan bai mutu ba. "Lubnah, lafiya?" Alamar tana wajen hayaniya. Kuma shi bata saba kiranshi haka kawai ba saidai inda dalili.
Ajiyar zuciya ta sauke, "Alhamdulillah kai an sameka. Kaga ko? Gani da Ramlah office din alkali, tazo ta kawo karar Yasir din akan ya saketa. An kirashi yana hanya zaizo amma alkalin yace dole saida namiji a tare damu idan ba haka ba bazasu sauraremu ba. Na kira Dr Aliyu wayarshi kwata kwata bata shiga. Dan Allah idan baka wani aikin mai mahimmanci kazo."
Wani irin sanyi wanda baisan daga ina yake ba yaji ya ratsa zuciyarshi. "Turo man address din wajen, gani nan zuwa."
Bata kara minti daya ba ta turo mashi address din. Saida ya kulle office din da komai dan ysan bazai samu karfin komowa ba tukunna ya tafi. Sauri yake saboda ya kosa ya ganta, shi koda bazai mata magana ba ganinta kawai da zaiyi zai rage mashi wani abun a cikin zuciyarshi.
Koda ya isa wajen sai yaga waje ne babba wanda bazai iya gane office din da suke ciki ba. Sako ya tura mata akan ta fito ta shiga dashi.
Lubnah kallon sakon da Rayyan ya turo tayi, gashi suna magana da alkalin zai zama rashin kunya idan tace zata tashi ta fita. Mikawa Ramlah wayar tayi ta juya suka cigaba da magana. Ramlah sakon ta karanta sai ta fahimci abunda take nufi, tashi tayi ta fita.
Hango Yasir tayi daga can bakin kofa da alamu waya yake, gabanta na faduwa haka ta taka amma maganganun da taji yanayi yasa tayi tsaye cak. "Nusaiba, ki kwantar da hankalinki dan Allah. Husnah zata samu lafiya, na fada maki da izinin Allah. Yanzu abunda nakeso ki fahimta shine bawai zan dawo da Ramlah bane dan ina santa ko dan wani abu, saboda matsalar da likita ya fada mana. Bone marrow din da ake nemawa Husnah dole sai ba dan uwanta jini daya, ke kuma an tabbatar mana bazaki kara haihuwa ba. Ya kikeso nayi? Munaji muna gani mu rasata? Data haihu na maki alkawari zan saketa shikenan mun rabu kuma har abada."
Ramlah ji tayi kasar da take takawa ma bazata iya daukarta ba. Wani irin numfashin tashin hankali taja ga wasu mugayen hawaye da suka balle mata. Juyowa yayi cike da tashin hankali yana kallonta a tsorace. "Ramlah..." nema yake yayi magana amma ta tsaida shi.
"Naji komai, kuma na fahimci komai, Yasir. Dama saida ya fada man. Yanzu dai saboda diyarka ta rayu zaka maido dani, idan na haifa maku da sai kuma ka rabu dani. Wannan wace irin wahalalliyar rayuwa kakeso nayi dakai?" Share hawayenta tayi, koda yazo zai kara magana ta tsaida shi. "Abunda baka sani ba shine koda aka kira ka anan ba wai dan sasantawa bane ba, sakina zakayi. Kuma in Allah ya yarda nida kai har abada. Koda zan mutu ban kara aure ba hakan zai fiye mani zama da kai." A hankali ta fara takawa, shi kuwa kallonta yke kamar idanunshi zasu fito alamar tashin hankali. Juyowa tayi tana share hawayenta, "Kuma ka sani bazan taba yafe maka ba. Sannan diyarka bazanyi fatan ta mutu ba, amma ina rokon Allah yasa kaji koda rabin azabar danaji ne lokacin da Hanan ke raye."
Tunda ta fita ta hango motar Rayyan take wani irin wahalallen kuka. Rayyan bai lira da ita ba saida tazo ta bude gaban motar ta shiga ta dora kanta saman cinya tana kare fashewa da kuka.
"Wai saboda kada diyarshi ta mutu yasa bazai rabu dani ba. Suna neman bone marrow din dan ubanta kuma matarshi bazata kara haihuwa ba. Idan na haifa mashi dan sai ya sakeni!" Numfashinta har wani sama sama yake tana magana kamar zuciyarta zata tsaya waje daya. Ashe dama sakara ya dauke ta, yana nuna mata ya damu da Hanan ashe duk karya yake. Yar wahala ya maida ita.
Rayyan kasa ce mata komai yayi, kallonta kawai yake tana kuka kamar ranta zai fita har ta gaji ta dago tana kallonshi fuska shabe shabe da hawaye. "Ki wanke fuskarki mu shiga. Yanzu sai ayi komai a gama, idan yaso daga baya sai muyi magana, kinji?"
