ZAB'IN WA ZANBI? 11

491 27 0
                                    

Jabo ina kika shiga wajan kwana biyar ina neman layinki, ke kuma ko ki kirani?.

Manyan kinga yanda kika koma, lallai auren ya amsheki, inji Bena, dariya suka saka, xaunawa sukai a bakin gado
Bena ta manta haka akace tazo sugaisa da kishiyarta, ita ma Jabo ta manta, Mom tamata waya tace ga abokinyar zamanta zata shigo
Hira suke sosai, harda sako labarin NWA da yanda sukeso komai ya tafi daidai, Jabo ce tace Ina Aunty YBK?, kwana biyu naga bata online ko haryanzu basu gama exams d'in ba?
Sun gama, jiya ma ta hau, kecedai kowa yafaraiwa tsiya, dad'i miji kin mantamu
Dariya tayi tace nida miji zai kashe, wallahi kuma Bena da akecewa 'yan sokoto suna shan magani, nifa bansha da yawa ba dan har Mama nacewa tagayan Mama na tace a dena bani, banqi ba, naci (jelar ayii), da kaza mai had'a da nonon rak'umi amma bayan haka wallahi kad'an naci komai.

Amma idan kinji yanda naji, saikace ana..... kedai bari, na gurzu, d'an mutumin baimin a slow ba
Dariya Bena takemata ganin ahaka ma idonta yacika da qwalla, huum nifa abin ba sauqi, naxata bazan k'ara moruwaba, amma gashi yanzu harna saba, tunda Kishiyata bata da lafiya, wajena yakoma, ai Jabo naga ta kaina, kinsan washe gari saiga Mamu, tamun waya wai ya labari? Kiji wallahi idan bakeba banga wadda zan fad'awa sirri na ba, kema d'in ba komai ba.

(Ina ganin rashin hankali da wawancin 'yammata da suke zama suna bawa k'awaye labarin abinda ya faru tsakanin su da maxajen su, haukane wannan kuma manzon Allah yayi hani akan haka, plx koda hira ta kama kayi, to kasan da irin wad'anda xakayi, Allah yasa mu dace)

  Ai Jabo saidai hak'uri amma idan
Allah ya baka miji mai kwakwa ba yadda xakayi   jarumine mijina gaskiya kuma yanada hankali SMS
Da sauri Jabo ta d'ago ido tace waye mijin ki? Sameer ai nan gidan surukaina ne, Abbun sa  zai dawo yau shine mukazo, Maman sa tace wai abokiyar zamana tana sama nazo mu gaisa, ni kuma naganki na shan take tana ina?

Ai jijiyoyin jikin Jabo ne, suka dena aiki na 'yan sakanni, jitayi kamar a mafarki, indai haka ne kuwa Benaxir ta tabbata itace Kishiyar ta?.

Bena ce tace, Jabo nan gidan 'yan uwan kune? A'a gidan Mom ne, SURUKATA, banganeba kina nufin kice SAMEER shine mijin ki? tabbas shine, indai hakane kenan kece Hauwa?, kada nashiga rud'u.

Itadai Jabo gaba d'aya ita tatafi wata duniya daban, kenan duk hirar da suke, dama mijin su d'aya?, dama suna zaune gida d'aya suke hira?, kenan Bena itace uwar gidan ta, ZAB'IN mahaifinsa?, yanzu duk shawarar da suke bawa juna dama miji gida zasu aura? meye abinyi yanxu.

Duk maganar datake batasan tafito fili ba, sai jin maganar Bena taji tace abin yi shine mu d'auka dama haka Allah yaso, kuma k'addararmu tazo a haka, tunda had'uwar online mukai dake, ba garin mu d'aya ba, ba tare mukai school ba, balantana nasan saurayinki ko kisan nawa, kinga kenan rubutaccene wannan auren daga rabbi samawati.

Fatana tunda munsan juna munsan halin juna, kuma munsan cewa abokan zama muke, muyi hak'uri mu rungumi mijin mu, muyi masa biyayya mu taimaka masa, wajan sauke hakkin kowacce
Koba haka ba?.

Tafi su kaji yo a bayan su, juyawa sukai Mom, Abbu, Sameer, sune abakin k'ofa suna murmushi.

Qarasa shigo wa sukayi, zama sukai, Mom ce tace ubangiji Allah ya had'a kanku, Allah kuma yasa abinda mu kaji kuna fad'a har zuciyarku, kurik'e juna da aminci.

Kaikuma Sameer kagansu k'awaye ne, nikaina shaidace saboda yanda naji sunayin waya da hira da chat, saboda haka kaxama mai adalci tsakanin su KA rik'e sirrin kowacce
Mom nima fa nasan tsakaninsu, dan babu wadda bataban labarin junansu, Allah yayimuku albarka
Rungume juna sukai suna masu farinciki.

