ZAB'IN WA ZANBI? 1

2.2K 88 0
                                    

Tafiya nake ina d'an waqata da littafina a hannu,ga yunwa da qishirwa sun daman,amma a haka na rantse yau baxan koma gida ba saina samo labarin da zan bawa makaranta.

Ganin har 5 tamun ba labari gashi na gaji,yasa nace bara na koma gida, harna juya sainaga wata "budurwa black beauty, da baqan doguwan riga,tayi rolling da mayafin,ga gashinta abaya yayi tum tum ga wayan a hannu ta tana d'an matsawa..gayu nace a zuciya ta.

Harzata wuce sainaji kamar inmata magana,amma kuma saina kasa
abaya naringa binta,idan naa zata juyo sainai maza na b"oye. Wani gida naga tashiga gate en gidan kansa abin kallone,haka naga "gate man d'in ya bud'e mata yana sannu da zuwa"Hajiya Bena,sannu baba ya aiki? aiki k'alau yar gidan Hajiya
Suna wanga magana nasa mu na shiga.

Wata qofa tayi nan ma binta nayi
Mama,mama,na'am yar gidan mama, ya kika dawo? lafiya lou
Adda Beebalo'n tace tana gaidaki, ina amsawa.

Ya Ahmad ne ya fito daga d'akinsa, wallah wannan yarinyar tafiya yawo daga taje wannan gidan sai taje wancen,salon ta b'ata ko mota ta bigeta taxo tanawa mutane raki.

Mama kinji shi koh, fata yakemun na mutu,kuma bazan mutuba, har sainaga jikokina"
Insha Allah,saidai shi ya mutu,nalura kafiya takurawa Benaxir, Abba ne yake wannan maganan.

Yauwa Abba fad'amasa dai, kaima nasan zaka mutu tunda kace bazakayi aure ba,Sofy  tana sonka amma kaqi ka amsamata,kasan dai ba baya bace gata fara,kowa yasameta a matsayin mata ya dace.

Ke ni rabani da ita,daga gani zatayi masifa,nikima ban iya fad'a ba
Abba kaji?, komai akace saiya fad'i aibun mutum,shidai Abba dariya kawai yake.

**********
Wacece Bexanir?.

Benaxir 'yace ga Eng Omar bauchi, itace ta uku gurin babanta da mamanta,tanada yayu biyu, Ahmad da Abbas, wad'anda yanxu haka sungama karatun su suna aiki a matatar mai na qasa baki d'aya NNPC, Ahmad shine manager awajan"Abbas kuma Director sosai suke da rifun asiri.

Babu wanda yayi aure cikin su
Qauna, kulawa, tattali, babu wanda basa nunawa k'anwarsu Benaxir idan kagan su a gidan su bazakace suneba, suna maida kansu qanana dan sufarantawa qanwarsu rai.

Komai take so suna mata, duk da haka idan tayi ba daidai ba, sai sun nunamata.

Tanada tarbiyya dai dai gwargwado, batada qiwa ko hayaniya
Yanxu haka,tana level 300 a ATBU dake garin bauchi, Islamiyya agida ake xuwa yimata, malami guda aka ware mata dan yaringa biya mata dukkan abinda Allah ya saukar na hani da kuma aika tawa.

Sunada 'yan aiki a gidan su, amma hakan baisa Mamanta tayi sanya wajan koyamata girki ba da kuma wasu abubuwan wanda zasu amfane ta nan gaba.

Benaxir takasance mace tamkar da goma wajan iyayenta, saboda xumuncin da take dashi, ako yaushe burinta ta xiyarci danginta tare da abin arziqi, shiyasa Ya Ahmad yakemata tsiya tunda shi baya zuwa
Maganar samari kuwa bata kulasu saboda cika umarnin mahaifinta nahar saitagama karatu,amma duk da haka batada shariya in dai anmata magana tana d'an yimu su.

    
wnn kenan.

Benaxir baxaki fito ayi dinner ba? kin zauna typing novel en tsiya, abinda ba kud'i xa'a baki ba saima wataran kisha zagi gun fans d'in naku.

Sakkowa tayi cikin takunta na gayu tace Ya Ahmady kenan, aini badan kud'i ko nayi suna nakeba, inayine dan nishad'i da kuma fad'akarwa ga jama'a masu irin halin danasa a book nawa.

Wani kuma wa'azine, ai ba shirme mukeyi ba, kuma nasan duk abinda muka fad'a wani gaskiya ne,koba haka ba Mama?.

Hakane d'iyar albarka, dan bakaji yanda ake yabon marubuta ba,kuma nasan 'yata tana daga cikin masu rubutu mai ma'ana da kyau
Huum, Mama da 'yar ta, ke kuma kyace nabaki kud'in data ko nacanjamiki Waya tunda ina magana kina k'arya Tani ya fad'a yana d'an hade rai.

Haba yayana na kaina, katangar sukari,mai rabani dakai sai yashirya
haka tayi ta masa dad'in baki, ganin ya sakko, tace
"Yaya"
"Na'ama" yauwa ina wayan dana gani gunka ran nan?
wacce fa? wata mai kyau sosai? OK sabuwar IPhone 7+ ce
dubu d'ari uku kenan
Au, menene? ba komai.

Ya Abbas ne yace ko kina so ne?
wallahi kuwa Yaya tayi kyau, dan naga itama Jabo tace tayi new phone jiya,shine kema kike so?eh
dariya ya Ahmad yayi yace,kaji koh ita kullum a canja waya
Idan ba zaku bata ba, ku rabu da ita
Sosai family'n suke bawa kowa sha'awa.
  Dariya sukai kana Ya Abbas yace haba Dady za'a bata, the only sister d'in mu ce fa we can do anything for her indai abin mai kyau ne.

Yauwa Allah yamuku albarka..ya k'ara muku son juna..Ameen suka amsa lokaci guda.

   Yaya dana inason tambayar ka?, inajin ki sis. Uhmm kaga..dama inason 20k ne wallahi kayan make up d'ina sunyi low gashi zamuyi birthday na k'awata ya za'ayi?.
 
Don't worry ki shirya sai muje nima zan fita anjima sabida akwai wani abu danake son dubawa.

  Tnx ta furta cikin husky voice nata kana ta haura sama ta shige study room dan duba wasu handouts data shigo dasu jiya.

Votes and comments u guys..

ZAB'IN WA ZANBI? Место, где живут истории. Откройте их для себя