*********ta dauki dan lokaci ahakan kana ta dan nisa ta dauki plate din tana cin abincin nata wanda cinsa kawai take badan yana mata dadi abakin ba,ko wani abincin kirkin bataci ba ta aje plate din ta shiga bandaki, tayi wanka ta fito tayi arwala kana ta koma dakin nata, ta shafa cream, ta dan shafa powder da lip gloss, ba karamin kyau tayi ba,cikin kuwa ba wata kwalliya ce tayi ba,haka ta shirya tsab cikin t-shirt dinta ta aiki, ta saka straight sket dinta black, ta saka dan hijab dinta dogo har kasa sky blue, ta feshe jikinta duka da arabian perfumes masu kamshin gaske, kana ta dauki wayanta da jakanta ta fito harta fito taji ana kiran sallah, hakan yasa ta koma ta gabatar da sallah zuhur kana ta fito, kara komawa tayi ta dauko nikab dinta ta fito, ta rega dakin ummah taganta tana bacci bata tada ita ba sai ta saki kyallen dakin ta fice abunta, tana fita kofar gidan ta dubi damanta da hagunta kana ta daura nikab din nata, ta kama hanya, tafiya take ahankali kaman batasan taka kasa
************* bangaren su shureim kuwa tunda safe ya fita neman hanna, duk inda yaje sai ace ba'a ganeta ba, haka ya dawo gidan nasu jikinsa ba kwari, washe garin ma haka ya fita neman still no available, yau kam kasa fita yayi dakinsa yake zaune abakin gado ya rasa gane abunda yake masa dadi, zuciyarsa har kuna take, ransa baya masa dadi, komai na duniya baya masa dadi ya rame, yayi haske sosai, kofar dakin aka turo bakowa bace face hajia afrah mummy, bakinta dauke da sallama amma hankalinsa baya kansa shiyasa ko amsa mata baiyi ba, harta karaso tayi tsaye agabansa, cikin kulawa tace har yanzu baka ganta ba? sai lokacin ya dago kansa sama yace hmm wallahi mummy ko ina naje amma babu wanda yasanta, bansan sunan da ake mata ba, har anguwar da suka fito naje amma anceman tun lokacin da sukabar anguwar busu kara dawowa ba, mummy ta dan nisa kana tace uhmmm shureim kenan, ka kwantar da hankalinka am sure iya zaman da kukayi akwai hint na inda take zuwa ko kuma kuke zuwa tare wanda ko tantama bakayi idan ta rasa gurin zuwa zataje cen🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃
***********shuru yayi yana kallan mummmy, kaman wata sabuwar bakuwa agaresa,murmushi tayi masa mai dauke da tausayi tace toh tunda ka kasa gano komai let me show u d way, gefensa ta zauna kana tace kaje gurinda take aiki? cikin hanzari yace wallahi mummy na manta ga baki daya,mikewa yayi tsaye ya dauki car key dinsa, cikin hanzari ya sunkuyo yayi kissing cheeks dinta ya fice da gudunsa, tayi murmushi ta mike tsaye tace uhmmm shureim na hanna kenan, nima karan kaina akwai yaki agabana dan tabbas yakamata naga ummah asma'u naji shawarar da ta yanke, haka ta fito dakin da tunanin yanda zataga ummah asma'u, tana fitowa tasa daya daga cikin ma'aikatan gidan gyaran dakin shureim ta fice zuwa nata dakin
***********bangaren hanifa kuwa tunda ta tashi da safe tayi wanka ta shirya tsab cikin wata gown red rigan ta kama jikinta sosai,tayi parking da gashin kanta har gadon baya,fitowa tayi, taji gidan tsit, mummy ce ta fito daga kitchen tana jera kayan breakfast, hanifa tana zaune har mummy ta karasa jera kayan, ko sannu babu bare mummy kawo na maki, mummy tana karasa jera kayan tayi serving hanifa, chips ne da sauce na kwai sai checkup dinda ta saka mata gefe, kana ta hada mata tea mai kaurin gaske, haka hanifa ke cin abincin itama mummy haka tayi serving kanta, shuru sukayi babu wanda ya iya magana, mummy ta katse shurun da hanifa you can't even say good morning to me, meyasa kike rayuwa irin wannan? kin manta cewa kema zaki haihu how will you feel idan danki ko yar'ki ta maki yanda kikeman? hanifa ta dan nisa kana tace kai mummy, meyasa kikesan man haka? am already moody wallahi, nd what's so special about d morning? dan Allah kidaina banaso, just let me b, mummy tace toh Allah ya kyauta, haka ta cigaba da cin abincin ta
*******bayan sun karasacin abincin, mummy ta kwashe komai taje kitchen ta aje, hanifa kuwa direct dakinta ta fice, mummy ta dawo falo ta zauna, tana tunanin irin yanda tayiwa ummah asma'u wulakanci saboda kawai farin cikin hanifa, amma gashi hanifa ko kallan albarka bata mata, wani nauyayyan numfashi ta saukar irin nasu na manya kana tace tabbas ko wacce uwar kirki bazataso danta ya auri mai rayuwa irin ta hanifa ba, tana cikin zance da zuciyarta taji sallamar hajia barakah, tana juyowa taganta, tace uhmmm manya masu gari sai yau? hajia barakah ta karaso ta zauna suka gaisa sosai, kana tace kedah bari kinsan zama ba namu bane, how far ina hajia afrah? mummy ta tabe baki tace before that mezan kawo maki? yanzun nan muka karasa breakfast wallahi, hajia barakah tace aaaah na koshi nikam just give me soft drink haka, haka hajia maryam taje ta kawo mata lemun kwali mai sanyin gaske, haka takesha suna taba firansu ta manya mata
YOU ARE READING
❤❤❤SALLAMAR SO❤❤❤
Short StoryLabari ne akan matasa mata biyu, yar' masu gida da kuma yar' masu aiki, Amma dai kubiyoni musha labari dan sanin menene yake shirin faruwa, maman hanna taku ce kuma nawa ne 😍😍😍😍😍😍
💕💕💕SALLAMAR SO💕💕💕
Start from the beginning
