CHAPTER 11 ( SHE'S BACK II)

22 2 3
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 11 ( She's back 2)

This chapter is dedicated to my sweethearts Uomm Abdallah and Aunty Maryam (Maaroyal) thanks for the love Allah bar zumuci😍❤

Cikin gida Hajjah ta shiga da ita tana mai jin kamar itama kukan zata yi, amma ta samu sukuni yanzu da ta ganta cikin k'oshin lafiya. Suna shiga Abba ya isa ga Musab dake k'ok'arin shiga motar shi don ya wuce gida, gefenshi Farhan ne da Burhaan da ya d'aure fuska tamau ko sallamar da yayi masa bai amsa ba Farhan ne ya amsa har da masa godiya.

Kallonsu yayi da kyau yace " mun gode fa bawan Allah, Allah ya saka da alkhairi aina ka sameta? " murmushi yayi yana cewa " Babu komai ai Alhaji, a nan gaban sabon wuse Allah dai ya sake tsarewa amma ta auna arziki" cewa yayi " Ameen dai, we really appreciate your efforts and da buk'atar mu ganka da kyau I can see yanzu kana sauri ga dare kuma".

Cewa yayi " haba dai, ai yiwa kaine ". Gyad'a kai yayi cikeda yabawa da d'abiun shi yace " tabbas yiwa kai ne amma dai zamu ganka we need to appreciate you more, let me have your digits here". Ya k'arashe yana mik'a mai wayarsa, amsa yayi ya rubuta masa number yace " name?" ya buk'ata.

A hankali yace " Arc. Musab Siraj Bawa". Murmushi yayi yana cewa " Masha Allah, Allah yayi maka albarka mun fa gode". Shima Farhan hannu ya sake mik'a masa yana cewa " mun gode Arc. Allah ya tsare hanya". Ameen yace ya shiga cikin motarshi, sai da ya bar gidan kafin Abba ya kalli Islaam k'wafa yayi bai ce masa uffan ba ya nufi cikin gidan Farhan ma goya masa baya yayi suka k'yaleshi tsaye kamar tsinkakken silifas, kamar ya wuce gida sai ya tuna rikicin Abba hakan yasa ya biyo bayansu yana b'ata fuska.

A zaune ya taddasu sun zagaye Hajjah dake rungume da Lelen, bai zauna ba ya dai coge a jikin garu jin Abba na cewa. " A samu tayi wanka, ta sha ko tea ne ta kwanta ta huta kar a matsa mata da wata magana har sai ta dawo jikinta". Toh Suliem ta furta tana k'ok'arin kamata da niyyar kaita ciki don cika umarnin Abba, sai cewa tayi " Abba na san yanzu ba lokacin da ya kamata ayi magana bane amma ina son in shaida maka da cewa Ya Islaam baida laifi ko kad'an, duk wani k'ok'ari yayi don yaga mun dawo tare amma ni nak'i baida zab'i sai na k'yale ni so in akwai wanda za ai wa hunkuci toh ni ce ba shi ba".

Kallonta yayi cikeda jin haushin kalaman da ta fad'i, yayinda takaicinta ya kamashi ainun. Kamar ya shak'eta a wurin yake ji, he hates playing victim that's why yakeda bak'in tambari. Ko yana da gaskiya bai tsayawa explaining kanshi balle yayi seeking for justice, in aka ce yayi abu zama yake akan haka ya shanye duk wani fad'a da tsangwama da zai biyo baya.

One thing about him is bai k'arya and ya tsane mai yi, wannan maganar da tayi ganinshi yayi a babbar laifi and it makes him hates her more. Abba ne yace " ban tambayeki waye mai laifi ko mara laifi ba, cewa nayi kije kiyi wanka ki kwanta".

Kanta a k'asa tace " kayi hak'uri...." Ya katseta da wata tsawar da ta tsoratata yana cewa " kika sake wata magana a nan sai na sab'a miki Nadeefah!!" ai da sauri suka wuce ciki ita da Suliem kamar zasu kifa, kallon mutanen parlorn yayi ya ci gaba da cewa " zaku iya tafiya ku kwanta". Ya k'arashe da mik'ewa tsaye, Umma ma mik'ewa tayi haka kusan kowa dake parlorn.

Gaban Hajjah ya k'arasa yana cewa " zamu shige mu kwanta kema ki je ki kwanta Allah ya k'ara kiyayewa". Cewa tayi " Ameen ya rabbi Abdoulaye Allah yayi maku albarka ". Ameen yace yana nufar k'ofa bai ko amsa sai da safen da ake yi masa, Farhan ne ya ajiye wayarta a kan handbag d'inta dake gefen Hajjah shima ya nufi k'ofa haka sauran kowa ya nufi gida bayan sun wa Hajjah sallama.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now