ZAB'IN WA ZANBI? 6

414 27 0
                                    


Sakkowa tayi daga benan a hankali, ta zauna kusa da Ya Ahmad, tace Ya Ahmad yanxu wai kunshirya da Sofy naga jiya kunjima kuna waya harda I like ur lips, duk da yana jin haushinta hakan baisa yayi shiru ba saidaya dara.

Ya Abass kaima ai kunsasanta da Fido saboda haka kaga sai ayi magana a had'a bikin mu tare, Mama kinga sai abin yafi armashi koh?.

Sosai suka shiga shock Jim cewa tana maganar biki kota haqura?
Mama ce tace Benaxir ai kince bakiso kinga shima yayanku yace baruwansa da qawarki Sofy 
Haba Mama ai magana ta wuce, itama Jabo ashe bikinta za'ayi nanda 2 weeka ,  Wallahi naso zuwa sokoto Allah baiyiba.

Tunda lokacin bikin mu yazo d'aya, itama bata mijin akayi, kowa datasa qaddarar saboda haka Allah yasa haka shine mafi alkhairi.

Sosai iyayen sukai murna,ai ba'a jimaba,Su ya Ahmad suma Abba yafara masu shirye shirye, anje gidan iyayen amaren anyi magana ansa nan da sati biyu idan yaso koda basu gama komai ba, sa tare daga baya
Haka akayi kwana biyu tsakani aka kai lefe, gidan su Sofy matar ya Ahmad shi aka fara zuwa, anmisu tarba ta mutunci, sosai dangin su Benaxir sukayi murna saboda sunsan sun auri 'yar babban gida.

Ya Abbas budurwansa Fiddausi suma gidansu gidan dattako ne, kowa yasan familyn Sodangi family ne na gari da ilimi da karamci.

Mom! Inajinka wai ni jiya naga Dr MD  da magashi suna maganar bikina kece kika fad'amus? SMS ne ke wannan tambayar?.

Eh nice naga kamar Baka d'auki auren da Mutunci ba tunda wallahi dana baka number Hauwa daka kirata zata fad'a mun amma na zuba maka Ido kayi abinda kake ganin shine right a gunka.

Haba Mom, wallahi naso zuwa har sokoto'n Allah ne baiyi ba kuma kinga yanxu an shiga hidima
Amma ban number'n ta, in tambaye ta kota nason yin wani Abu? Eh lallai wato *ZAB'INA* bashida amfani tunda har baka da number ta, kuma  ainaji kuna magana da Abbu cewa kajegidan Eng Omar gurin Benixariy ko Benaxir?.

Mom nifa banjeba kuma ai dole kinsan ZAB'IN KI shine ZAB'INA nayiwa Abbu biyayya ne kawai
Yauwa, haka yayita shigar da ita, shima haka yayiwa Abbu yace ZAB'IN sa shine ZAB'INA sosai take murna jin anfison ZAB'IN ta.

Wayar tace tafara ringing, harxata share saita ce Son miqomin  wayana, sunan Hauwa data gani akan screen en wayar, shine tabata damar d'agawa had'e da murmushi
"Hello"
"Mom, ya gida ?
Lafiya lou 'yata kuna lafiya dai? Eh
Mom dan Allah ki cewa Mami tadena bani wannan tsimun tun yana dad'i yanxu ya dena
Dariya tai tace hoo! Hauwa shirme banda abinki ai 'yanci zamu nemomiki agurun abokiyar xaman ki, sosai ta shiga shock itafa tamanta Mami tacemata su biyu zaya aura
Huum, nidai banso, to kice banso, tom xancemata shi kenan? Eh

Ga yayanku zaku gaisa, jibi zaizo kuma dan ma yau yana aiki, kinsan anaso abud'e masa asibintin sa ranar  d'aurun aure, amma jibi ki saurareshi
Ungo, wayyo takaici, shifa wallahi su Abbu sun gama dashi, inama laifin mace d'aya amma 2 lokaci d'aya gaskiya abin da dubawa, shi bayada idon ganin matar aure da har sai an samomasa, kuma bama 'yan kano ba, Sokoto da bauchi kai...

"Alo" yamanta da waya
a kunnensa saijin wata sanyayyar murya yai, sosai yaji wani yarrr
Ya SAMEER ina yini ya gida, ka dawo lafiya? a hankali yace lafiya Lou, ya kk? normal daga haka duk sukayi shiru, sai shine yace tusbah alal khairi, ya datse wayar
Kaji koh? ai Hauwa badai kirki ba, eh tanada kirki haka yace.

