ZAB'IN WA ZANBI? 2

737 38 0
                                    


Mami yaufa insha Allah, gidan Aunty saleema xani, dan namata waya kuma Yaya  F yace naje,
Huum, kinganki Hauwa da yawo kamar me, Foisal en da zaice kije shine mai gidan? a'a Mami amma ance babban wa magajin uba, tunda Abee  baya gari aikinga saimu tambayi Ya F koh?.

Hakane,  amma yanxu Hauwa ace ki d'auki qafa daga sokoto har kano daga ke sai driver?, ba hanaki zanyi ba, amma kiyi tunani shi Faisal en basaiya kaiki ba?.

Mami kinsan dai yana yin aikin su, dashi zaikaini amma indai baki yadda ba, wallahi na haqura.

"Rufan asiri yanxu saleema tace nahanaki
Allah ya kaimu goben.

" Amen Mami na, shiyasa nake sonki sosai
Bawani?Allah Mamina tana magana tana kwanciya ajikinta
D'agani kada ki karyani, dama ga qafa na ciwo, d'agani ai kinyi lukuti yanxu
Allah Mami kedena cewa nayi lukuti to na dena.

wacece Hauwa

"Alhaji Mohd Jabo mutum ne nagari" d'an kasuwane amma na qasashen waje da gida Nigeria🇳🇬
Atamfa super Holland, da Shadda Gexna, su yake kawowa, kusan shine na biyu amasu kawo wannan kaya, yanada lokacin iyalensa wataran tare dasu yake zuwa England ko Holland.

Yanada mata d'aya da yara biyu, Faisal da Hauwa, sai 'yar wansa  Saleema wadda suka riqe
Yanxu haka tana aure agarin kano
Iyalan gidan Alhaji Mohd Jabo sunada kyakyawar alaqa da kowa, matarsa tanada kirki sosai
Faisal yayi karatunsa a garin kano, tundaga secondary har jami'a
Yanxu kuma yana aiki a CBN na garin sokoto.

Mahaifinsa shine yasamasa aikin.
Sai Hauwa wadda takasance qarama, shgwab'ab'iya ce ta gaske, amma kuma akwai qoqari da hankali, gata da son jama'a
Kowa natane, ita ko kayimata abin rashin kirki, bazata d'aga ido ta kalle kaba bare ta tanka maka shiru ma magana ce.

Ta taso cikin gata gaba da baya,tana karatu a Iran yanxu haka ta kamalla tadawo gida Nigeria🇳🇬

Tana d'aya daga cikin writers wanda duniyar Online keji dasu, tun tana qarama takeda sha'awar rubutu, gashi Allah yasa tayi kuma ko yanxu tana kan yi.

Tanada qawaye,amma batada kamar Benaxir Omar kamar yadda itama  Benaxir bata da kamar M Jabo.

Kowa yasan qawancensu  basa  b'oyewa juna sirrinsu, wala na dad'i ko na akasin haka.

Alhaji Mohd Jabo, Mutum nai na jama'a kowa yasan shi, danginsa suna alfahari da shi,J abo sunan garin su ne shiyasa ake masa laqabi da Alhaji Mohd Jabo
 
       wannan Kenan.

Tun safe, Hauwa ta tashi, shiri take dan zuwa kano, saiga kira daga qawarta Benaxir  keh Jabo bakida kirki, ko waya?, bayan kinsan banda lafiya? wallahi bansaniba, @ut@ bata fad'a miki ba? bata fad'an ba, OK,ni yau fa baxan hau online ba, typing xanyi,shiyasa nabugomiki kada kijini shiru OK, nima bazan hauba, saboda tafiya zanyi, kin sanni da bacci, nasan dole a mota sainayi.

Allah ya kiyaye,amma dai zakije gidan fans d'inmu?anya"sai yanda hali yayi OK.

Safe journey Aminiya.

Haka sukayi sallama, nan ma ta sakko tayi sallama da Mami driver yaja ta sai hanyar kano

ZAB'IN WA ZANBI? Where stories live. Discover now