*********page 10-15
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
💌💌 M. HANNA💌💌💌💌
Hanifa ce kwance akan lafiyayyan gadonta, tana shashshekan kuka hannunta dauke da hoto tana kallansa bakowa bane face hoton yaya shureim wanda yasha ado cikin wasu hadaddun kananun kaya black nd white, kofar dakin aka turo hanna ce ta shigo bakinta dauke da sallama tana murmushi harta zauna gefen hanifa, hanifa batasan da shigowar mutun ba, hanna ta wani ya mutse fuska cikin muryar kulawa tace hanifa, ahankali ta dago ta rungume hanna ta fashe da kuka kaman ranta zai fita, hanna tana shafar gadon bayanta itama kukan take, dakyar sukayi shuru, hanna ta zameta jikinta tace kiyi hakuri though bansan menene yasaki kuka ba, hanifa ta kara rungume hanna kana tace hanna baya sona, wallahi baya sona, bai damu dani ba, ko kwalliyana bai yaba ba, bai gayaman nayi kyau ba, hanna bayasona wallahi
********hanna tayi murmushi ta zameta jikinta, kana tace haba sisto meyasa kike irin wannan tunanin?kawai kibari ya huta, kinsan yanda doguwar tafiya take, ya kanyu ya gaji wallahi, just give him time mana, hanifa tasa hannu ta goge guntayen hawayenta kana tace kin tabbatar da cewa yana sona hanna? Hanna tayi murmushi tace sosai ma kuwa, just go and see him koda bayan magriba ne, hanifa tace okay then nayarda da zancenki anjima zanje, hope zaki rakani? Hanna tayi murmushi tace not really saboda i will b busy by then, hanifa tace okay toh yayi
******hanna ce tsaye a cikin kitchen tana yanka alayyahu lokacinda da taji muryar yaya shureim yana cewa dan Allah help me with water, batare da ta juyo ba ta wanke hannunta tasa towel ta goge kana ta nufi fridge ta bude komai akan idonsa takeyinsa, amma tana juyowa yayi saurin kauda kansa zuwa gefe, hannayensa biyu a aljihun wandonsa, hanna tana karasowa ta dan sunkuya kana tace ga ruwan yaya shureim, ahankali ya juyo ya karbi cup din hannunta ba tare da yace da ita alif ba, ta bude ruwan goran ta zuba masa, cikin isa yace is okay, haka ta juya ta fice taci gaba da aikin nata, kallo yaya shureim ya bita dashi babu kyabtawa harya shanye ruwan bashida labari cup din yana abakinsa, muryar mummy ce ta katse shi da saurin gaske ya juyo yace mummy barka da fitowa, tace barka dai shureim mekake a kofar kitchen? Yace wallahi i was tasty shiyasa , mummy tace fridge din dakinka baya aiki ne ko ba ruwa? Yayi murmushi yace noo ba daga daki nake ba, tace alright then,
***********misalin karfe takwas na dare sukayi dinner, a fallo suka zauna suka kwashi firansu, da mummy da yaya shureim, sai dariya suke,misalin karfe tara tace nizan shiga ciki, yace toh mummy gudnyt, tace okay nyt son, tana ficewa yaya shureim ya mike tsaye ya fice zuwa dakinsa, wanka yayi kana yayi dressing cikin kayansa na bacci silky ones black, ya dawo fallonsa ya zauna, da yake dakinsa ciki da fallo ne, kafa daya ya dora akan daya ya shiga yanar gizo awayansa, lokacin akayi knocking, shuru yayi nadan lokaci, kara knocking akayi yace come in, hanifa ce ta shigo cikin kananun kayanta riga da sket kayan sun zauna jikinta sosai, sai dan karamin mayafinda ke kanta, gefensa ta zauna cikin shagwaba tace yaya shureim am sorry, hankalinsa akan wayansa yace mekikayi ne? Tace uhmm abunda nayi dazu wallahi nakasa controlling kaina ne but am sorry, ahankali ya ajiye wayansa yace bakomai nafahimta, any problem? Cikin rashin fahimta tace haba yaya shureim hanifar ka ce fah, yace nagane mana hanifa kanwar yaya shureim koh? Tuni ta wani ya mutse fuska tace kanwa kuma? Yace uhmm eh mana, tace okay naji
*******yaya shureim na maka wani laifi ne? Ko kallan kwarai bakaman ba tunda kazo, ko kwalliyar da namaka baka yaba ba, dan Allah idan namaka wani laifi kayi hakuri ta fadi hakan tare da dora hannunta akan kafadarsa, yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace kada kidamu, bakiman komai ba, hakan ba karamin dadi ya mata ba, tuni ta shige jikinsa tace nagode yaya shureim, yace your welcome, cikin kulawa yace bacci nakeji, tace okay, yayi murmushi yace toh ki dagani mana, ahankali ta dago tana smiling tace ooh sorry, harta mike tana rangwada tana karawa, yace ki kawoman fura nasha i really miss dat,ta juyo tace okay yaya shureim tare da kashe masa one eye, tana ficewa yayi murmushi yace hanifa kenan
*********tana fitowa taci karo da hanna ta fito daga dakinta, hanna tayi murmushi tace bukata ta biya koh? Hanifa tace uhmmm kedai bari dakyar wallahi, hanna tayi murmushi tace dama nagayamaki,gajia ce kawai dazun, hanifa tayi murmushi tace thank you darling, ki kaimasa fura nizan shiga na kwanta, hanna tace okay babu matsala saida safe, hanifa ta