💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞

932 36 6
                                        

Page 135-140

M. HANNA 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Kaman yanda HANNA take bawa fatiumar690 haushi nima karan kaina M. HANNA haka take bani haushi, ayyi inaga komai ya wuce amma dole mu mata uzuri ko menene dalilinta nayin hakan, muje, zuwa dan samo amsar

Cast
Hanifa
Hanna
Shureim
Ummah asma'u
Malam habibu
Hajia afrah
Dr Othman hali
Hajia maryam
Audu
Hydar
Yusrah
A'alim
Nas
Nura
Ummi
Hamdiya
Hajia barakah
And other's all in SALLAMAR SO💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟

Story continues

Zaune take akan kujeran da take kallan gadon da shureim yake kwance wanda aka sakawa ruwa drip ajiki sai baccinsa yake, sosai fuskarsa tayi haske, yau kwanan sa biyu banda bacci ba abunda yake dan tun ranar da aka kawosa bai falka ba, a'alim ne da hajia afrah keta safa da marwa acikin hospital din,sanye take cikin wata arabian jallabiya black wacce tasha stones work ko ina, sai dan karamin Arabian hijab dinda ta saka, kafa daya ta dora akan daya tana kallan shureim, wata ajiyar zuciya ta saukar kana ta dauki wayan shureim dake gefen fillonsa, nan ta shiga contact dinsa, sai scrolling take, haka dai taketa scrolling through kana ta dan nisa murya cen kasa tace toh kome yayiwa HANNA saving dashi, nan dai ta danna senorita nan take sunan ya fito, tayi dan guntun murmushi tace dama na taba jin ya kirata da sunan wato shine ya mata saving dashi, shureim kenan nan take tayi copying number to phone dinta tayi saving nata da HANNA, kana tace uhmmm natabbatar bazai rasa ta ummanta ba, nan ma dialing ummah asma'u tayi, haka sunan ya fito awayansa, tayi copying number tayi saving nata, kana ta kashe wayan tasa ta ajiye masa gefensa

********knocking din kofar dakin akayi, mummy afrah ta danyi shuru tana sauraren shigowar mutun amma tsit kara knocking akayi tace come in, ahankali aka turo kofar dakin bakowa bane face a'alim hannunsa dauke da basket din abinci, tayi murmushi tace aaah kai ne kaketa knocking sai kace wani bako, murmushi yayi tare da ajiye basket din hannunsa har kasa ya sunkuya ya gaisheda mummy, ta amsa masa cikin sakin fuska, nan tace ya aikin? ya amsa da alhamdulillahi, komai lafiya lau, nan shima ya samu kujera ya zauna daga gefen hagun mummy, yace ya tashi kuwa? mummy ta girgiza masa kai alamun aaah, yace amma kam yasha bacci, mummy tace dr yace kwatakwata baya bacci, a'alim yace Allah sarki cikin muryar tausayi kana yace Allah ya baka abunda kakeso indai alhairi ne agareka, mummy ta amsa da ameen, zatayi magana, sukaji ya fara coughing da karfin gaske, haka mummy da a'alim sukayi kansa, dakyar yayi shuru kana ya bude idanuwansa mummy da a'alim kusa sai sannu suke ce masa, bayan ya bude idanuwansa yace mummy HANNA, mummy shs left me shattered wallahi, i can't  imagine my life without her, mummy ta rungumesa jikinta, tana shafar gadon bayansa ahankali, a'alim yace haba abokina is okay mana, kadaina irin zancen nan, you can live for mum mana if not hanna, Allah dix ix totally wrong, shureim yayi murmushin ciwo yace bazaka gane ba a'alim wallahi hanna itace rayuwata, itace komai nawa, a'alim zaiyi magana, mummy tayi saurin taron numfashinsa da haba shureim idan dai dagaske kake ayyi ba haka ya dace kayi ba, Hanna was here, she was crying sosai amma baccin ka kawai kake, ahnakali ya zame jikinsa daga na mummy yace shine baki tadani ba ganin yana kokarin saukowa mummy tace kaga dan Allah, tace zata dawo, yace Allah bazata dawo ba mummy, mummy tace nina aiketa zata dawo, haka dai mummy ta samu ta lallashesa yayi shuru, har yaci abinci mai isarsa yasha magani kana ya koma baccinsa, yana rungume da hannun mummy, saida baccin ya masa yawa kana mummy ta zame hannunta ahankali, sign ta yiwa a'alim dake zaune ya biyo bayanta suka fito tare

***********mummy afrah tayi murmushi tare da jingina a jikin bango tace yanzu sai ya kenan a'alim? A'alim dake tsaye jikin bangon shima yace uhmm ayyi ni mummy kin kasheman Niki duka, kince masa HANNA tazo ni kuma bansan yaushe tazo ba before nazo ne ko kuma when? mummy tayi murmushi tace kana tunanin banda na masa haka zaici abinci har ya koma ya kwanta kuwa? A'alim yayi murmushi yace kinyi gaskiya mummy, amma gaskiya yakamata naje neman HANNA na tabbatar idan ya kara tashi muka bashi labari iri daya abunda zai biyo baya bazaiyi kyau ba, so mekike tunanin yakamata ayi yanzu? mummy tayi murmushi tace kada kadamu a'alim kabarman komai a hannuna yanzu zan fita but i will b back later in d evening take care of him, a'alim yace okay mummy Allah ya tsare, haka suka koma ciki ta dauki handbag dinta hade da car key dinta ta fice tare da masa sai anjima, bayan fitar mummy, a'alim ya zauna yana karantawa shureim adduoi yana tofa masa

❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon