ZAB'IN WA ZANBI? 7

394 28 0
                                    


Dayake aranar zasu koma gida, shiyasa yana fita waya ya bugawa Abbu cewa ina zai sameshi?.

Yana airport yace dashi, sallama yayi da abokansa wad'anda ya xiyarta ad'an lokacin
Shigarsa airport keda wuya aka fara announcement, a dai dai yace, shiyasa baitsaya wani b'ata lokacin ba, yayi maxa ya shige.

Sosai Mom tayi musu girki kafin su dawo, tafiyar 2 hours ya kasu kano, driver yana zaune jiransu haka suka d'unguma dan tafiya gida.

A b'angaren Hauwa itama tanata shirin tarban baqo, shiyasa tun yau take rage wasu ayyukan da take na biki, kinsan sha'anin biki, Aunty Saleema, da Aunty Beebalo dasu Bingel duk suna gidan
Sune ma, suke yimata gyaran jiki tareda wata 'yar chadi da Mami ta kitawo, dama gata fara saitaqara wani sirrin kyau.

Shima bai jima da dawowa ba, Mom tasashi fitar dole danyiwa Hauwa siyayya sosai yaji haushin abinda Mom tace, sai kace wata 'yar sarki shifa yagaji da abinda ake masa
Wai mata biyu lokaci d'aya, shi garama Benaxir saboda duk yanda yakeson matarsa ta kasance ta had'a komai, ga kunya da ladabi, kuma indai ita tayi girkin jiya to tabbas ta iya girki.

Sosai kuma yafara tunanin moment en su shida ita jiya, mts ai bani nace inasonta ba, saboda haka baxan sota ba
Amma dai Bena tayi 99% , gatada dimple dan jiya kamar ya tab'a lokacin da take bashi labarin qawarta jabo
Wai Son mai katsayi yi? Kaxo kayi sauri kasan tafiyar asubah zakayi, kuma ga kacaniyar biki, jiya aka kawo IV naso ayi koda dinner ne atare da amaren, amma abin baxai yu yuba.

Ita gidan su Bena  da yayunta xa'a had'a, kuma tunda ba'a d'aura aure ba, baxamu ce tazo ba, kuma ma dai gari ba d'aya ba.

Ga na Hauwa IV sai ka tafi mata dashi, wannan kuma kabata saqone kace injini, tafiyarka jiya afujajan taxo shiyasa banyiwa Benaxir komai ba.

Yaka ganta?"
"Mom wallahi yanda naxaceta bahaka take ba, kunganta so cute, banxaci akwai kyawawa a Bauchi ba, wallahi tayi sosai Abbu ya iya xab'i
Koh! Allah to yabaka wuyan d'auka, ya kuma saka kayi adalci,Ameen yace.

Qarfe 5, batayimasa a kano ba, dayake a mota zashi, shiyasa yatafi da wuri,
Alhamdulillah, qarfe 1 yaje dayake gudu sosai yayi, shiyasa baiyi taking time en da ake d'auka ba
Yana shiga garin, ya tsaya duk da ya tab'a zuwa wajan abokinsa, baisan gari ba ta ina ma zai fara?.

Waya ya bugawa Mom, cewa yazo ina zaiyi? OK katambaya gidan Alhaji Mohd Jabo xa'a kaika kowa ka samu, haka akayi kuwa wata motace ta tsaya kusa dashi d'an matsawa yayi kusa dashi yace
" salamu alaikum "

Amsawa yayi, wani saurayine da waya a hannunsa da key en motar
Dan Allah tambayanake? Allah yasa nasani, gidan Alhaji Mohd Jabo
Kallonsa yayi yace, wakake nema a gidan? kamar bazaice komai ba, saidai yace gurin 'yarsa xani, hannu ya miqamasa yace SMS koh? Kai ya kad'a.

Wnn saurayin yace I'm Faisal M Jabo, Yaya ga Hauwa koh? Eh
Anan suka shiga mota yafara binsa abaya, har katafaren gidan su
D'akinsa ya shigar dashi, yace ka gaji da xaka iya ka fara wanka before akiramaka ita? Sosai yaji dad'in hakan, amma kuma ai gidan sirukaine, kamar Y F yasan meyake tunani, yace ai nan gida ne, kuma kanaso kaje a haka jikinka koda babu wani abu, amma baxakaji dad'in saba.