Ruwan dake tsakanin kujerun ta dauka ta wanke fuskarta sai ta fita motar gaba daya. Shima fita yayi suka fara takawa a hankali, wani tukukin bakin ciki ne ke cin zuciyarta har suka shiga office din alkalin a nan suka tarar dashi shima zaune.
Zama sukayi suma a nan alkalin yake tambayar komai, duk amsar daya bada akan dalilin abunda ya mata sai Ramlah taji kaman ya soka mata mashi cikin zuciya. Duk abunda yayi ba dan komai bane sai dan kaunarta da bayayi. Zama da ita ba karamin cutar da zuciyarshi yake ba kuma yanada wadda yakeso. Shine ya shirya mutuwar karya da taimakon abokinshi likita.
Da aka tambayeshi me yakeyi a maiduguri da sunan Yassar sai yace iyayen Nusaiba ita kadai suka haifa. Kamfanin babanta yake aiki yanzu kuma sune suka bashi new identity da duk abunda yake bukata.
Karshe da aka bukaci ya saketa yace bazai iyaba. Ramlah har ta bude baki zatayi magana Lubnah ta riko hannunta ta tsaida ta. Alkalin saida ya tabbatar mashi zasuyi suing dinshi da laifuka masu yawa mafi girman ciki shine karyar mutuwar da yayi da kuma chanja identity ga watsar da iyalenshi wanda hakan har ya haifar da rashin tilon yarsu. A nan take ya tabbatar mashi zai kira yan human rights wanda inhar case din ya shiga hannunsu to tabbas zai karasa rayuwarshi a gidan yari kuma banda tarar da za'aci shi, bayan haka kuma Alkalin yanada hurumin sakinta da kanshi.
Dakyar kamar zaiyi kuka ya furta, "Na sakeki, saki daya." Runtse idanunta tayi tanajin wani irin abu yana sokar mata zuciya daga wani gefen kuma kaman an kwara mata ruwan sanyi haka takejin kanta.
Har aka gama abunda za'ayi Ramlah batace komai ba, hawayenta kuma sun tsaya cak kamar an dauke wuta. Shi ya fara barin wajen, koda suka sauko sai Lubnah tayi hugging dinta. "Zan dawo da wuri kinji? Yanzu anata kirana kar nayi laifi can."
Daga mata kai kawai tayi dan gani take idan ma tace zata bude baki tayi magana to tabbas hawayenta sai sun kusa ambaliya da kaf garin Abuja. Motarshi ta shiga babu magana ta zauna. Tunda ya fara tuki babu wanda yace da dan uwanshi kala har ya isa gidan. Motar Mama bata nan, wanda hakan kadai alama ce ta bata gidan.
Ramlah tana jira taji ya mata magana taga ya fito daga cikin motar yana neman yin gaba ya tafi wajenshi. Tsayawa tayi tana kallonshi har ya bace da ganinta, wani kududun bakin ciki ne ya tokare mata zuciyata. Ita sai a lokacin ma ta lura fushi yake da ita, ko kallonta bayayi balle ta saka ran zai mata magana.
Neman natsuwarta tayi ta rasa. Cikin gidan ta shiga ta saka wancan ta fidda wannan amma kwata kwata ranta yaki ya mata dadi. Karshe dai dataga ko tunanin Yasir dinma da sakin daya mata ta kasayi yasa ta daura dan kwalinta ta nufi bangarenshi.
Bata tsayawa kwankwasawa ba ta bude kofar falon ta shiga. Nan ta ganshi zaune ya dan kishingida, idanunshi rufe amma ba sai an fada ba tasan ba bacci yake ba. Ko takalmi tunda ya shigo bai cire ba. Tsaye tayi tana kallonshi ranta yana kara baci, ita gara suyi fada kaca kaca akan wannan shirun da yake mata. Gudunta ma yakeyi tun ba yanzu ba ta lura, abu indai akwai ta ciki to tabbas duk yanda zaiyi ya zare kanshi to tabbas zaiyi.
A hankali ya bude ido yana kallonta, ji yake kaman yayi kuka. Yanzu da yaga zahiran Yasir ya saketa yasan bata da miji sai Dr Aliyu. Gyarawa yayi ya zauna lafiya lau, "Lafiya? Ko akwai wani abu ne?"
Maganar ma haushi ta bata, "Miye hakan kakeyi wai? Idan wani abu na maka Rayyan ai fada man zakayi ba wai ka zauna kana fushi dani ba ko?" Tsayawa yayi yana kallonta, shi data barshi da abunda yakeji dukda abun yafi sauki, dan yanzu dukda yanaso ace yana ganinta kuma suna magana sosai da abun duk sai yafi mashi sauki.
