💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞

Start from the beginning
                                        

******hajia afrah tace ina hanna? ummah asma'u  tace wallahi ina nan kwance taman sama ko kasa ya kanyu ta fita aiki saboda bacci nake kiranki ya tadani, hajia afrah tace Allah sarki toh yanzu dai gani nayi maki tattaki ko yau da kokon barana nazo kaman yanda nazo dashi farko, dan Allah ummah asma'u kiman rai, ki taimakaman, wallahi shureim kadai ya rageman duniya, banida kowa bayan shi, nasan kinfi kowa sanin zafin haihuwa ki fahimceni mana, wallahi bazanso shureim yayi zabin tumun dare ba, kowa ya yaba da hankali da natsuwar hanna itace irin macen da nakesan shureim  ya aura, ki aje zancen kudi gefe, wallahi bazaki samu matsala daga bangarena ba, bangaren shureim kuwa nasan halinsa sosai wallahi bazaa samu irin matsalar da kike tunani ba, ummah asma'u tayi murmushi tace toh hajia afrah ayyi inaga baa neman aure cikin aure, saboda yanzu haka zancen da nake maki malam habibu ya mata miji shekaran jiya ma taje ganinsa wallahi, kuma ba laifi alhamdulillahi, sedai kash nima karan kaina basan auren nake ba saboda sosai hankalina ya kwanta akan  shureim, amma ya zanyi, kinsan bani nake da iko akan hanna ba, hajia afrah tace keko kikeda iko akan hanna saboda ke kika bata tarbiya, kika kula da ita har takai wannan matsayin, sedai idan baki shirya bani auren hanna ba, amma na tabbatar kema kinada babba matsayi agurin hanna duk yanda kikace haka din ne, amma bakomai nagode, amma kada kimanta da'a ma na kowa ne, nabarki lafiya, haka ta mike tayi tafiyanta, ummah asma'u kuwa kasa motsi tayi saboda ta rasa yanda zatayi, dakyar ta iya tashi tayi sallah, kana ta zauna akan sallayar tana nazarin kalaman hajia afrah, haka har akayi la'asar tayi sallah, amma hanna shuru bako motsinta acikin gidan, haka ummah ta mike ta sauya kayanta, kana ta fita itama

******shigar hajia afrah dakin da  shureim  yake kwance ba wuya ta samu friends dinsa sunzo gaida shi, ganinta yasa suka sunkuya har kasa suna kai gaisuwa, ita kuwa cikin sakin fuska take amsa musu, shureim dake zaune, an dora masa fillo abayansa da tea cup hannunsa sai smiling yake abunsa,mummy yake kallo wacce yanayinta yaga ya sauya sosai ba kaman yanda ya saba ganinta ba, haka cikin muryar kulawa yace mummy are you okay? Mummy tayi murmushi tare da kai dubanta kansa tace lafiya lau son just stress, ba dan ya yadda da zancen nata ba yace okay, nan ta fice daga dakin ganin friends dinsa, a'alim ya mike tsaye ya biyo bayanta, zaune ya sameta akan kujeran da ke gefen kofar dakin shureim, ahankali ya sunkuya har kasa tare da dora hannunsa akan kneels dinta yace mummy lafiya kuwa? tace uhmmm a'alim yanzu kam i don't know what to do? I have to tell him d truth zan iya jure duk wata rashin lafiyar da zaiyi amma bana tunanin hanna will b his, cikin rashin fahimtar zancen a'alim yace kamanya kenan mummy? Ina kika fito ne mummy ? shuru tayi bata bashi amsar tambayar sa ba,yayi murmushi yace cen kikaje koh mummy? sai lokacin tace uhmm a'alim cen na fito, nan ta kwashe komai ta gayamasa, a'alim kuwa baisan lokacin da yakai zaune ba yana kallan mummy, idanuwansa sun rine sunyi jawur, mummy kuwa dakyar ta iya lallabarsa ya tashi ya zauna gefenta, cikin rawar murya yace ina kika samu number ummah? tace awayansa na dauki number harda ta hanna, but nayita kiranta hanna but unavailable, a'alim ya Shafa kansa tare da cewa hasbunallahu wani'imal wakil, innalillahi wa'inna illaihir raju'un, anya mummy shureim zai iya SALLAMAR SO kuwa? dubansa tayi kana tace nima karan kaina tambayar da nake yiwa kaina kenan,  a'alim yace uhmmm amsar daya ce mummy, tace what? yace never bazai taba SALLAMAR SOYAYYAR HANNAH ga kowa ba, dix ix d one thing am very sure of, mummy tace nima karan kaina nasan he can't, nd he will never try to

*********hajia afrah ta maida dubanta kan a'alim  tace, na rasa shureim kenan a'alim? kaman daga sama sukaji ance baki rasa shureim ba kuma bazaki taba rasa shureim ba saboda HANNA ba saidai idan lokacinsa ne yayi, mikewa sukayi tsaye dukansu tare da maida dubansa inda suka jiyo muryar, hajia afrah dake zubarda hawaye ta nufeta cikin hanzari tare da hugging nata tana fadin nagode kwarai ummah asma'u, Allah ya saka maki da alhairi, sosai take kukan hajia afrah, ummah asma'u kuwa batasan lokacin da hawayen suka zubo mata ba itama, dakyar ta iya lallashin hajia afrah suka zauna, a'alim ya sunkuya har kasa yana gaida ummah asma'u tare da mata godiya, ummah asma'u tace saidai wani hanzari ba gudu ba hajia afrah, wallahi na nemi HANNA sama da kasa na rasa nayi kiran number ta akashe, a'alim yayi murmushi yace bataje aiki ba yau? ummah tace bata gayaman zataje ba, hajia afrah tace kada kidamu ayyi hanna ba irin sauran mata bace, zata dawo, na tabbatar wani abu mai muhimmanci ne ya fitar da ita, farin ciki gun a'alim kuwa baa cewa komai dan ya tabbatar daga wannan lokacin abokinsa zai kasance cikin farin ciki da nishadi, hajia afrah tace uhmmm nagode sosai ummah asma'u, wallahi harna sadakar da zan rasa shureim har lahira

❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤Where stories live. Discover now