Ashirin Da Biyu

1.3K 192 4
                                    

A daren ranar tare suka ci abinci da Lubnah, babu yanda Rayyan baiyi ba amma ko kadan Ramlah bata kulashi ba. Karshe ma gajiya yayi ya tafi bangarenshi su kuma suka koma sama dakin Lubnah. Gyara zama Lubnah tayi tana kallon Ramlah da guntun murmushi kan fuskarta, "Wai ni Lubnah ban gane wannan murmushin da kikata yi tun dazu ba. Halan wani abu ya faru dazu da rana?" Dariya Lubnah ta fashe da ita tana daga mata kai. Nana da nan kamar an kunna radio haka ta fara bata labarin abunda ya faru tsakaninsu ita kau Ramlah me takeyi inba dariya ba.

"Dan darajar Allah?! Dama ya fadi gaskia da duk abun yafi sauki, kishin dai yakeyi." Tafawa sukayi, ita kau Ramlah zuciyarta fal murna dan kuwa babu abunda takeso face taga yau ga Lubnah ta samu abunda takeso wanda a yanzu bai wuce ta samu Rayyan ba. "Dama na fada maki, Allah kiris ya rage ya fara sanki. Ni ko dan haka zan daina mashi rashin mutunci to, mijin yar'uwa ai yafi wasa." Dukan wasa Lubnah ta kai mata, "Nifa wallahi banki ace yau an daura mana aure ba, ke ni wallahi..." kukan shagwaba ta fara na wasa, nan wata irin dariya da Ramlah ta fashe da ita tana dariya, "Wayyo Allah kunne na! Diyar mutane ta fada, bari dai inje in gaya ma Mama, kar ki lalace mana cikin gida."

Wani irin wawan janyowa ta mata ta fadar da ita kan gado, "Ke dallah banza, sharri zaki ja man? Ni ba aure nike so ba, shi dinne dai nikeso wallahi." Dariya suka fara tare suka tafawa. "Yanzu dai tsaya, aurenshi kikesan yi da gaske?" Ramlah ta tambaya tana murmushi, ita dai a rayuwa tana burin Lubnah ta samu Rayyan ko dan farin cikinta.

Gyaran murya Lubnah tayi tana gyara zamanta, maganar fahimta takeso suyi da Ramlah. "Kinga ko? Wallahi Ramlah ina sanshi sosai, ni banma san ya akai na fara sanshi haka ba. At first ko?" Ganin yanda tayi maganar da mahimmanci yasa Ramlah ta girgiza kai tana me kara bata dukkan hankalinta. "Ni da haushi naji lokacin da Mama tace wai zaizo ya zauna nan gidan dan mu fahimci juna, sai naga ai anma zubda man aji na. Daga baya kuma tunda yazo naga he's so nice, gashi da kyau kamar shi yayi kanshi. Sai muka hadu dake, naga yana da tausayi da mutunci sosai, toh nidai na bude ido na kawai naga ina sanshi. Ke kina ganin zai aureni, Ramlah?" Rau rau idanta yayi a lokacin da tayi tambayar. Murmushi Ramlah tayi.

"Haba mana Lubnah, ji wata magana wai kamar wata musaka? Ko musakai a zamanin nan suna samun mazan aure balle mace kamarki. Kina duba kanki a madubi kuwa? Tsaya bama wannan ba, yama isa? Wallahi zai aureki, nasan shima yana sanki, kila tsoro ma yakeji ya fadi maki ace baki sanshi. Waya tsoron tsoro." Ramlah ta furta tana dariya.

Fira suka cigaba daya cike da farin ciki da kwanciyar hankali kafin wayar Ramlah tayi kara. Tashi tayi tama Lubnah sallama sannan ta wuce dakinta, Dr Aliyu ne, har wani murmushi ya subuce mata. Zama tayi kan gadonta tana me rungume pillow dinta, "Ina yiniiii." Taja cike da muryar me kwantar da hankali. Ita dai bazata ce ga abunda takeji game dashi ba kamar yanda take ganin take taken nashi, amma dai kawai tana jin dadi idan ya kirata. Ranta yana mata sanyi idan suna fira dashi, komai nashi yakan kwantar mata da hankali.

"Ramlatu na. Ya kike?" Tabe baki tayi, amma hakan bai hana ta jin wani dadi a zuciyarta ba. Yau ce rana ta farko daya fara kiranta da 'Ramlatu na.' So take ta nuna mashi bataji sunan ba amma kuma hakan bazai yiwu ba.

"Yau kuma Ramlatu na koma? Kuma baza'a amsa gaisuwa ta ba?"

"A'a ni na isa? Lafiya lau Ramlah, ya kike ya gida?" Tana iya jiyo sautin murmushin shi. Gyara zamanta tayi tana tuno irin maganganun da Lubnah ta fada akan Rayyan wanda sune abubuwan dayasa ta gane cewar tana san Rayyan. So take taga koda ita tanajin hakan gameda Dr Aliyu.

"Lafiya lau, yau dai nayi abunda kace. Banyi kuka ba, ban bari abun ya dameni ba, kuma nayi editing pictures dayawa sosai. Nayi dariya, nayi murmushi, nayi farin ciki. A bani kyautar da akace za'a bani."

"Ah, gaskia yau Ammi ta kyauta sosai. To ai kyautar tawa tsada gareta, kin shirya amsa ko?" Yar dariya tayi, wanda har kasan zuciyarshi saida sautin muryarta ya kai mashi. Yasan yaso Fadila, wato Mahaifiyar Hafsah, amma shidai bai tabajin irin yanda yakeji game da Ramlah ba. Komai nata na daban ne, komai nata burgeshi yake kuma farin ciki yake sakashi.

