CHAPTER 17 ( LIVING WITH HIM)

27 1 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 17 ( Living with him).

Zama tayi suna hirar tana cin abincinta sai magrib suka wuce gidajensu lokacin ne ta samu kan Hajjahr tata. Ko da sukayi sallah zama sukayi suna hirar yaushe gamo da kuma sake mata nasiha mai tsayi akan Burhaan. Ita dai jinta take yi amma ta ajiye duk wata nasiha sai ran da Islaam d'in zai waiwayeta a matsayin mata, musamman maganar da tayi na cusa shak'uwa a tsakaninsu ta hanyar kusanta kan su ga juna.

Ba shi yazo gidan ba sai after 9, cikin parlorn ya shigo yau har da hira da Hajjah. Cikin dabara ta sake ba shi amanar lelenta, kamar kullum jin ta kawai yayi amma fuskar nan ta shi dake kullum a d'aure ta hana a gane ya amshi maganar ko akasin haka. Fita yayi zuwa waje, Hajjah ta kalleta tana cewa " ki tashi ku tafi ki cigaba da hak'uri ban da wasa kuma da addua" Mik'ewa tayi tana cewa "in shaa Allah Hajjah, ina keys d'ina suke kafin in manta ".

Murmushi tayi ta janyo drawern dake jikin kujerarta da ba kowa ya san da ita ba, sai 'yan gidan cikakku irinsu Lele da Yana. A nan ta kan yi k'ananun ajiyarta wanda ba sai ta tashi ba, keys ta kwaso tana ajiye mata a gaba alamun ta d'auki na ta. Tura baki tayi tana ajiye bag d'in ta da ledar turaren Hajjahr da ta d'iba, murmushi tayi tana cewa " kin gama k'umu-k'umun da ledar?".

Cewa tayi "ai ba d'auka nayi ba, kin san ai na d'iba shi ma hana ni akayi balle ma ace". Tace " ai ban yi magana ba ya da kama kai haka ". Murgud'a baki tayi ta cire keys d'in ta ta ajiye mata na ta, a jakarta ta zuba kayanta sai kuma ta sunkuya ta sumbace ta a kunci tace " kamar kar in tafi Hajjah".

Cewa tayi " kuma tafiyar zaki yin ba". Jakar ta d'auka ta rik'o hannun Hajjahr, mik'ewa tayi suka nufi k'ofar fita bayan ta k'wala wa Yana kira tana cewa ta wuce. Har bakin mota ta rakata, lokacin kam Islaam ya cika ya batse. Ba ta ma kula da kumburar da yayi ba, sai da ta sake musu addua kafin ta saki hannayenta shiga motar tayi ya tada suka nufi hanyar barin gidan.

Shiru ne ya biyo bayan tafiyar ta su zuwa gida, fuskar nan babu yabo ba fallasa sai ita ce dake ta yin streak ta hanyar snapping hanyar da suke bi. Bai ma kalleta ba balle ya tanka duk da ko yana lure da abinda take yin, mai da hankalinshi yayi kan titi.

A usual joint d'in shi ya tsaya siyan nama kallon gefenshi yayi yana sakin tsaki, in da shi d'aya ne da yana ciki zasu zo ya sa order. Yanzu kam bai shirya kallon k'urilla daga maza ba, haka d'azu ya kwashi takaicin yanda mazaje su ka din ga kallonta a gaban motarshi. Da yake ba tinted ba ce ga shi tayi worsening lamarin ta hanyar murmushin da ta dinga saki da sunar tana waya, shi yasa yanzu ya canjo motar ya d'auko jacquard d'in mai bak'ak'en glass.

Fita yayi zuwa wajen masu naman da suna ganinshi suka fara washe baki, gaisawa sukayi "Alhaji yau da kanka". In ji mai namar yana washe baki, cewa yayi " wallahi kam Lawandi, a saka min yanda aka saba amma guda biyu akwai mai d'umi dai ko?"

"Toh Toh Alhaji, bari a d'umama" ya furta yana iza wuta, neman wuri yayi ya zauna don da ya koma su zauna da Lele gwara ya zauna a wurin komai sanyi kuwa. Shi bai ma san yanda akayi ya siya da ita d'in ba, yana zaune yana ta lissafi har aka had'a mai naman. Amsa yayi ya basu card d'in shi suka cire kud'in ta POS kafin yayi musu sallama, san da ya shigo motar ta gaji da zaman kad'aici sai dai ko a fuska ba ta nuna ba ita ma addua take yi akan ya dawo da wuri su koma gida dan bacci take ji.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now