Page 60-65💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
M. HANNA 💕💕💕💕💕💕💕
************************************
Yau sati daya kenan da zancen auren hanna, haka take bacci haka take tashi ranta baya mata dadi, duniya tana mata zafi, komai na duniya baya mata dadi, sai sake sake take aranta, wata zuciyar tana gayamata tayi hakuri, wata kuma tana gayamata ta gudu, tana cikin hakan wayanta tayi kara tana dubawa taga kiran khalid, Jikinta asanyaye ta daga wayan tare da cewa hello khalid, nan suka gaisa kana yace kizo gani kofar gidan, tace okay, haka ta mike ta zuba hijabinta dogo har kasa mai hannu sky blue kana ta fice abunta tafiya take kaman batasan taka kasa, tana fitowa ta samesa akan babur dinsa zaune nan ta mashi sallama ya amsa cikin sakin fuska, bayan sun gaisa yace kwana biyu kin shareni bayan kinsan kece farin cikina banasan bacin ranki, kiyi hakuri ki yafeman mana wallahi fushin zuciya ne kawai bakomai ba, hanna tace uhmmm bakomai khalid Allah ya yafemana duka ayyi kasan dan adam ajizi ne komai na rayuwa dan hakuri ne, da haka dai suka dan taba fira mai dan tsayi, suna cikin hakan yace toh yanzu dai aje wannan gefen dama nazo muyi wata yar shawara ne, kinsan before nagayamaki auren mu sai nan da shekara daya amma gaskiya yanzu nakasa hakuri zanso ki kasance mata agareni, ya abun namu zai kasance ma'ana shirye shiryen bikin namu,hanna ta masa kallan tausayin kana tace uhmmm khalid kenan ayyi bakin alkalami ya riga da ya bushe saboda yanzu haka zancen da nake maka su baba habibu sun tsayar man da miji bana tunanin aurena zai jima gaskiya, khalid dake zaune ya sauko ya karaso ahankali gunta yace kice dani kina wasa kinji hanna, hanna ta dubesa da sexy eyes dinta tace wallahi dagaske nake ba wasa nake ba, nan ya shiga salati yafi akirga kana yace amma kin yaudareni hanna kin cuceni kin kuma zalunceni, sannan wallahi wallahi bazan barki haka ba wallahi you will pay for ur mistake in sha Allahu, sai kinyi da kinsanin sanina wallahi, sai na tabbatar kinzama goro ko abun saye banza kawai, diyar talakawa dama saidai aka gayaman amma naki ta mutane, ashe kina kasa kina man rame wallahi ke zaki fada aciki,wato kinyi clean kin zauna agidan masu kudi, toh kowa yasan mekukeyi dake da tsohuwar ki aike kukeyi, cikin zafin nama tace ya isheka khalid, daga magana sai abu ya zama dan zane, ayyi kai ne babban matsiyacin dan iska, cikin zafin nama khalid ya daga hannu sai jin hannunsa yayi asama yayi hanging ita kuwa harta juya ta runtse idanuwanta,cike da mamaki na juya bakowa bane face shureim wanda ransa yayi mugun baci, da hannu daya ya rikesa amma sai wanj kokarin fizge hannun yake, jin babu saukar marin yasa ta dago ta dubesa, ganin yaya shureim rike da hannunsa yasa taji tsoro sosai
*******khalid kuwa cewa yayi kai me haka, kana hauka ne, wai meyasa diyan masu kudin nan kuncika shishshigi ne, sai ku dinga abubuwa irin na masu karfi bayan kunsan bazaku iya komai ba sai lissafin kudi, kada kace zakayi dani saboda mun riga mun saba da aikin karfi, ko yawun bakinsa bai karasa hadiyewa ba yaji saukar mari, shureim yace wannan na gwada marinta ne da kayi, ya kara masa daya yace wannan kuma na zaginta ne da kayi, toh tun wuri Kabar nan gurin before nayi handling naka, khalid dake rike da kuncensa gefe biyu yayi turu turu da idanuwa yana kallan kira irin ta shureim, aransa kuwa cewa yayi bari nabar nan kamin wannan basamuden ya daukeni da wani marin nasha dukan banza cikin rawar jiki ya hau babur dinsa ya fice cikin hanzari kaman zai fira sama saida yayi nisa dasu kana yace Allah ya isa, dariya ta kubuce masu dukansu, sun dauki lokaci sunayi kana shureim yasa kai ya fice ba tare da yacewa hanna alif ba, ganin ya fice ransa abace yasa tabi bayansa da gudunta, dede parking space ta samesa yayi tsaye ajikin mota yayi crossing legs dinsa, fuskansa adaure ta karasa gunsa, zatayi magana ya daga mata hannu alamun tayi shuru, chak ta tsaya, cikin isa yace meyasa kike hulda da mutane irin wadannan? ko alama ba class dinki bane gaskiya bazan boyemaki ba banjidadin hakan ba natabbatar da ban isa gurin ba zakisha dukan banza wallahi, karki kara kar kuma kibari nakara ganinki dashi atsaye ke bama shi kaidaiba kada na kara ganinki da kowa, i hope u get me right? Ahankali ta dan daga kanta alamun taji kana tace kayi hakuri yaya shureim bazan kara ba in sha Allahu, yace u better not, mekikeyi ne yanzu? tace bakomai, yace muje ki rakani wani guri, batayi masa musu ba kuwa ta shiga suka fice.........
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
