Karshe.

2.3K 237 62
                                    

BAYAN SHEKARA DAYA.

Wakar yara ke tashi daka nufo gidan, juyawa tayi suka hada ido tana dariya shikuma ya dan bata fuska. "Wai Rayyan na bani, nace maka fa ni lafiyata lau dan Allah ka saki ranka, gidan mutane fa zamuje." Kauda kai yayi yana tukin kamar bai san yi, a yanda ya kamata da tuni sun ido gidan amma saboda yanda yake tukin kamar yana tsoron taba steering wheel din motar yasa sai yanzu suka iso. "Jiya fa muka dawo Ramlah, keda bakinki kikace mararki na ciwo, ki kwanta ki huta ne bazaki iya ba?" Yi tayi kamar bata jishi ba ta dauka camera dinta tana hadawa, dan so take komai ta dauka. "Allah naji sauki, ka gani, taba ma kaji har motsi yanayi kuma lafiya lau." Hannunshi ta jawo ta dora saman cikinta wanda a yanzu watanshi shida. Ya fito tayi gwanin kyau da ita. Akaci sa'a kuwa daidai lokacin baby ya motsa a tare sukayi yar dariya kamar wannan ne karo na farko.

Gate aka bude masu suka shiga, sai murmushi take dan so take taga ya Lubnah zatayi. Kamar yanda Lubnah ta rad'a wa baby sunan Ramlah, amma yanzu Hanan suka ce mata. Duk yanda Ramlah taso kar a saka sunanta fir Lubnah taki yarda wai ita ala dole sai ta mata takwara. Dan daga farko ma dataji wai diyar Ramlah ta rasu cewa tayi a bata tata, yin hakan ba karamin kuka ya saka Ramlah ba kuma ya tabbatar mata da abunda tayi shine daidai. Wato ita a yanda take san diyarta amma tanajin ance ta Ramlah ta rasu har ta sadaukar mata da ita. Da Ramlah tayi fur tace bataso shine ta saka sunanta kuma ana kiranta Hanan.

Watansu daya da haihuwa Rayyan yayi signing up for wani course a Instanbul, ita Ramlah tasan in baccin abunda ya faru babu abunda zaisa yayi joining course dinnan, amma sai yace mata wai she needs some time away from kowa kuma kila ganin Baby Hanan zai iya sakawa taji rashin dadi, tasha fada mashi ita wallahi ta fidda yarinyar a zuciyarta, kawai kallon diyar Lubnah take mata kuma har abada haka ne amma haka suka tafi. Yau ake birthday din Hanan na shekara daya, tunda suka tafi basu kara ganinta ba sai video call, babu ma wanda yasan sun dawo saidai suyi suprising kowa.

Fitowa sukayi daga motar hannunsu hade dana juna. Daka ganta zaka san tanada ciki dukda ba wani mugun girma yayi ba. Wani ihu aka rangada, "Ammi!!! Wayyo, Ammi ki fito ga Ammi tazo!" Sai Ramlah kawai ta fashe da dariya, dan cikin su biyun batasan dawa Hafsah take ba. Da gudu ta rugo ta rungume ta. Kasancewar wakar yara na tash a garden din gidan inda nan ake birthday din Lubnah bataji ba har saida suka zagaya, tana kan nunawa photographer yanda takeso ya dauki hoton ta tsaya tana dan guntun tsaki.

"Ni bansan yanda zan maka ka gane ba, bari na kira Ramlah kila idan ta maka bayani zaka fahimci abunda nake nufi." Ta furta tana laluben wayarta. Ta baya Ramlah ta rungumeta tana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarta, "Ai gani nazo, ni zanwa diyata hoto da kaina ba sai kowa ya tayani ba." Da farko Lubnah ta dauka ko tunani takeyi, amma jin da gaske mutum ya rungumeta yasa tayi tsalle kamar wata yarinya, dukda mutanen dake wajen bai hana ta juyo ta rungume Ramlah ba sai hawaye.

Dariya sukayi suna kokarin tsaida kukansu. "Yaushe kuka dawo? Oh Allah Ramlah nayi kewarki!" Kara rungume juna sukayi sai a lokacin idanun Ramlah suka sauka akan Hanan wacce Hafsah kewa wasa sai kyalkyata dariya suke. Murmushi tayi ganin kamanninta dana Hanan sun fito zagwai tana karawa Allah godiya akan ni'imomin daya mata ta sanadiyar Lubnah.

Duk yanda Lubnah taso Ramlah ta zauna ta natsu saidai ta hakura, dan kuwa shi dama Rayyan ciki ya shiga suka zauna shida Dr Aliyu suna firar yaushe gamo. Hotuna kam tayi masu shi bila adadin. Birthday party akayi sosai yara sukasha wasa da dariya kamar kar ya kare. Sai yamma lis iyaye suka fara daukar yaransu sunawa Lubnah sallama, da godiya ta rika basu gifts din da aka hada tana masu sallama. Kafin maghrib tayi kowa ya watse sai su suka shiga cikin gida.

Kuka Hanan keyi dan dama ita idan har taji yunwa to hankalin kowa sai ya tashi. Lubnah ta bata nono amma kwata kwata taki amsa saboda zuciyar da tayi dan saida ta jima tana kuka kafin Lubnah ta gama sallah. "Karbarta Ramlah dan Allah, bari na hado mata abinci. Wannan masifarta sak irin taki." Itadai Ramlah dariya tayi tana karbar ta, "A daina saka mana ido, wannan masifar tamu arziki ce ko me sunana?" Dagata tayi tana mata wasa tun tana kuka har ta koma tana dariya.

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now