*****ummah asma'u tace kada kimanta nagayamaki cewa akwai alkawari tsakaninmu ma'ana dani da shureim na tabbatar bazai bari naji kunya ba, hajia afrah tace wato har akwai wani sirri kenan wanda ni afrah bansani ba, ummah asma'u ta tabe baki tace wannan kuma tsakanin uwa da da'a ne, bari naje naga yarona saboda lafiyarsa ta fiyeman komai,haka suka mike dukansu suna dariya suka shiga dakin, suna shiga abokanansa suka fito har a'alim, akabar daga hajia afrah, ummah asma'u sai shureim, wanda ganin ummaj asma'u ba karamin mamaki yaji ba, cikin rashin gamsuwa da itace yace ummah asma'u? tace uhmm shureim nice nan ba wata ba, ko kana tunanin gizo ne nake maka? Wani dan guntun murmushi yayi kana ya saukar da wata ajiyar zuciya tare da cewa alhamdulillahi hannayensa sama lokacin da ya fadi hakan, mummy afrah dake zaune gefensa na dama tayi murmushi tace bakada kunya yanzu koh shureim? yayi murmushi yace mummy kinfi kowa sanin rashin HANNA agurina tamkar rasa rayuwata ne i so much love her, wallahi mummy bantaba ganin macen da ta kwantaman arai ba kaman yanda hanna ta kwantaman ba, am sure zakifi kowa farin ciki idan HANNA ta kasance daughter in law dinki, so please stop blaming me nd blame my heart, mummy afrah tayi murmushi ta shafi gefen fuskarsa tace i know my son, dubansa ya maida kan ummah asma'u yace ummahna shine kika tafi kikabar danki? ummah asma'u tace kayi hakuri dole ce tasa hakan, bansan cewa hakan zata kasance dakai ba, amma kayi hakuri haka bazata Kara faruwa ba, shureim yayi murmushi yace nagode ummahna, yanzu ina kuka koma? kunbar anguwarku ta farko, jin hakan yasa ummah asma'u tace kasan unguwar da muka baro ne? yace sosai ummah, ranar da naje ranar na samu kaina awannan yanayin sanadiyar.... Nan ya kwashe zuwansa har kiran a'alim da yayi, ummah asma'u tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un Allah ya baka lafiya, kayi hakuri, amma anya wannan dillalen besan dalilin barin mu wannan gidan ba kuwa? shureim yace meya faru ummah? Nan ta gayamasa komai shima kaman yanda ta gayawa mummynsa, yayi murmushi yace uhmm wato shine dalilin da yasa HANNA ta sauya maku gida kenan, hajia afrah da ummah asma'u sukace kamanya kenan?
*******shureim yace dama ni naje na sami hanifa har gida........ Nan ya kwashe komai ya gayamasu, ummah asma'u tayi shuru nadan lokaci kana tace "duk inda jirgi yaje idan akayi hakuri kunkunu ma zaije"wato HANNA tayi hakan ne saboda ta kara nisantarka, tabbas"yau da gobe mai sa amari suruka"hajia afrah kuwa shuru tayi kana tace uhmmm "mai hankali shi yake gane baccin makaho"tabbas kinyi saurin gano tarkon nata, amma yanzu menene mafita? Na tabbatar idan ta fahimci cewa kinsan komai ayanda nasan halinta da kunya da jin tsoronki abunda zai biyo baya, bazaiyi kyau ba,shureim ne ya katsesu ta hanyar cewa duk wannan ba aikin ku bane nawa ne nan, mummy ta juyo tana kallansa cike da mamakin yanda taga ya warware ganin ummah asma'u, ummah asma'u tace toh aikin waye ja'irin yaro? yayi murmushi yace aikin SHUREIM DIN HANNA NE, mummy ta dan dangwareshi cikin wasa, haka sukasa dariya dukansu,
******ummah asma'u tayi murmushi tace wato akwai wani boyayyen al'amari wanda ya kamata ace kaida zaka zauna da hanna kasani, cikin sanyin jiki yace menene kenan ummah? tace ba wani abun tada hankali bane shureim, hanna dai marainiya ce, batada uwa batada uba,ni ummah asma'u bani na haifi HANNA ba, cikin rashin gamsuwa da zancen ummah asma'u, hajia afrah tace ban fahimci zancen naki ba ummah asma'u, mekike nufi da bake kika haifi HANNA ba? shureim ne yace su waye mahaifanta? Ummah asma'u ta murmusa tace uhmmm duka zan amsa maku tambayar ku, amma kuma banan ya dace muyi maganar ba saboda maganar tanada muhimmanci sosai, hajia afrah ta dubi shureim cikin rashin gamsuwa da zancen, shureim yace mummy muje gida mana, ummah asma'u tace aaah shureim kada kadamu kabari ka samu sauki mana ayyi ba abun barin gari bane,ina nan ba inda zanje ta fadi hakan tare da murmushi a fuskanta
**********hajia afrah tayi shuru, duka jikinta yayi sanyi sosai, sosai takejin gabanta yana faduwa kaman zai tsage, dubanta ta kara maidawa kan ummah asma'u dake sunkuye da kai tana wasa da dan yatsanta,ahankali take kara yiwa ummah asma'u kallan tsabta kaman zata cinyeta, shureim da ya gama karanta irin kallan da mahaifiyarsa keyiwa ummah asma'u yasa ya katse shurun da amma ummah na tambeki? Sai lokacin ta dago kai tare da cewa ina jinka, yace amma dai kunada alaka da hanna koh?ummah asma'u tace uhmmm sosai kuwa badai ni na haifeta ba amma nima matsayin mahaifiya nake gareta, ko bakaga kama bane? yace ummmm naga tafiki kyau ne sosai, ummah asma'u tace uhmmm duba dai da kyau kagani kaganka shureim, haka suketa wasa da dariya, ita kuwa hajia afrah ta kasa uhmm bare hmm tunda ummah asma'u tayi maganar ta kasa cewa komai
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞
Start from the beginning
