*********page 50-55********
M. HANNA
***************************
23-9-2019*************************
Hajia maryam(mummy) ce atsaye jikin kofar dakin hanifa tana kallan yar'ta wacce take kwance rairan kaman wacce batada rai banda numfashin da take sosai alamu suka nuna tayi zurfi aduniya mutane masu tunani, wata ajiyar zuciya hanifa ta saukar kana ta gyara kwanciyarta tare da bawa mummy baya wanda hakan zai tabbatarwa mai karatu cewa batasan da mutun atsaye jikin kofar ba,haka mummy ta share minute tsaye agurin kana ta fice daga dakin zuwa dakinta safa da marwa ta dauki yi atsakiyar dakin ta goya duka hannayenta biyu abaya, chak ta tsaya ta zauna gefen gadon kana ta dan nisa irin nasu na manyan mata murya cen kasa tace na shiga uku ni maryam, ni kuwa menene yake kokarin illartaman da yar'ta daya wacce ita kadai ce ta rageman aduniya, rashin bata farin cikinta babbar illa ce gareni ga duk kuma wanda yake tare da ita, uhmmm tabbas hajia afrah idan kikayi wasa zakiga wasa saboda bazan taba yadda narasa hanifa sanadiyar danki shureim ba, ya zama dole shureim ya auri hanifa cikin yan kwanaki kalilan ta ko wacce irin hanya kuwa💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
💥💥💥💥💥💥💥💥💥
Hanna ce kwance itama akan kafafuwan ummah idanuwanta alumshe alamun kaman na mai bacci, ummah kuwa qur'ani ne hannunta damanta hagunta kuwa shi take shafar gashin kan hanna da yayi lamo lamo akanta cikin natsuwa takeyin hakan,muryar hanna najiyo tana fadin ummahna? ummah tace naam hanna, bakiyi bacci ba kenan? sai lokacin ta bude idanuwanta ahankali kana tace eh ummah inasan magana dake, ummah ta ajiye qur'anin akan hannun sofa tace toh inajinki gimbiyata, murya cen kasa tace meyasa masu kudi basuda adalci ne? meyasa masu kudi suka cikasan zuciya ne? tambayoyinta sosai suka daurewa ummah kai, cikin kulawa tace uhmmm hanna kenan,ni kuwa waya tabaman ke haka? hanna tace bakowa ummah kawai tambaya ce, ummah tace kinyi gaskiya sedai ba duka aka taru aka zama daya ba, ko acikin talakawa akwai masu irin wadannan halayyar sedai mu roki Allah ya karemu daga fadawa cikin irin su, shiyasa nake yawan gayamaki ki rike gaskiya da amince ki kuma kasance mace mai hangen nesa kada kibari abun wani ya tsone maki ido har yakai ga kin fara hassadarsa ko bakin cikinsa, kedai kiyi hakuri da abunda kike da shi ki godewa Allah idan kika godemasa shi kuma sai ya karamaki, hanna tayi murmushi tace in sha Allahu ummah zan kasance cikin irin matayen da mazajensu da al'ummah ga baki daya zasuyi alfahari dasu💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝
#@@@@@@@@@M . HANNA
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Hajia maryam(mummy) ce zaune a karamin falonta mai dauke da designer's sofa's komai na falon red nd black ne, sanye take cikin shadda atamfa wacce akayiwa gown, sai just cover mayafinda ke kanta, alamu sosai suka nuna tayi zurfi gurin tunani,sallamar ummah asma'u naji tun daga kofar falon harta karaso ta sunkuya mummy batasan da shigowarta ba, bayan ta samu guri ta zauna akan carfet tayi murmushi kana tadan taba hajia maryam, kaman wacce aka tsakura ta waiga nan ta waiga cen, ummah tace gani nan agabanki hajia, wannan irin tunani haka, meyake damunki ne? meyasa kikesan sawa kanki damuwa? mummy tadan nisa kana tace bakomai wallahi asma'u, lafiya? ummah tace lafiya lau dama zuwa nayi na sanar dake cewa yan uwan mahaifin hanna ne suka turo cewa suna son ganina gobe, shine nazo neman alfarma dan naje, mummy cikin rashin fahimta tace mesuke nema gunku kuma yanzu,kai jama'a Allah ya kyauta, ina fatan ba hanna zasu karba hannunki ba? Ummah tace uhmmm ba mamaki nima haka raina yake bani, mummy tace kada kidamu duk yanda kukayi kizo ki sanar dani ni kuma zanyi tsayin daka gurin ganin basu cuceku ba,yaushe zakije? Ummah tace nagode hajia, wai tunda cikin garu daya ne shine naso naje yanzu, mummy tace babu matsala ayyi hanna tana nan koh? ummah tace eh tana nan, mummy ta dauki purse dinta dake gefenta ta bude ta zaro dubu biyar ta bawa ummah tace kiyi kudin mota, nan tayi mata godiya ta fice abunta, bayan fitarta mummy tace Allah yasa ba hanna zasu karba ba saboda itace komai na asma'u wallahi, cikin tausayin ummah ta koma lulawa zuwa duniyar masu tunanin kuma 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
DU LIEST GERADE
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
KurzgeschichtenLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