"Yaushe nace ina fushi dake?" Tsayawa tayi tana kallonshi can kuma sai ga hawaye. Batasan ya akayi ba ta tsani wannan shirun da yake mata, yanzu ma yanda ya mata kadai ya isa ya tabbatar mata da cewar tabbas fushin yake.
"Idan babu abunda zakice dan Allah ki tafi, bacci nakeso nayi." Maganar nan ba karamin kuna ta mata ba a zuciya. Da tayi shiru can kuma ta furta, "Na maka wani laifi ne? Ko kuwa sakin daya mun ne bakaso ba kafi so kaga ina zaune ina rayuwa da wanda zai zalunce ni?" Tana share hawayenta take maganar.
"Aa, naji dadi daya sakeki Ramlah amma me hakan zai amfanar dani? Babu. Dan Allah ki tafi, ganinki kadai azaba ne a zuciyata Ramlah." Shima kallonta yake kamar zaiyi kuka. Gata din dai, amma ta zame mashi haramiya. Na farko yasan ko zai mutu Ramlah bazata taba amincewa da soyayyarshi ko dan Lubnah, na biyu kuma tasha fada a gabanshi cewar Dr Aliyu takeso.
Idanunta kamar zaau fado take kallonshi, "Azaba kuma, Rayyan? Ni kuwa me na maka haka da har ganina zai zame maka azaba?" Zuwa yanzu kasa tsaida hawayenta tayi, wani irin zafi da bata taba jinshi a ranta ba takeji.
"Nidai dan Allah ki tafi. Wallahi Ramlah ganinki wahala yake bani." Mikewa yayi tsaye alamar bukatar ta tafi din itama hankali a tashe ta mike, ga hawayenta da ke zarya saman kuncinta. "Kuma ki daina wannan kukan dan Allah, kina kara azabtar dani Ramlah."
Da masifa ta fara magana ga kuka, "Wai sai maganar azaba kake, me na taba yi maka? Me na tsare maka Rayyan ta ina nake azabtar dakai nikam?!"
"Kina azabtar dani da soyayyarki! Na fara sanki bansan lokacin dana fara ba yanzu kuma shine silar daukewar farin cikina. Ya kikeso nayi? Shin rashin ganin naki ma dukda shima wata azabar ce bazan samu ba? Dan Allah ki tafi wallahi ni kadai nasan azabar da nake sha."
Taku biyu tayi baya taji kaman zata fadi. Kalmominshi wata irin amsa kuwwa suke mata cikin kunne. Kallonshi take kamar yau ta taba ganinshi a lokaci daya kuma zuciyarta sai wani irin bugawa take. "Ban gane ba. Anya kana cikin hankalinka kuwa?"
"Na sani, bana cikin hankalina dan na tabbata soyayyarki a zuciyata wata fannin azaba ce da jarabawa daga ubangiji." Jajayen idanunshi yasa cikin nata yana kallonta da tarin kuncin dake cin zuciyarshi. "Ina sanki, Ramlah, amma nasan bazan taba samunki ba."
Wuri ta samu ta zauna, hawayen nata ma kasa zubowa sukayi, gaba daya jikinta yayi sanyi, da kyar ta samu bakinta ya furta. "Saboda me, Rayyan? Akan me zaka bari ka aikata wannan abun? Na shiga uku ni Ramlah. Dan Allah ka rufa man asiri."
"In baccin kinzo kin sameni nan bazan taba furta maki hakan ba. Yanzu ma da kikaji kina iya nuna kamar baki taba ji ba. Ki tafi kawai ki barni da abunda yake raina, Ramlah. Jarabawa ce daga Allah kuma na dauka hannu biyu." Sai yanzu ta gane duk inda damuwarshi ta dosa tun ba yanzu ba. Tausayi taji ya bata amma kuma hankalinta a tashe yake.
"Dan Allah karka bari kowa yaji. Dan Allah, bansan me zance ba, bansan me zanyi ba. Rayyan, na bani." Lubnah kawai take tunani, "Lubnah fah? Dan Allah kace man kana santa itama." Idan yana santa to duk abun zaizo da sauki, bayan aurensu zai manta da ita.
"Ke kadai nakeso, Ramlah. Kuma ke din zan cigaba da so har karshen rayuwata." Tashi yayi ya tafi daki ya barta nan tana fashewa da wani irin wahalallen kuka. Wai meyasa ita dai bata taba zama haka kawai ba? Daga wancan sai wannan? Ta ina Rayyan zai fara santa? Ya akai har yayi nisa haka? Me zatace ma Lubnah? Wannan wace irin jarabawa ce?

Duk mai son shiga whatsapp group tayi message ta whatsapp ga 08132526951 za'a sakata.

TeamRR🥺

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now