Babi na daya

759 15 3
                                    

💕AUTA💕
🌸Bismillahi rahmani rahim. 🌸

*1*
Yanayin yau ya kasance mai dan sanyi a dalilinrashin zafin rana,

yarinya ce qarama tana wasa da kayan wasan ta dai dai misali su ba masu tsada da yawa ba ba kuma masu arha ba gidan shiru da ke ba kowa sai iya (mai aiki) da kuma adda ruqayya kowa kuma sabgar sa yake misalin sha biyu na rana ne ita iya tana kitchen ne tana aiki Addah rue kuma tana daki tana karanta wani English novel mai suna 'DESTINY' yayin da yarinyar take ta wasan ta a wajen dining.

na tsaya na qare ma yarinyar kallo ba xata huce shekara tara xua goma ba, bata da jiki amma fa ba irin siraran nan bane, ita ba fara ba amma ba xa a kira ta baqa ba color ein ta irin chocolate skin ein nan ne mai haske alamar tana samun kula fuskar ta na da tsayi da kuma dan fadi kadan sai dan hancin ta a fuska ba dogo ba ba kuma gajere ba ya dan tashi idanuwanta masu kyau ba manya ba ne amma yankan idon ya fita,gashin idon dogaye da kuma gira a saman su mai cikar gashi da dan bakin ta mai kyau da na kalli bakin sai na ga lips din ta combine na qasa pink na sama kuma brown kamar an mata kwalliya a raina nace mashaa Allah banga gashin kanta ba sbd tasa hula amma a goshin ta ya kwanta kamar na babies.

Sai ga iya ta zo kawo plates dining tace auta har an gama koke koken ?

Yarinyar dai bata kalleta ba dan har ynxu fushi take saida ta ji iya tace to ai shi kenan bari naje na nemi dan rakiya tunda yau mulkin ya motsa Allah ya sa ma ba a gama ba batula yar albarka (ya Zarah) haka iya ke ce mata.

Ai tana jin haka ta dago da sauri ta ce dan Allah kiyi haquri ki je dani dama da kina magana ban ji da kyau bane kin ji iya ta ta qarasa maganar ta da fuskar a tausaya mata,

Iya dariya ma abn yaso bata amma sai ta saita kanta tace ai ba komai auta xauna dai kici gaba da wasan ki kinga kar ma mu fita a bar yarki ita kadai a gida kinga tana jin motsin ki ai ta ji dadi auta ta tace iya ai bacci take

Mu je in gani in bacci take in tafi dake in kuma idonta biyu a gida xaki xauna iya ta amsa ta.

Kamar ta ce iya ta barta ta dubo in yaso ta xo ta fada mata amma kan ta gama tunaninta har iya ta nufi dakin adda rue ta bita da sauri aranta tana addua Allah yasa bacci Addah take amma suna shiga suka ganta tana karatu, iya tace yauwa gurin ki mu ka xo amana na kawo gata nan dan Allah banda duka addah tace to iya ai in kinga na kai hannu na kan yarinyar nan laifi tayi ynxu dai ta xo ta zauna nan ai ko iya ta riqo hannun na ta miqa ma adda ta juya ta ce sai na dawo.

ta barta tana ta qunquni adda tace to sai kin dawo iya.

ta juyo taga auta ta hada fuska xata yi kuka tace yanyy cry cry baby sai in fasa baki chocolate da kuma story mai dadi ai kua nan da nan ta saki ranta.

Dama daxu dalilin kukan mummy ce ta tafi ta barta wai sai tayi assignment dama kan yi take ta ga xata tafi quranic grad din ya zarah ta tashi ta ce sai ta bita shine ta tafi ta barta.

adda rue ta ce in miki explaining constitution ein Nigeria da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan qasar tamu da jihar mu ta jigawa? da eh ta bata amsa tana ta Murna kasancewar ta yarinya mai son jin labari adda tace to da mai xan fara qasa ko kuwa nan gda jigawa ta ce nan, tana nufin jigawa kenan.

adda rue tace a iya shekarun ki dai nasan xa ki iya fahimtar me ake nufi da zalunci, cin amana duk da ba lallai ki fahimci makirci irin na mutane amma da sannu xaki fahimta in na gama baki lbrn nan ina son ki fada min abn da ya qara miki ilimi a ciki kinji,ta ce to.adda rue ta fara

"An yi wani attajiri a nan garin jigawa alhaji Muhammad S Alfais mutum ne mai son jamaa mai taimaka wa na qasa dashi bashi da qyashi ko kadan mutanen garin dutse na jin dadin xama da shi sosai (inda ya ke da xama kuma mahaifarsa) kasancewar sa mutum me kyauta da alheri ga duk wanda ya fuskan ci yana buqata, shahararren dan kasuwa ne, sanaarsa ya na haqar gwal ne ya je kuma wasu qasashen fatauci kusa da nesa yana da matar sa Hajiya sadiya mace abar alfahari ga duk wanda ya sameta fara ce tas kyakkyawa kasancewar ta ruwa biyu ina nufin mahaifinta balarabe ne sai mahaifiyarta bafulatana kuma a taqaice dai zamu iya cewa wannan shi ya kawo kyawun kuma halin kirki na mijin ta bata rage komai ba saima qari.

AUTA (Unedited) Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu