ZAB'IN WA ZANBI? 8

376 28 0
                                    


Amarya Jabo, anyi kyau sosai tana cikin tsakiyar k'awayenta, irinsu Zainab khaleefa, Nahal, Lubie, Jameela M Ali, inna habeeba, Ummu marwa, Maman Faty(fatu abirni), kai da yawan su dai anata shafta, ga kuma k'awayenta Marubuta, wad'anda suke garin na sokoto da wad'anda basa garin, Anker itace gaba, suna ta yimata shak'iyanci yau su Jabo xa'ayi kwanan Kano ba sokoto ba, kuma gidan miji ba gidan Aunty Saleema ba, ita dai jinsu kawai take
Wayarta ta janyo, Adda Benaxir, ta kitawo.

"Hello Adda"
A'a Amarya yanxu fa nake shirin kiranki nace ko pics d'in baxa'a turo mana ba?.

Haba dai wallahi gajiya ta biki bata barni na hau online jiya da yau ba, gakuma su Maryam k'awata, duk sun xaman.

Amma bara yanxu na turo miki,  ya ango?
Yana lafiya, kinsan wai yau xa'a kaini shiri ma ake, ita amaryar tawa itama yau xa'a kata
Benaxir, ai kuwa kiyi sauri afara kaiki, duk tsiya kece uwar gida, nima abinda yanxu Aunty Beebalo dasu Lubie suke cewa kenan.

Huum, nifa wallahi kinga hankali duk ta tashi, zama da Kishiya sai dole, kuma fa ni mijin bawai muna son juna ba, daga ni harshi.

Adda sai hak'uri an rigada an d'aura, kuma kema ai bazama zakiyi ba, kyaun da Allah yabaki ai kada ki bari ya tashi a banza, nasan duk tsiya indai ba India ya auro ba, to kowacce nafila CE, kinada kyau, aike zaki janyo hankakin sa, kinga bari wannan maganar sai dai mun shiga muga irin kishiyoyin namu, koba haka ba?.

Hakane kam, sallama sukai, alokacin ita Jabo ma angama had'amata ruwan wanka, dan qarfe 2 za'a tafi, saboda nisan dake tsakaninsu sokoto da kano, ita kuma sai 3 xa'a kaita, tunda jirgi zasu ni.

A can ma, Benaxir itada nata k'awayen irin su, Meena d'an Musa, Ummu samha, YBK, Meemi, da kuma wad'anda suke Bauchi, Rash Kardam, Meimi bee, da sauran su suma atare suke anata shagali, 'yan uwa kowa zuzuta kyan da tayi yake, abinka da black beauty anhad'a kuma da gyara ga gashi nan, shima sai kyalli yake, ita hartayi wanka, sallama ma yakewa Iyayenta, San nan akaita gidan kakaninta daga nan xa'a kaita, dan jirgin baifi 30 minutes ya tashi ba.

Benaxir, aka fara kaiwa, gidan Mom aka kaita, sosai , akayi musu tarba ta girma tare da 'yan uwan Abbu da Mom d'in.

Anyiwa Amarya fad'a na tsakani da Allah, itama Mom ta mata, amatsayinta na uwa da tace ta d'auketa ba suruka ba, tunda basu da kkowa a kano, koda da akwai amma basuda wadda ta fita.

Sunji dad'i dangin Benaxir da karammawar da akayi musu
Haka suka d'auketa sai gidan ta, dake sharad'a NNDC qrts.

Lokacin da suka fito lokacin ne aka kawo Hauwa tareda rakiyar danginta itama.

Nan ma sun nuna musu halin girma, da karamci, fad'a dai itama akayi mata, Mom tace dama ni Hauwa 'ya tace ba suruka ba, saboda haka kuzauna lafiya, babu tashin hankali, ko kace nace, dan ita uwargidan kowa yayi shaidarta wajan hak'uri da kawaici, to kema saiki kasance haka.

Gidan su, gida ne, babban gaske, ya qawatu da abubuwan more rayuwa dan tundaga gate en gidan, xaka tantance, frems frems na Allahu duka zagaye yake acikin gidan.

