CHAPTER 29 ( MILESTONE)

46 3 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 29 (Milestone).

Wannan shafin gabaki d'aya sadaukarwa ne ga sojojin k'asata da aka kashe ranar jumaa a dajin shiroro dake jihar Niger, particulary Late Capt. Muhammad Auwal Adam, hak'ik'a Uncle Auwal jarumi ne kuma jan gwarzo mai kishin alumma da kuma kyakkyawan muamala da kowa. Hakaza rashin irinsu a alumma babbar asara ce wacce muka yi da ba zamu tab'a samun mak'wafinshi ba balle ya cike gurbi Hakazalika ba zamu tab'a mantawa da shi ba a rayuwarmu gabad'aya sai dai adduar mu da shi ma in shaa Allahu ba zamu gurin aikasu gareshi ba matuk'ar numfashi.

Allah ka ji k'an uncle Auwal ka gafarta masa, ka sa kyawawan halayenshi su zame masa abokan tafiya, kisan gillar da aka masa ta zama kaffara a gareshi ka kyautata makwancinsa da ta sauran alummar musulmi. Ka raya abinda ya bari ka shirya masa su ka basu dangana a bisa rashinshi ka sa su zame masa ababen alfahari a gobe k'iyama, mu ma ka sa idan tamu tazo mu yi kyakyawan k'arshe🥺.

If you come across this page please include him in your duas, jazakumullahu khairan as you do so🙏🏻

Ba ta tanka mata ba sai mai da kanta da tayi kan Zulfaa tana mata sharrin saura ita itama tana ramawa da saura mu dai, a nan gidan ta yini ba ta iya matsawa ko nan da can tana nan manne da yaron mai matuk'ar kama da ElSadeeq kuma kamar almara ya d'ebo haskenta don ko yaron fari ne tas irin nata. Murmushi tayi bayan idar da sallahr la'asar d'inta ta dubi Suleim taka cewa " ni dai nayi booking Afdhal wa 'yata wallahi". 



"Waye Afdhal kuma?" In ji Zulfaa dake zaune kan dadduma don tunda ta yi sallah ta kasa tashi tana daga zaune sai nishi take yi.

"Ga shi nan babyna ai sunanshi Afdhal".

"Auuu ashe ma har an sa masa suna kenan?"

"Koma menene sunanshi ni dai Afdhal zan na kiranshi, kuma sirikana ne".

"Mai haihuwa daban mai sa suna daban, ina k'aunar shahararki".

"Ke ma ai ni zan sa miki suna yarinya, sai dai in baki haihu ba. In namiji ne he'll be Ayan mace kuma Ayanah".

"Ke zaki ga Ayyana ba ni ba, ai gwara ma namijin Ayan amma ni ban son wata Ayanah a na zaman lafiya".

Dariya Suleim da ta fito wanka tayi tana cewa "ke kuma naki me zaa saka mata ".

"Wa ma ya sani?" Ta k'arashe da gaskiyarta har cikin ranta, Zulfaa tace " Ayanahr ce zaki haifa ba komai ba''.

"Toh Allah ya rayata " ta furta tana shafa kumatun jaririn sai kuma tace "Allah yaron nan da ni yake kama, ji shi fa mai kyau sosai Allah ya taimake shi bai d'ebo wasu ba".

"Ke dai kika sani 'yar rainin sense ni ba biye miki zan yi ba". Dariya suka kwashe da shi don kowa ya san me take nufi da maganarta Farhan take tsokana, tunda kuma ba ya nan toh matarshi ce zata shigan masa ita kuma haki take fama da shi.


Sai bayan ishai Burhaan ya dawo gidan shi da su Sadeeq da Farhaan, a parlor suka zauna Farhaan ne ya shiga ciki ya nemi iso wa Sadeeq akan zai gana da Suleim. Dukansu fitowa suka yi Farhaan d'in rik'e da hannun Zulfaa don tafiyar wahala take ba ta ainun ita Nadeefah ta d'auko yaron ta kawo ma Islaam, mik'a masa yaron tayi tana zama a kujerar dake opposite ta shi.


NISFU DEENIY.......!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin