*****cikin rawar murya tace na'am baba, yace yawwa shin akwai wanda kikeso? shuru tayi ta kasa magana, shima shurun yayi yana kallanta, tambayarta ya karayi, still shurun tayi, yayi murmushi yace ki aje zancen wai wani yazo nemanki ta hanyata, zakiman ladabi ki amince dashi koda bakya son shi, banasan haka, saboda duka yarana babu wacce na aurawa wanda bataso, babu kuma wacce nayiwa auren dole, dan haka kema karan kanki bazan maki auren dole ba, ki gayaman idan akwai wanda kikeso na maki alkawarin shi zan aura maki koda kuwa zan bada raina ne, cikin hanzari ta dago da kanta ta dubesa, saboda wannan ne karo na farko da taji yana magana daga zuciyarsa, wannan ne karo na farko da taji yana fadin abunda yake zuciyarsa, hakan yasa taji wani dadi aranta, cikin jindadi da farin ciki tace eh baba inada shi, murmushi yayi tare da yiwa Allah godiya
*******kana yace kin kyauta kuma nagode da amincewa da kikayi dani amatsayin mahaifi, gareki, me sunansa? kanta sunkuye akasa idanuwanta alumshe tace "SHUREIM "ne sunansa baba, fuskanta dauke da murmushi, malam habibu yace toh ayyi Allah ne abin godiya, babu matsala hanna, kije ki kwantar da hankalin ki, aure kuma da SHUREIM kisa aranki ke matarsa ce, in sha Allahu bazan bari kiji kunya ba, haka ta fito tana murna da zumudi, nan ta taya Inna luba aikin gidan, kana suka zauna suna fira, nan yaran malam habibu suka nemi yafiye sa gafarar hanna, haka tayi murmushi tace bakomai ayyi komai ya wuce nima kuyafeman, sukace Allah ya yafe mana, yau kam wasa sukayi da dariya, farin ciki gun HANNA baa cewa komai, bakinta ko rufuwa bayayi, haka ta zauna zaman jiran ummah har karfe takwas amma shuru, nan ta yanke shawaran zuwa gida, nan sukayi saida safe ta fice abunta
******tana cikin adaidaita wayanta tayi ringing, tana dubawa taga kiran ummah, cikin hanzari ta daga wayan, ummah kuwa dakyar ta iya cewa ki sameni a uduth, ba tare da ta jira feedback din hanna ba ta kashe wayan, tuni hanna tace da mai adaidaita mu wuce uduth malam, nan ta shiga kiran number ummah amma network ba kyau, tuni ta shigo zubda hawaye, nan aka ajeta a gate din uduth ta biyasa ta shiga zuba gudu, saida ta karaso emergency, nan ma kiran number take amma bata zuwa, tana tsaye tana wulga na mazurunta ko zataga ummah taga an wuce da mutun kwance akan gadon hospital zaa shiga operation room, tuni taji gabanta yayi mugun faduwa, cikin hanzari tabi gadon da kallo, jin andafa kafadarta yasa tayi saurin firgita tare da juyowa, bakowa bace face hajia afrah, ganin hajia afrah yasa tayi saurin waigawa dan ganin wanda aka wuce dashi akan gadon amma kash tuni sun shige operation room
"""""""""Zatayi magana hajia afrah tayi murmushi tace HANNA? ganin yanda idanuwanta sukayi jawur yasa hanna cikin rawar murya tace mummy lafiya? Ina ummahna? kaman daga sama taji ance gani nan hanna, juyowa tayi tare da karasawa cikin hanzari tayi hugging nata, tace kai ummah Allah kin tsoratani, mekikeyi anan? Wanene bashida lafiya? ummah tayi murmushi tace kowa lafiya lau hanna, dama nace kizo ne dan nasamu abokin zuwa gida, badan ta gamsu da zancen ummah ba, ta kara juyowa ta dubi hajia afrah dake tsaye jugum tana kallansu idanuwanta sunyi jawur, jikinta a sanyaye ta karasa gunta, ta dan dago habarta tace mummy lafiya kuwa? Meyasa nakeji kaman da akwai abunda kuke boyeman? ina shureim?
*********saboda yau nazo maki da babban albishir, amma dai kamin wannan albishir din dan Allah ki sanar dani ina yaya shureim? ummah ce tayi tako zuwa gareta tace muje ki zauna koh hanna? hakan ya kara tabbatar mata da ba lafiya, ahankali tace mummy ina shureim? hajia afrah ta fashe da wani irin kuka cikin muryar kukan tace HANNA kin cuceni, meyasa? Why? Meyasa kika masa haka? idan ya tafi ya barni hanna i have no one, banida kowa my life is meaningless without him, shureim kike tambaya koh hanna? jikin hanna da ya jima da mutuwa, hajia afrah tace then listen.......... Nan ta kwashe tun barin su gidan hajia maryam, har zuwansa gidansu tsoho, har dalilin zuwan sa hospital, kana tace yanzu kuma yana cikin murna da jindadin firan ki da ummah asma'u, ya tsinci kansa a wannan yanayin ba, I know deep down he's not happy without you been by his side, hannayenta ta rike biyu tace hanna i can't afford to loose him wallahi, ki taimaka ki amince ki auresa bayada wani hope bayan wannan, ki taimaka ki SALLAMA SOYAYYAR kowa ki zauna dashi shi kadai, Allah yana sonki, ahankali takai guwawunta kasa tana rokon hanna, ummah dake tsaye tayi saurin karasawa ta rungumeta tana bata hakuri, hanna kuwa tuni tayi mutuwar tsaye saboda banda kallan hajia afrah ba abunda take, sai wasu hawaye zafafa dake biyo kuncenta, kaman wacce aka dasa haka take a tsaye
***********nan take sukaga mutun ya sulale kasa, haka sukayi ruuuu kanta, ummah ta rungumeta tana jijjigata, idanuwanta ta bude ahankali tana smiling tace ummah, mummy, bazan iya rayuwa ba shureim ba wallahi ina sonsa, wallahi dashi nakesan rayuwa, wallahi bazan iya ba, mummy ummah kuman rai, karku bari ya mutu yabarni, karku bari wanda keman son tsakani da Allah ya mutu ya barni, wallahi zan kashe kaina idan yabarni, mummy dake zubar hawaye da itada ummah asma'u, suka shiga lallashinta, ummah ta dafe kanta tana fadin innalillahi wa'inna illaihir raju'un, innalillahi wa'inna illaihir raju'un, innalillahi wa'inna illaihir raju'un
*********mummy kuwa sai shafar gefen fuskar hanna take wacce take kallanta chak tana zubarda hawaye, hanna tace ummah, mummy, bazan iya rayuwa ba shureim ba itace kalma ta karshe da hanna ta fadi, haka suka shiga jijjigata amma ina..................
M. HANNAH 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
More comment
More likes
More vote
More post 👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐👐
Last page hitting in sha Allah 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
SALLAMAR SO 2019
💕💕💕HASHUM 2K19💕💕💕💕💕💕💕
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞
Start from the beginning
