Arba'in Da Takwas

1.3K 221 25
                                    

Tun Rayyan yana ganin abun a matsayin wasa har ya zamana yana gani zahiran ba bad'inan ba cewar babu Ramlah. Hankalinshi idan yakai kololuwa to ya tashi, shi tunanin shi ma ko Katsina ta tafi? Kwana biyu kenan yau amma babu labarin ina zai ganta. Kusan duk bayan minti talatin sai Lubnah ta kirashi, itama tun tana kuka har ta hakura, dukansu sun zauna sun zubawa saurautar Allah ido.

A bangaren Ramlah kuwa tana can gida tana sheke ayarta. Babu abunda take illa tayi bacci, taci abinci sai tayi sallah, idan ta gaji ne take kunne kallo a laptop dinta wani sa'in yanayi zata bingire da baccin sai ta farka tukunna ta kasheshi. Kullum sai ta bawa mai aikin nan kudi duk dan kar ta tona mata asiri. A wani bangare na zuciyarta tanajin yanda batayi wa kowa aldalci ba, musamman Lubnah domin kuwa zatayi tunanin da batayi abunda tayi ba da har yanzu suna tare, saidai yin hakan shine kadai zai tabbatar ma Rayyan cewar bafa ta sanshi kuma bazata soshi ba.

Rayyan yana falo ya dan kishingida, shi ba tunani ba kuma shi baiyi baccin ba gaba daya. Domin kuwa rabonshi da bacci tun ranar data tafi. Wayarshi ce tayi kara, dubawa yayi yaga Mama ke kira a hankali ya dora saman kunnenshi, shi in baccin sunce babu wanda suka sani nata a Katsina ai da can ya tafi ya nemo ta, amma idan ya tafi Katsina wajen wa zaije? wace unguwa ma zaije?

"Assalamu Alaikum," sai yanzu ya duba yaga lokaci a agogo wajen karfe sha biyu saura yan mintuna, to kodai sunga Ramlah shiyasa aka kirashi? "Hajia ina yini?" ya furta murya can kasa domin kuwa shi kadai yasan yanda yakeji a ranshi.

"Lafiya lau, Rayyan. Nasan dare yayi amma kazo gida ina neman ka." Dut ta kashe waya, amma daga gani ranta ba karamin baci yake ba. Ko minti daya bai kara ba cikin gida ya tafi, a ranshi kuwa addu'a yake Allah yasa an ganta, shi baima san me zaiyi mata ba. Yau da baisan halin Ramlah ba sai yace sace ta akayi, amma dayake sarai ya santa yasan me zata iya.

Bai shiga da motar gidan ba dan baiga amfanin hakan ba, tunda fitowa zaiyi kuma ya tafi gida. Mama ya samu zaune falo ta lula cikin duniyar tunani, shi tunda akayi auren basu hadu ba, dan Lubnah ya fadawa akan ta fada mata,  sai yanzu yakejin kunya duk abunda ya faru, kwata kwata yama mance da hakan kafin yazo. Zama yayi a kujera mafi nisa da tata. "Mama ina yini?"

Saida ta sauke ajiyar zuciya tukunna tace, "Lafiya lau, Rayyan. Na tadoka cikin dare ko?" Mika mashi waya tayi, amsa yayi yana juyawa alamar me zaiyi da ita, "Wayar mai aikinmu ce, naje dakinsu zan sakata aiki naga number Ramlah na kiranta, ina dauka naji tana fada mata akan ta kawo mata abu. In takaice maka dai Ramlah duk kwanakin nan tana gidan nan, dakinta." Wani irin yawun bakin ciki da takaici ya hadiya, yau ko abunda yafi so yakewa Ramlah tabbas sai ta gane kurenta.

Da hanzari ya mike har wani huci huci yake, yar dariya Mama tayi, "Kai ka biman diya a hankali kaji, bansan wannan saurin fushin naku. Karbi ga makullin dakin nan, bansan ko a kulle yake ba dan ban nuna nasan tana ciki ba." Dan sosa keya yayi ya karba yana mata godiya, "Ka dauketa kawai ku tafi, zan kiraku zamuyi magana idan gari ya waye." Saida ya jira har ta shige dakinta, yanajin karar makulli ta kulle alamar ma bata bukatar jin yanda suke tattaunawa dan tasan dole akwai masifa kafin Rayyan ya hau benen, biyu biyu yake bi har ya tsaya bakin dakinta.

Dan kwankwasawa yayi, Ramlah dake kwance bacci ya kwasheta ga system dinta tana kallo sai wani biscuit da yake tsohuwar ajiya ta fasa ta fara ci ta aje sauran. Jin bata amsa ba yasa ya saka key din kofar ta bude, cikin sa'a kuwa batabar makulli jiki ba. Wutar dakin ya kunna nan da nan haske ya gauraye ko ina, ganinta yayi cikin bargo hankalinta kwance, ga sanyin AC ga system dinta da har yanzu tana magana alamar film din bai kare ba. Yanda tayi hankalinta kwance kai ka dauka bata taba yin wani laifi ba a rayuwarta.

Tsaye kawai yayi ya harde hannayenshi saman kirjinshi dan yanda yakejin zuciyarshi na suya idan yace zai tadata da magana baisan wace irin kalma zai furta mata ba, idan yace kuwa zai dan bugeta ta farka ne zata iya mashi maganar da zai maketa ma baisan yayi ba. Ramlah kuwa duk yanda take bacci aka kunna wuta sai ta farka, a hankali ta fara bude ido tana yamutsa fuska. Saida ta tsaida film din kafin ta dago a hankali, "Tun dazu na kira baki dauka ba, kin hado man custard din?" Bata lura da waye tsaye ba tana magana har ta tashi zaune tana kara janyo bargon jikinta alamar sanyi takeji, "Kuna na fada maki bansan ana kunna man wuta."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now