A haka aka sakko akaci abinci, daga nan sai hira, ranar dai gidan Mom aka kwana
Washe gari suka tarkata suka koma gidansu
Zama ne ake naso da juna, da mutunta juna, da amana, shi kansa maigidan sosai yakejin dad'in halin matansa, komai tare
Idan wannan keda girki, to saikaga wadda ba itace da shiba hartafi mai girkin yin aiki
Hauwa datake 'yar sokoto, sosai ita ke had'a musu abinda jikinsu zaiyi kyau, babu cuta
Kowa yazo gidan, sai sun baka sha'awa, duk da ance tsakanin harshe da hakori ana sab'awa, to kosunsami sabanin baya zuwa ko ina.

Dakansa yakai kowacce gidan su, tare sukaje kuma tare suke kwana, k'awaye nasu duk suma sunsan kishiyo yine, amma babu mai maganar wata agurun wata, saboda babu fuska.

Bayan wata bakwai

Daga Bena har Jabo nagani da qaton ciki, kowacce tayi nauyi, shikuma yana zaune tsakiyarsu Mango da Cherie (Agwaluma) yake yan kamu su, gaba d'aya yanxu shine abin tausayi, saboda wahala suke bashi, daga wannan tace wannan sai wannan tace wancen.

Yanxuma Jabo ce tace Cherie take so, saidaga siyo, tace baby mango yake so, haka yaqara komawa ya siyo
Yana shigo wa Benaxir tace itakuma manyan mango take so irin mai smenting nan, harara ya watsa nata, dariya suka sheqe da ita.

Tsakani da Allah, yanxu bakwa tausayamun, daga wannan sai wannan, Benaxir ce tace, nidai idan baka siyo mun ka fad'a , naga banice ke soba, d'anka ne yake so, tana gama fad'a ta juya masa baya.

Ganin yadda ta juya, yasaka bashiri ya juyo da ita, peck yamata sannan ya fita
Dariya suka saka, masa ganin yanda yafita
Yana dawowa sukace ya zauna, ya yanka, haka yake musu idan yabawa wannan saiya bawa waccen
Dama Jabo uwar ci, haka take cin nata, taci na Benaxir. Bena sarkin hak'uri saida tayimata murmushi kawai.

Mom kullum ana hanya, za'ayi jikoki har biyu lokaci d'aya
Yau tunsafe Benaxir keta naquda, sosai Jabo hankalinta ya tashi, ganin yadda Bena ke yada kai, gashi sunzo asibiti nan ma, shiru.

Mom hankalinta itama ya tashi, sosai addu'a take mata kan Allah ya sauke ta lafiya
Jimawa kad'an itama Jabo tafara labour, hangomun SAMEER gashi kwarraren likita amma yakasa komai, akai, sai da taimakon Dr Sa'adatu da Dr Ummul fadeela, Allah ya kawowa Bana haihuwa.

"Twinc duka mata, wayyo murna, haka aka gyara mai jego
Can kuma, itama Allah ya sauki, Hauwa lafiya Lou, tasami d'anta namiji amma Allah tayimasa rasuwa
Kuma gashi kamar su d'aya da Sameer babu Inda ya barshi, haka akayi masa, wanka pic ya d'aukeshi, daga nan aka kaishi gidan sa na gaskiya.

Kuka sosai Sameer yayi, saboda yadda yakeson yaga d'an Hauwa, kuma yaron yashiga ransa
Zuciyarsa tanason Hauwa sosai, Benaxir kuma yana girma mata saboda macece mai hankali da hak'uri, saboda haka yaji d'acin mutuwar Mohd sunan daya sawa Babyn.

'Yan uwan Hauwa da Mom tasa sosai suke farinciki Hauwa nada ciki
Ashe duk abinda Hauwa take Babyn baxaizo da raina, haka Allah yaso
Benaxir itama saidatayi kuka na rashin Babyn k'awarta, sosai mutuwar ta bigeta.

Lokacin da aka sallamesu, gida suka koma, part d'in mai gidan duka aka koma
Jabo itama tayi shar da ita, anyi mata wanka, 'yan uwanta sunzo wad'anda suke kusa
Lokacin data shiga wajan Benaxir duka kowa yana zaune, karb'an Babyn tayi, sosai ta musu addu'a
D'ayan ta karb'a shima tamasa, hawaye ta share, Benaxir ce tadafa kafad'arta, tace kiyi hak'uri haka Allah yaso.

Wadda take hannunta Babyn ta karb'a, maidamata ta k'arayi tace, ga Babyn ki duniya da lahira, 'yarkice halak malak nabaki ita
Juyawa tayi, tace Ya Sameer nayi abu bada shawararkaba, ina fatan banyi laifi ba
Bakiyiba, yace haka kowa yasamata albarka, sosai Hauwa taji dad'i, godiya kawai take zubawa
A ranar kowacce tafara bawa nata Babyn Mamma.

'Yan gidansu Benaxir tun ana gobe suna, sukazo, tareda matan yayunta Sofy da Fido wad'anda suma haihuwa ko yau ko gobe.

Kayan barka masha Allah, kunsandai basaina tsaya b'ata bakina wajan fad'a ba, komai dai gashi nan
Dangi koina sai xuwa suke, daga na Hauwa harna Bena.

Yara sunci sunana, Fatima da Xahra Allah yarayasu cikin Islama.
Auta ce

ZAB'IN WA ZANBI? Where stories live. Discover now