SMS yana zaune yana duba wani abu cikin system nasa, sai wayar Abbu taji,SAMEER maxa kaxo ina waje yanxu, tom Abbu
Boxer ne jikinsa, shiyasa ya d'an tsaya canja kaya, yadine fari ya d'auko yasaka,  fita yai, Abbu yagani atsaye cikin girmamawa yace Abbu gani, yauwa dama wani aiki ya taso yanxu zamu Bauchi shine nace maixaihana katawo muje daga can saika gaisa da Benaxir.. ya Allah ! tom Abba Sameer kawai yace.

Haka ya koma, kayansa ya d'auka kala biyu sai inner wears nasa da abinda ba'arasaba
Sallama yayiwa Mom, cewa tare zasu tafi da Abbu, kuma daga can zai gaisa da Benaxir.

Allah ya kiyaye, amma an nunan banda matsayi tunda ai ni nafara maganar kaje wajan Hauwa shine zaice kafara zuwa.

Zama yayi kusa da ita, hannunta ya kama yace Mom dan Allah tunda na yadda na Amince na karb'i  ZAB'IN ku toki daina banbanta tsakanin su, Hauwa 'yarkice, Benaxir itama haka, wannan abinda kike shixaija tashin hankali tsakaninsu koda bayan auren mune.

Kiso su duk kan su, ki d'aukesu matasyin 'ya'ya, duk da xuciyarki Hauwa  take so, ki danne kidaina nunawa kinji Mom?.

Kuma badan Abbu yazo da magana ba, ai gurin Hauwa zan fara zuwa, kuma ita aikinga mun gaisa koh?
Kai ta kad'amasa, Allah yaimaka albarka, abinda Abbu yace kenan, wallahi Son dama inason nayima Mominka magana tadena haka, duk Kansu 'ya'ya suke wajena amma Mom taka bata d'auki Benaxir akan 'ya ba, bayan kuma mahaifiyar ta tazo har gidan  nan, kuma 'yayansu abokaine wajan d'an ki.

Sosai taji dad'in hakan, nuna musu musu tayi tadena, Amma qasan zuciyarta Hauwa ce star saboda ta taimake ta.

Lefe ma, komai iri d'ayane colour ce ta banbanta, akwatu set biyu akayiwa ko wacce
A gobe kuma xa'a kai.

Bena gobe xa'akawo lefena, haba? nima haka, kinsan maimata xan aura fa? Dan Allah nima haka
Kuma atare xa'a d'aura auren, nima haka lallai xamuci uban Kishiyan
Dariya sukayi Benaxir ce tace haba qawata ai yanxu andena yayin haka, kishi ai yanxu  na nuna kulawa da tattali wa miji akeyi.haka dai sukayi hiransu da yanda xamansu zai kasance agida miji sosai suke bawa juna tips  akan rayuwar aure, amatsayinsu na aminan juna.

Yau Benaxir sai aikin tarbar baqo ake angyara nan angyara can, har lokacin da zaizo yayi.

Shigar ta tayi ta Atamfa da mayafi tayi kyau dama gata black beauty kyakyawa kowa yasan Benaxir afagen kyau ta fito sosai
Shikuma anasa b'angaren, shima yayi kyau, sirrin kyaunsa ya fito haka yai driving kansa zuwa gidan
Maigadine yayimasa iso, har parlour'n gidan,lokacin itama take fitowa daga d'akinta.

Benaxir yazo fa, kiyi sauri, jitayi kamar kada taje,amma yata iya, magana taxama babban tunda gashi yau da safe aka kai lefenta gidan kakanin su batada ZAB'I
Haka ta fita, shiga tayi suka gaisa, idonta a qasa, anan yad'an bata brief history nasa, itama tabashi nata, kinsan dai Ku biyu can aura? nasani tace.

Kanta aqasa, shikuma kuma ahakann ya bashi damar kallonta,beautiful yace, gaskiya ZAB'IN Abbu yafi duk da banga Hauwan   ba, sosai kuma ya yaba da hankalita.

Da hira yad'an jata  kad'an itama haka, hartake bashi labarin qawarta Jabo da yanda suke, Huum kenan da ita x'ayi komai na biki? a'a itama nata bikin xa'ayi rama daya da namu..amma da nasan sai taxo dan Jabo she's my best friend.

Baki ya tab'e kana yace  Bak'o xaiyi halinsa, saboda haka xan tafi, bandir na 'yan dubu ajiyemata guda 5
Haka sukayi sallama, yatafi , sosai taji ya kwanta mata arai dan bata zata haka yake ba.

Waya ta bugawa Jabo labarinsa ta bata, haka dai sukayi hiran su irin na aminan juna masu kula da junan su.

Auta ce

ZAB'IN WA ZANBI? Where stories live. Discover now