"Na shirya mana, ina jinka."

Yar dariya yayi jin yanda ta zak'u, "Toh, gobe dai zan cika alkawari na, idan an tashi su Hafsah makaranta mun roki Hajia ta yarda za'a kawo maki ita ta miki weekends." Ai Ramlah bata san lokacin data mike ta daka tsalle ba tana ihun murna. "Dan Allah da gaske kake? Wayyo Hafsah ta!"

Yanda take san diyarshi, hakan kadai ya isa yasa mashi san Ramlah balle nashi dalilan na daban. "Da gaske nake Amminmu."

Mikewa tayi ta fita dakin, Kitchen ta shiga ta fara dube dube sunayi suna fira, "Yanzu tsaya, fada man duk abubuwan da Hafsah take san ci na snacks da komai ma."

Jin karar kwanuka yasa ya fara dariya, "Kardai kice man kina kitchen?"

"Eh mana, kasan yin snacks da daddare yafi dadi, kuma muna waya kafin ma na lura nagama. Kaidai kawai ka fada man." Yana dariya yana fada mata jin yanda ta takura akan ita fa lallai sai ya fada mata din. A hankali ta fara hada daya, zuwa gobe da asuba sai tayi sauran.

Tanayi suna waya tana koya mashi sai taji karar tafiyar mutum, wani irin tsoro ne ya sauko mata, gashi bata san ta nuna ma Dr Aliyu kar ya shiga damuwa tasan halinshi. "Mama ta sauko zan dafa mata wani abu, kaje kayi bacci gobe zakaje wajen aiki, kar taji ina waya." Magana take amma zuciyarta dar dar take dan yanda takejin sahun tafiyar yana gabato ta.

"Ki bata mana mu gaisa, ai na kusa zuwa na gaisheta da kaina."

"In kazo da kanka sai ku gaisa, nidai yanzu ta shigo, Bye!" Da hanzari ta kashe wayar da yar dariyarta dan kar yaji tana cikin fargaba. Frying fan din data dauko gefenta ne ta rike a hannu ta fara nufar hanyar parlour, ta daga kenan aka kunna wuta sai taga fuskar Rayyan da alamu ya fara bacci.

"Na bani, badai dukana zakiyi ba?" Tsayawa sukayi suna kallon juna ita kuwa Ramlah ta zumburo baki gaba. Ba karamar razana tayi ba yau. Da tasan shine ai da bata kashe wayar ba, kuma yanzu da kunya ta kara kiran Dr Aliyu.

"Yo tsoro ka bani ko? Kana tafiya sai sahun taku kawai akeji kuma dare yayi sosai." Ratsawa yayi ta gefenta ya wuce ya shiga kitchen din. Shi yunwa ce dama ta tada shi, dan bai wani ci abincin daren ba saboda haushin da Ramlah ta bashi sai wani shareshi takeyi.

"Me kikeyi? Dama abinci nazo nema." Janyo kujera yayi ya zauna yana kallon dough din data riga tayi. Dawo tayo cikin kitchen din ta koma wajen aikinta, tunowa da tayi ta daina yi mashi rashin mutunci saboda Lubnah yasa ta saki fuskarta. "Wai cookies zanma Hafsah, gobe za'a kawo man ita weekends. In zakaci bari na fara sakawa sai kaci first batch din."

Bata juyo ba taga irin kallon da yake mata, sai lokacin ya tuna yaji alamar mutum yana magana dama, wato da Dr Aliyu take waya kenan. Amma daya tashi bai nuna mata yama gane wacece Hafsar ba. "Wacece Hafsah kuma? Ko yar'uwarki ce?"

Juyowa tayi da mamaki kwance kan fuskarta, "Hafsah fa diyata, Rayyan."

Hannayenshi ya harde saman kirji yana kure idanunshi akan nata, itama bata dauke idanunta ba. "Oh dama kinada wata diyar bayan Hanan?"

Turbune baki tayi, "Diyar Dr Aliyu fah, ji Rayyan."

Yar dariya yayi ganin yanda tayi maganar, "To ai kema ce wai diyata. Sai kice mana diyar mijina zatazo, Rayyan."

"Wai miji na, sau nawa zan fada maku babu abunda ke tsakanin mu? Kuma ni da aure ba yanzu ba, sai nan da shekaru ba kadan ba, kafin dai nayi talatin."

"Yanzu kina shekara nawa?" Tambaya yaya dukda cewar ya san shekarun nata nawa ne.

"Ashirin da uku ko, nan da shekara bakwai kenan."

"Da saurinki, Ramlah. To aure zamu miki, ko ki zauna ko karki zauna duk daya, munsan dai baki guduwa ai. Balle muka kaiki gidan Likita ai saidai muji an kiramu ana cewa muzo Ramlah na labour room." Ramlah bata san lokacin data fara dariya ba tana rufe fuska. Ita duk duniya babu mai fada magana san ranshi kamar Rayyan, shi ko irin tauna ta bayayi.

"In an kiraku lokacin ai yayi kusa, saidai ace maku yau suna za'a saka ma yaro Rayyan. Tunda wannan sayen fada da kakewa babanshi ai dole." Gatse ta mishi kafin ta juya ta cigaba da abun da takeyi, har lokacin dariyar dake kan fuskarta bata gushe ba. Wai Allah, ta ganta ita Ramlah da yaro wanda ba Hanan ba, da miji wanda ba Yaasir ba, ko ya zatayi rayuwa?

"Idan kuma ni kika haifawa d'an bazan taba saka mashi Aliyu ba, tun yanzu ma ki sani." Daga ita har shi ya tsaidasu. Shi baisan maganar zuci zata fito ba ita kuma maganar yanda yayita bata taba tsanmaninta ba. 

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now