💕💕💕💕💕💕💕page 20 -25💕💕💕
**********M. HANNA CE KE MAGANA********
1-9-2019
################
Da sassafe hanifa ta tashi tayi sallah subahin kana ta fice daga dakin cikin silky red kayanta na bacci riga da wando, kayan sun mata kyau sosai, sai packing gashinta da tayi tsakiyar kai, hanifa dai kyakkyawa ce zubin fulani, ita ba gajeruwa ba ita ba mai tsayi ba, amma kallo daya idan ka mata zakaso ka kara wani kallon, hanifa macece mai ji da kanta, tanada aji da class sosai, bata daukan raini gun kowa musamman namiji,fara ce sosai, kaman ka taba jini ya fito, ba wani jiki ne da ita ba amma akwai na fulani da kuma hips sosai wadanda sune ke jan ra'ayin maza zuwa gareta, ita kadai ce yar'tilo da mahaifanta suka haifa aduniya bayan sunsha wuya da wahala gurin nemanta, hakan yasa duk suka dauki son duniya suka dora mata, basasan bacin ranta bare tashin hankalinta, hanifa tayi duka karatunta tun daga nursery, primary har university a kasar waje uk, saboda acen aka haifeta, saida ta karasa karatunta na degree a fannin (zoology) gefen dabbobi kenan kana suka dawo nigeria, sosai hanifa takesan dabbabobi musamman mage da dai sauransu,
*********bari mu dakata anan danjin abunda ya fito da hanifa da sassafe ***
*****direct kitchen ta nufa bakowa a kitchen din amma ga dukkan alamu hanna ta shigo ta fita saboda dankalin turawan da tagani a ruwa an feresa ankuma yankasa yankan suya, wani dan guntun tsaki taja, kana tayi tsaye alamun mai nazari, bayan dan wani lokaci tace yawwa pancake will b okay for breakfast, nan take ta fara aikin yin pancake din, bayan ta dauki 10minute a kitchen din hanna ta shigo kaman kullun cikin doguwar rigarta ta bacci da hijab dinta, ganin hanifa a kitchen ba karamin mamaki yabata ba hakan yasa taji zuciyarta tana bugawa uku-uku, cikin sanyin jiki ta karasa fuskanta dauke da murmushi tace yau sarauniyar ce a kitchen? Hanifa kuwa kota kanta batayi ba taci gaba da hada abun pancake din
*******hanna tace uhmmm yan maganar basa bisa kai ne? Taji shuru, jin hakan yasa ta fara tsorata da hanifa, hakan yasa tayi shuru ta fara aikin nata na soya arish din cike da fargaba da tsoro, tana cikin hakan hanifa tace dan ubanki bakiga zanyi amfani da gas din bane? Jin hakan daga bakin hanifa yasa hanna tayi saurin waigowa tace hanifa ubana kuma yau ke da kanki kike zagin ubana? Cikin zafin nama hanifa tace ko zaki rama ne?dan naga kinfi yar masu gidan iya rainin hankali da kuma daukar hankali, hanna tayi murmushi na takaici tace kiyi hakuri yanzu zan baki guri, jikinta yana rawa ta karasa komai harda soya kwai, ta jera komai takai kan dinning ta aje, takaiwa masu gadin gidan nasu kana ta dawo ta dauki nasu zata fice hanifa tace ina kuma zaki? Chak ta tsaya ba tare data juyo ba tace zanje dakine, hanifa tace kije dakina ki gyara, kiman wankin toilet sannan ki wankeman underwears dina, hanna tace toh, kulan hannunta ta ajiye kana ta fice zuwa aikin hanifa
********cikin dan kankanin lokaci ta karasa aikin nata, harda wankin underwears din, wani iska ne mai zafi ta huro daga bakinta kana tace menayiwa hanifa ne take zagina? menayi mata take kokarin sauyaman daga hanifa zuwa wata macen ta daban, na shiga uku, Allah yasa wulakancin da ta faraman ya tsaya akaina kawai saboda gaskiya idan tace zatayiwa ummahna wallahi bazan kyaleta ba, ahaka dai tabar dakin, tana fitowa sukayi kacibus da yaya shureim wanda yayi shirin fita office, cikin girma da girmamawa ta gaidashi, har zata wuce yace hanna ki sameni adaki, bai jira feedback nata ba ya ficewansa
*********ta dauki yan mintuna kana ta biyo bayansa, tsakiyar dakinsa ta samesa atsaya fuskansa adaure, tana shigowa ta sunkuyar da kanta kasa ta fara wasa da yatsunta batare da tace dashi alif ba,cikin husky voice dinsa yace me yake faruwa ne? Cikin small voice dinta tace bakomai yaya shureim, yace karki boyan komai saboda naga komai, hakan yasa tayi saurin dagowa da kanta ta dubesa cikin sexy sleepy eyes dinsa tace meka gani? Yace abunda ya faru tsakaninki da hanifa mana, tayi murmushi tace uhmmm bakomai yaya shureim, cike da takaici tace kada kadamu ayyi kasan akwai banbanci sosai atsakaninmu ni yar aikin gidan ce wacce suka taimakawa, ta daukeni amatsayin yar uwa yanzu kuma tana ganin cewa ba dede bane ta daukeni yanda ta daukeni ba, kawai tana kokarin nunaman matsayina ne, cikin rashin fahimta yace wane matsayi kenan? Tace ni yar aikin gidance ita kuwa diyar masu gidance🙍🙍🙍🙍🙍🙍🙍🙍🙍🙍🙍
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