Part ukune, na Benaxir yana daga hannun dama, saina Ogan a tsakiya, saikuma na Hauwa a hagu, kowacce tanada k'ofa a sama da k'asa na gidanta, wanda zata shiga part d'in mai gidan.

Amarya an kaita, kuma d'akinta ko ban fad'a ba, kunsan dai ya had'u, k'anwar Manager da Director na NNPC kuma 'ya ga Eng Omar mai kamfanin Camery Motors, na baku assignment na hango tsarin d'akin da yanda aka qawata shi.

4 bedroom ne, sai 3 toilet ga kitchen, da dining area har 2, parlour kansa biyu ne, kuma ko wanne dank'am yake da kaya.

Dayake aranar xasu juya masu kawota har sun fara haramar tafiya, jirgi ne zai d'ebesu.

Lokacin da suke fitowa, lokacin ne kuma aka kawo Hauwa, tsayawa sukai suka gaisa, gaisuwa da girma, da nuna daraja wa d'an Adam.

Kai lokacin danaje part d'in Benaxir harna yanke hukuncin cewa 100% nayi, amma yanzu danaje gidan Hauwa gaba d'aya noting kaina sai yake neman kwance wa, saboda banyi tsamanin zan ganshi haka ba

Babu ce kawai babu, komai akwai, kuma babu wadda baxakaso ace d'akinta shine na kaba.

Komai nata daga k'asar England aka siyo, itad'in babanta babban dila ne na Atamfa super, da Shadda gaxena kuma d'an siyasane kenan dai babu koma baya, Ya F wanta shine Managing Director na EFCC kunga wannan had'i yayi

Itama aranar suka juya, kowacce aka barta daga ita sai halinta
Jin shirun yayi yawa, yasa Hauwa janyo wayar ta, daidai lokacin itama Bena ta janyo tata, chat suka fara, jin chat d'in bazaiyi dad'i ba, yasaka Benaxir ta bugomata Waya
"Hello"
Yana ganki online inji Hauwa, eh angon bai shigo ba, inaji yana part d'in Amarya kinsan nice uwar gida.
Him nima kinga bai shigo ba, ko kuma yana b'arin uwar gida? dan nice Amarya, anriga kawo ta, a kaina.

Haba? aini lokacin da muka gama waya kikace nayi sauri, wallahi ban b'ata lokaciba dama nayi wanka, kaya kawai nasaka, aka tawo, Benaxir ke wannan maganar.

Lokacin da muka tawo, lokacin muma aka kamana amaren, Sofy da Fido, suma bakiga d'akunan suba, ana jere mu kaje, kinsan 'yan katsina ne, suma da wuri aka kasu.

Ango dai yana part d'in sa bai shiga ko ina ba, saboda baisan wace uwar gida ba, kuma baisan wace Amarya ba, Mom ya yanke shawarar tambaya.

Haka akayi kuwa, ta fad'a masa, wanka yayi, ya d'auki ledan da ya shigo da ita, k'ofar da zata sa dashi da d'akin Hauwa yayi, ganinta yayi a parlour.

Bena ya shigo bye, maza tayi mata sallama, gaisawa sukai, anan suka d'an tab'a hira, yabata ledar d'aya shigo da ita, yace Hauwa, zan shiga wajan uwar gida  da fatan ba wata matsala koh? Kai ta kad'a, OK Allah yabamu alkairi, fuskarta ya Shafa,saboda tunda ya shigo yaga tamsa kyau  juyawa yai yaqara bud'e k'ofar ya fita..

Wai, wani iri Hauwa taji, lokacin d'aya shafa fuskarta, laushi k'amshi hannun sa haka tace..tana murmushi

Hello " Bena yanxu ya fita, Haba? Wllh gayen fa ya had'u ta ko ina Bena ce ta bugomata, suny sallama, saitake bata labarin..
Jabo, bye nima naji motsi maybe shine, ok bye a kula dai yau xa'ayi su kuwa akan wata...mts Jabo kenan sai kinji dai.

Auta ce

ZAB'IN WA ZANBI? Where stories live. Discover now