Haka ya amince, inda yaqqara godewa Allah tafiyar da xasuyi da Abbu ya d'ebi kayansa kuma a motar ya xuba, tunda mantasu yayi aciki driver'n da yakaisu airport kuma ya juyo da motar sai wani ya siya a wani Shop, suna siyar da d'inkakku
Shiga yayi, yana fitowa yasauya kaya, zuwa wata farar shadda mai kyau, saidaga shirya sai ga Ya F, a'a kace da kayanka dama? Eh wllh, to abinci xamu faraci sannan akiramaka ita?.

Yanda yayanmu yace, sosai suka yi hira, Danbun shinkafa suka ci, dama SMS dason abincin gargajiya
Suna gamawa aka kiramasa ita
Sosai suka gaisa, itama yaganta kyakyawa kamar ita tayi kanta, dama gashi tasha gyaran jiki, gata da dimple yace,
Hira sukai, yasaki jikinsa da ita, nanma saiyadace kinsan Ku biyu xan aura koh? Eh tace, yauwa atak'aice yabata tarihin sa, itama tabashi nata
ZAB'IN Ku duk yayi, irin wnn mata haka, Allah yasoni da bance banso ba, waccen chocolate colour, wannan fara, kuma kowacce tayi 99%
Babu makusa ZAB'IN Mom yayi, ZAB'IN Abbu shima yayi.

Sosai yakejin wata nitsuwa na shigarsa, baiyi zaton xai gansu haka ba
Lallai d'an gatane shi, ada yayi tunanin ya musu wulak'anci, amma daga ganin su baxasu d'auka ba, kuma ba irinsu akewa ba
Itama haka tabashi labarin qawarta, aminiyarta, Adda, dariya yai yace, itama abokiyar xaman naki tanada qawa sosai take Sonta, wai Jidda, ke kuma Adda lallai kunaji da juna, gaskiya dan ni nad'auki Adda sister bama qawa b, kice xamu bikin ta?.

Lah, itama bikin ta xa'ayi, amma da babu abinda xaisa banjeba
Ya sunanta ki kace Add ok , da shi harya fara tunanin kodai qawayene to saidayaji sunan
Xan gudu, ga saqon Mom tace abawa 'yarta, kai nagode sosai Allah yaqara girma.

Har ya miqe saiyace bara nabaki Ku gaisa, da Aunty'n ki?
OK, su Jabo harda gyara murya,
Bugu d'aya tayi, ta d'auka, cikin husky voice nata tamasa sallama, amsawa yayi yatambayeta ya take, sosai muryanta tayi masa dad'i
Ungo,
"Hello"
Haka suka amsa lokaci d'aya, d'an shiru sukai,ita Jabo jitayi kamar tasan muryan, itama Bena haka
Sharewa sukai gaiswa sukai kamar dama sunsan juna.

Yaji dad'in jin yadda yaga sun gaisa, haka yayi mata sallama ya tafi, cikin farin cikin samun matayensa cikakku, masu ilimi
Sai wajan dare, Jabo tayiwa Bena waya akan yazo, labarin sa tafara bata, kowa kuma saiya fara cewa saurayinsa yafi na kowa
To kituran pic nasa? bandashi, ni kuma ina dashi Inji Jabo to kituran nagani, naqi, to kada ki turo bye.

Biki ya matso tunda gashi, yau kowacce ta fara kamu daga kan, Benaxir harsu Sofy en, dan guri guda sukayi har Fido.

*'Yan EXCELLENT da NAGARTA, ga MUMBARIN JABO duk sunje saboda ana bikin manyan su
Dama basa wuce tayi, 'Yan EXELLENT da  Mimbarin M Jabo  wawaso tsakanin marubuta da makaranta abin sai dariya.

Itama  Jabo yau take nata,komai dai yatafi cikin tsari
Ango, yau ake dinner a Bauchi na Benaxir  abokansa duk sunje anyi antashi lafiya
Itama Jabo yaje mata, Dan tare da Mom akaje, anyi itama lafiya antashi lafiya
Yaune kuma d'aurin Aure Benaxir Omar ita aka fara d'aurawa tare da mijinta Sameer Mohd SAMEER (SMS) k'arfe 9:30 na safe, akan sadaki naira dubu hamsin.

Daga nan kuma aka d'unguma zuwa airport danxuwa sokoto, sunje lafiya
Nanma aka d'aura Auren Hauwa Mohd Jabo tare da mijinta Sameer Mohd Sameer (SMS) akan sadaki naira dubu Hamsin, anan akayi waleema daga nan aka dawo gida kano ta dabo tumbin giwa
A yaune kuma xa'a kai amare gidan su.

Auta ce

ZAB'IN WA ZANBI? Where stories live. Discover now