💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞

Start from the beginning
                                        

******bangaren hanna kuwa har lokacin tana nan zaune karkashin bishiyar taga fitowan hajia afrah rai bace, daga kuma lokacin da ummah ta fita, cikin hanzari ta shigo gidan nasu direct sai dakinta, nan ta shiga hada kayanta, cikin sauri da rawar jiki, idanuwanta sun rine sunyi jawur, sai gumi take tana karawa ga fanka amma gumin kawai take, kab ta gama hada kayanta, tana saukowa da trolley din daga kan gadon kiran "ummah" yana shigowa wayanta tana dubawa taga ummah asma'u dakyar ta iya hadiye yawun bakinta tana kallan screen din wayan tare da wani kyabce kyabcen idanuwa kaman wata yar tsana, har wayan ta gama ringing bata daga ba, kira aka sakeyi, dole ta daga wannan karon, murya cen kasa tace assalamu alaikum, ummah tace wa'alaikissalam kina ina ne hala hanna? wai meyake damunki ne kwanakin nan sai dai na nemeki cikin gida na rasa ko kuma ki shige daki sai kace tsohuwar mayya, kina ina ne yanzu? cikin rawar murya tace ina cikin gida, ummah tace toh kije mazza gidan malam habibu kawunki yana neman ki sannan ki tsaya cen har sai nazo, ki tabbatar kinje dan banasan wani turanci,hanna tace uhmm ummah asma'u ya kashe wayan ba tare data jira feedback dinta ba, haka hanna ta kai har kasa zaune tana hawaye, sosai duk inda rikicewa take hanna ta gama rikicewa, ta rasa meyake mata dadi duniya, komai na duniya jinsa take kaman wuta, komai baya mata dadi, haka cikin rashin kwarkn guiwa ta mike tsaye ta dauki purse dinta da wayanta  ta fita, nan dakin yabar trolley dinta gefen gadon

********direct gidan kawunta taje wato malam habibu,nan ta shiga bakinta dauke da sallama, haka aka amsa mata bakin mutun uku, duka yaran malam habibu da sukayi aure sunzo ganin gida yau, biyu dauke da yaran su wadanda zasu wuce 2years dayan ce dauke da ciki haihuwa ko yau ko gobe, tana shiga tagansu haka suka dinga watsa mata harara ta raini da wulakanci, inna luba ce ta fito daga dakinta ganin hanna yasa ta wani washe 32 dinta tare da cewa amaryarmu ta Jibi,cikin jin kunya suka gaisa, kana tace kije yana dakinsa, haka ta mike ta fice, daya daga cikin yaran malam habibu tace me haka ummah, wannan irin farat farat da kikeyi da hanna na menene? inna luba tace yaro yaro ne baisan wuta ba sai ya taka, tun wuri Kuyiwa kanku karatun ta natsu dan ko wanda kuke goyon bayansa ana masu wulakanci ya tuba ya koma ga Allah, saboda dukanku albarkacin ta ne kukeci har yanzu da kukayi aure ko kun dauka mahaifinku ya samu wani aiki ne da ya biya bashin ku na aure? shuru sukayi dukansu, kana tace toh duk gun mai neman auren hanna ne aka samo kudin biyan bashin duka, har ake maku aiken dubu biyar dubu goma dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira, indai ni na maku bayani haka toh shi kam bansan mezai maku ba, wacce keda tsohon ciki cikinsu tace Allah sarki amma wallahi ummah najidadin wannan labari, Allah sarki duniya, dama haka ta gada, muma ya kamata mu nemi yafiyarta saboda mun aikata mata ba dede, dan Allah kuyi hakuri, dukansu shuru sukayi saboda sosai jikinsu yayi sanyi, dayan tace tabbas dole mu nade tabarmar kunyar mu da hauka saboda dukanmu munci amfaninta sosai, inna luba dake tsaye a kofar dakinta tace dadai yafiye maku sauki, kana ta fice zuwa kitchen,

*******bayan shigar hanna dakin malam habibu ko yau zaune ta sameta amma yau yasha banban da kullun zaune yake akan sallaya yana jan charbi kansa sunkuye akasa, bakinsa kawai yake motsi, sallamar ta yasa shi juyowa yana ganinta yayi murmushi ya mata nuni da gefensa ta zauna cikin natsuwa, ya dan dauki 5minute kana ya juyo yace hanna ya gidan naku? Ta amsa masa da lafiya lau, yace toh ma sha Allahu, kiyi hakuri sai yawo nake saki safa da marwa kawai kike yi,hanna dai banda smiling ba abunda take, malam habibu yayi gyaran murya kana yace yau ummahnki tazo ta nemi wata alfarma guna, wacce nake tunanin duk duniya yanzu idan akwai wacce nakejin nauyin ta nemi abu guna banyi ba toh tana bayan hasama'u, cikin rashin gamsuwa tace alfarma kuma? yace sosai kuwa, ta gayaman cewa kinada wanda kikeso kuma duk duniya bata tunanin kin taba san wani bayansa, ta tabbatar man da cewa hankalinki da nata zaifi kwanciyar idan kika auresa, dan haka shiyasa nace toh ta turoman ke naji daga bakinki kinsan ance waka abakin mai ita toh tafi dadi, yanzu shin hanna kinada wani uba ne  bayan ni? idan ban maki abunda kikeso ba kina tunanin mahaifinki zaiji dadi a inda yake? haba dan Allah, ni fah sanin da kikaman dan bani bane yanzu na sauya sosai hanna, wallahi nayi karatun ta natsu tun lokacin da naga yanda rayuwa tayi da mutanen da na wulakanta da kuma yanda tayi da wadanda suka wulakanta, tabbas rayuwa /duniya ba bakin komai bane, duniya ba matabbata bace, dan haka muna rokon Allah ya mana karshe mai kyau, tabbas duk wanda ya wulakanta mutun zai ga yanda bayaso ko ba yanzu ba toh zai gani ga yaransa ko dan uwansa, dan haka ki cire zancen komai aranki, ki saki ranki, ki daukeni yanda kika dauki mahaifinki, na tabbatar baki manta irin hudubarda yake maki ba tun bakida wayo har Allah ya karbi ransa, hanna?

❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤Where stories live. Discover now