Arba'in

1.3K 202 70
                                    

Bude masu gate akayi suka shiga, batasan ya akai ba bacci ya kwasheta kuma shima dayaga wai har yamma tayi bata tashi ba sai bai tadata ba ya cigaba da aikinshi cikin gidan sai wajen shida na marece ta tashi tayi sallah, ko kafin su kawo gida dare ya farayi. "Yanzu ni me zance masu?" abunda ta furta kenan tana turbune baki, kallonta yayi da wani sassanyan murmushi, dakaga fuskarta kasan tayi bacci kuma irin me dadewar nan.

"Lubnah tasan muna tare ai, na fada mata komai." Har tazo bude kofar taja ta koma tana kallonshi, "Ki natsu, Ramlah. Munyi magana da ita, yanzu haka shi Yasir ne ko Yassar yana cikin gidan nan, Dr Aliyu ma. Munga cewar gara a gama maganar nan lokaci daya." Batace komai ba sai gabanta dataji yana faduwa kamar me. Saida ya sauke ajiyar zuciya tukunna ya cigaba, "Idan har shi dinne da gaske, bakuyi shekara biyar da rabuwa ba, dan haka har yanzu aurenshi yana kanki." Tunda take ta dade bataji maganar me matukar tadin hankali ba irin wannan, so take tayi magana amma ta kasa.

"Nasan ranki bazai so ba, dukda cewar tana iya yiwuwa idan kinga da halin komawa gidan mijinki zaki koma. Amma dai yanzu muje ayi magana dashi a warware komai, kinji?" kamar karamar yarinya haka ta daga mashi kai, fitowa sukayi a tare yanata bata baki, ita ji take kamar ma duniyar na juya mata, gata dai a mutum amma bata da maraba da gawar itama.

Tayi hanyar falon cikin gida ya tsaida ta, "Suna falon baki su duka, da da Mamar za'a zauna tace amma duk maganar da zamuyi muyi, idan da bukatar ta wajen sai a kirata a waya." Juya akalar tafiyar sukayi zuwa falon baki. Takalmansu ne ta gani bakin kofa, kuma koda suka kunna kai cikin falon tana iya jiyo maganganunsu sama sama.

Har yazo zai rigata shiga ta riko mashi riga ya juyo yana kallonta, gaba daya daka ganta kasan natsuwa na daya daga cikin abubuwan da sukayi mata kaura. Dan baya sukayi nesa kadan da falon, "Meya faru, Ramlah? Ki daure kinji? Akwai abubuwa dayawa a rayuwa wanda duk yanda mukaso da mu guje masu saboda yanda muke tsoron fuskantarsu dole muyi hakan, Ramlah. Matsaloli dayawa na cikin rayuwarmu dole muyi gaba da gaba dasu ko dan samun kawar dasu daga cikin rayuwarmu. It's not easy, nasani, amma daurewa zakiyi kinji?" Zuwa yanzu yasan karashen labarin rayuwarta, kuma yasan yanda zataji inhar ta tabbata cewa wannan mutumin shine mijin nata, amma ya zatayi? Dole ta fuskanci komai kuma tayi ma kanta zabi.

"Tsoro nakeji, Rayyan. Idan yace bazai sakeni ba fah?" Ita yanzu bama ta komai takeyi ba sai wannan, dan wallahi data koma aure da Yasir gara ta mutu uban kowa ma ya huta.

"Ba akwai kotun musulunci ba? Sai mu kaishi can Ramlah. Bazan taba bari ki zauna da wanda ya zalunce ki kamar yanda ya miki ba, kinji?" Daga kai tayi kamar yarinya, a haka ya lallaba ta suka shiga cikin falon.

Shiga tayi kanta a kasa, tunda ta hango inda Lubnah take ko kallon wajen Dr Aliyu batayi ba dan taga alamar kusan kujera daya suka zauna da Yasir, can ta nufa ta zaune a hankali taji Lubnah ta matso tana mata rada. "Ramlah banda wannan kukan yau, kinaji na? Ki saki baki kiyi magana dan ubanshi idan shi dinne ma dole ya rabu dake yau dinnan ba sai gobe ba."

A hankali Ramlah ta juyo tana kallonta tana mata wani murmushi, har kasan ranta take san Lubnah, kuma Lubnah kullum tana tabbatar mata itama tana kaunarta. Hannuwan juna suka rike kafin ta dago taga ita ya kura ma ido. "Lafiya dai, Malam?" Abunda ta furta kenan, duk wannan kuncin da wani ban tausayi ajeshi tayi gefe, yau a asalin Ramlatun Hajia ta fito tun kafin ya shigo rayuwarta ya maidata yar wahala saboda soyayyar shi.

"Toh fah, Autar Hajia abun duk baikai nan ba." Wani irin wawan tsaki taja, tana jin idanun Dr Aliyu a kanta, tasan bai wuci yace mata kar tayi rashin mutunci ba komai dan sauki ake binshi, amma ita wannan saukin a yau dai kam bada ita ba. "Kallar ka dan Allah, bakaji kunya ba?" Sauke numfashi tayi, "Yanzu tsaya, ka yarda kaine Yasir din ko har yanzu a Yassar dinka kake? Dan idan baka yarda ba banga amfanin zaman nan da zamuyi ba."

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now