shigewanta daki, hanna kuwa kitchen ta shiga ta zuba masa furan a bowl da ludayi ta nufi dakinsa,knocking tayi , kana ta bude da akace ta shigo, tana shiga tayi sallama cikin tattausar muryarta mai dadin sauraro, ahankali yake kallanta yana kwance akan doguwar sofa, tace yaya shureim ga furan, yace okay dora akan table din, ahankali ta dora bowl din akan side table dinda ke gefensa, tace kana bukatar wani abu ne? Yace aaah kada kidamu, ina fatan kinci abinci? Tayi murmushi tace naci yace okay toh yayi, menene sunanki? Tana wasa da yatsunta tace HANNA, yace okay hanna thank you, haka ta fice daga dakin cikin natsuwa da takonta tamkar batasan taka kasa,
********EARLY IN D MORNING ***
Da sassafe hanna tayi breakfast ta jera komai akan dinning, misalin karfe takwas suka fito breakfast haka tayi serving nasu kaman kullun, ta juya zata fice yaya shureim yace ki zauna mana kema kiyi breakfast din, amsar da ta saba basa ta basa cewa nasu yana daki, haka ta fice, hajia maryam(mummy) mahaifiyar hanifa cikin rashin fahimta tace wai shureim meyasa kullun kake cewa ta zauna cikinmu taci abinci ne, mai aiki ce fah, yaya shureim yayi murmushi yace ayyi naga itama mutun ce, hanifa tace kada kidamu mummy, kinsan yaya shureim da son mutane, mummy tace hakane kuma, toh ka saba da yar aiki ce bazataci abinci acikinmu ba,ransa abace yace kiyi hakuri mummy, nan suka karasa breakfast din ransa baya masa dadi saboda furucin mummy akan hanna
**********hanna ce tsaye awaje tare da masoyinta KHALID,zaune yake akan babur dinsa, yana smiling,tayi murmushi tace kayi hakuri na tsayar dakai ina aiki ne cikin gida,cikin kulawa yace bakomai habibty, ayyi nasan bazaki barni awaje ba,batare da wani dalili ba, yace albishirinki, tace goro fari tas,hannunsa ya saka a aljihun wandonsa ya fito da wani envelope fari ya mika mata, juya envelope din take dama da hauni kana tace menene wannan? Yace uhmm aikinda kikace nanema maki ne a big restaurant dinda yake cikin sokoto,cikin zumudi ta bude envelope din ta fiddo da takarda ciki ta karanta, tsalle tayi Kaman zata rungumesa tace nagode sosai khalid wallahi naji dadi sosai, yayi murmushi yace toh shikenan yanzu kam adaina zama boring, tace in sha Allahu,haka sukayi sallama ta shigo cikin gidan, nan taci karo da yaya shureim zai shiga mota, tana ganinsa tace adawo lafiya,
*******yayi murmushi yace Allah yasa, zo nan hanna, tana karasowa, yace ina kika fito ne? Tace naje karban sako ne awaje, yace menene hannunki? Tace uhmmm takardan aikinda nasamu ne a restaurant, inasan naje nagansu, sugani, yace okay, muje na ajeki koh? Cike da kunyarsa tace aaah yaya shureim jeka kawai zanje daga baya, wata harara ya wulga mata kana yace jeki shirya muje, tace okay bari nagayawa ummah, haka ta karasa bangarensu tana tsalle tana karawa, daki ta sami ummah zaune tana nadiyar kayanda ta wanke, shigowar hanna yasa ta dago tana smiling tace wannan murmushi haka kaman wacce akayiwa kyautar aljannah, hanna tayi mata bayanin komai, kana tace yanzu haka yaya shureim yace nazo ya ajeni, ummah tayi mata addu'a kana tace adawo lafiya, haka ta fito suka fice tare da yaya shureim
*******suna isa restaurant din, tace nagode sai anjima koh? Yayi murmushi yace get out joooh ayyi ina nan tare dake, muje kiyi duk abunda zakiyi mu koma gida, hanna tace ba aiki zakaje ba? Yace uhmmm before naganki kenan, amma yanzu ayyi kece aikin nawa, zatayi magana ya dora dan yatsansa akan lips dinsa yace shiiiiiiiiiiiiiii muje don't say a word, tayi murmushi suka karasa ciki tare, bayan ta karasa komai suka fito, suna kan hanyarsu yace ni kuwa na tambeki hanna? Tace inajinka yaya shureim, yace okay, uhmmm will you b my friend ? Kinsan bako ne ni daga office babu inda nasani so inasan ki nunaman wuraren da bansani ba, najima bana kasar nan musamman garin nan naku, hanna tayi murmushi tace uhmmm ayyi wannan aikin hanifa ne, saboda...... Katseta yayi ta hanyar dake nake zance kidaina kawoman hanifa idan muna magana, tace kayi hakuri yaya shureim i don't mean to hurt you, is just dat naga..... Katseta ya sakeyi kana yace just say something about maganar da nayi, forget hanifa, ayyi nasan hanifa nayi maki maganar, so kada kibataman rai, kada kuma kice ummah saboda nasan ummah bazata hanaki ba, so d answer is yes you will, hanna tayi shuru tana kallansa takasa ce masa komai, yayi murmushi yace my next question.......
Cast
Yaya shureim
HAJIA maryam(mummy)
Ummah asma'u
Hanna
Hanifa
Khalid💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞nd other's
More comment
More post
M. HANNA
MRS MUHAMMAD NOOR💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
