💞💞💞💞SALLAMAR SO💞💞💞

Start from the beginning
                                        

*********bayan fitar hajia afrah kuwa driving take tana smiling, wani nauyayyan numfashi ta saukar irin nasu na manya tace lallai HANNA kinyi dacen miji, kinyi dacen abokin rayuwa, tabbas na yarda da sonda shureim yake maki, tabbas shureim yana sonki, guri ta samu tayi parking kana ta dauki wayanta tayi dialing number ummah asma'u, harta karasa ringing baa daga ba kira uku ta mata jere da juna amma babu wanda aka daga, kanta ta hade da sitarin motarta tare da lumshe idanuwanta ahankali, ta dauki lokaci mai tsayi ahaka ringing din wayanta yasa ta zabura tare da daukan wayan da ke kan hips dinta, tana dubawa taga kiran ummah asma'u ayyi bata jira wata ba ta daga kiran, bayan sun gaisa, ummah asma'u tace dan Allah wake magana? Mummy afrah tace nice nan ummah asma'u meyayi zafi maman hanna? ummah asma'u tayi shuru nadan lokaci kana tace wannan kaman hajia afrah saboda ita kadai ke kirana sa maman hanna, hajia afrah? mummy tayi murmushi tace gaskiya bakiman adalci ba ummah asma'u, haba dan Allah, ayyi bamu muka maki laifi amma kika dauki laifi kika doramana haba dan Allah, yanzu haka danki yana hospital kwance ba lafiya, zan ma iya cewa rai ga hannun Allah, ummah asma'u tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un, badai shureim ba? mummy tace kinada wani da'a bayan shureim, wallahi ummah asma'u abun dai baa cewa komai, ummah  asma'u  tace yanzu kuna wane asibitin kenan? hajia afrah tace yanzu ke kina ina?  saboda na fito kuma wallahi magana nakesan nayi dake mai muhimmanci, ummah asma'u tace kizo ina gida, nan ta gayamata unguwarsu hajia afrah tace yanzu nan zatazo, suna karasa wayan tayiwa Allah godiya kana ta kama hanyar zuwa gidan su HANNA

*********ummah asma'u tana karasa wayan da hajia afrah  tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un, Allah ya baka lafiya shureim, haba biri yayi kamada mutun nidai nasan shureim bazai taba saba alkawarin da ya daukarman ba da ransa da lafiya, Allah dai ya baka lafiya shureim, in sha Allahu zaka samu sauki da yarda Allah, nan ta mike tsaye ta nufi dakin hanna wanda yake a bude, taganshi wayam bakowa, wani ya mutse fuska tayi kana tace ita kuma wannan yaushe ta fita banida labari, nan dai ta fitowanta ta koma dakinta,

******hanna ce zaune a karkashin wata bishiya ta zuba wani uban tagumi murya cen kasa tace na shiga uku ni HANNA, yanzu kuma ya zanyi, ko me hajia afrah take nema gun ummah oho, toh ni menawa aciki dan shureim bashida lafiya, Allah yasa ya mutu, ni wallahi nagaji da wasa da hankali da samari keyi, hassan left saboda ina diyar talakawa, khalid left saboda kishin taiya, Allah kadai yasan samarin da nayi suke rabuwa dani saboda nasu dalili, anya bazan gudu nabar garin nan ba kuwa? Saboda wannan itace kawai mafita agareni, nan dai tayi shuru

*******cikin 30minute hajia afrah ta karaso gidansu hanna, nan tayi knocking aka bude mata, ummah asma'u tace wata sabon gani ashe rai kanga rai, hajia afrah ta tabe baki tace Allah kin man ba dede ba maman hanna, nan dai suka karasa cikin gidan, inda suka shiga dakin ummah asma'u, suka zauna a gefen gadon, bayan sun karasa gaisawa ummah asma'u tace toh kiyi hakuri, kinsan ba laifina bane? Hajia  afrah tace toh ki sanar dani abunda ya faru mana? ummah asma'u tace toh........ Nan ta kwashe komai daga farko har karshe... Hajia afrah tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un tabbas kunsha wuya kuma kun wahala, ki godewa Allah, ya baki diya mai zuciya da kuma neman na kanta, yanzu da wannan duniyar ta lallace bako wane yaro bane zai nemi na kansa ba, Allah dai ya kara rufa asiri, amma a labarin ki kinceman banan kuka fara zama ba menene ya dawo daku nan? Ummah asma'u tace toh nidai hanna taceman wai megidan ne ke bukatar gidansa, nima ina zaune acikin gidan naga dillale ya shigo yaceman hanna ta aikosa su kwashi kaya, wallahi sosai nayi mamaki amma yana iya tunda kinsan halin yar taki, hajia afrah tayi shuru tana kallan ummah asma'u

*****bayan dan wani lokaci tace wato dai wannan lamarin yana bukatar bayani, ummah asma'u tace wane lamari kenan? hajia afrah tace toh nidai iya abunda nasani shine a'alim abokin shureim yagayaman cewa gurin hanna shureim  yaje daga cen ne aka dauko shi sai hospital, ummah asma'u ta dan dubi hajia afrah cikin rashin gamsuwa tace inda hanna kuma? amma ni hanna bata sanar dani zuwan shureim ba, sannan tunda muka baro gidan hajia maryam hanna bata sakeman firan shureim ba, anya kuwa biri zaiyi mai bana? hajia afrah tace uhmmmm wato dai wannan shine ake kira da SALLAMAR SO, ummah asma'u tace kamanya SALLAMAR SO? hajia afrah tace HANNA, HANIFA, da shureim sune sukasan amsar tambayar?

❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤Where stories live. Discover now