CHAPTER FIVE (MEETING.. ).

21 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... (A Yerwa family love triangle )

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER FIVE (MEETING.. ).

Da murmushi kyakkyawar dattijuwar ta tarbe ta rungume ta tsam tayi a k'irjinta cike da k'auna, kana ganinta kaga balarabiya pure blood ta d'an manyanta amma hutu da kyan jiki ya b'oye tsufan. In ka ganta zaka rantse Yayar su Nadeefah ce, ga tsananin kyau nan na gano inda suka d'auko kyau duk da dai Lelen ta so zarta ta ma a kyan ko dan sun d'auko features na Abbu kad'an ne?.

"Ummu who told this spoilt girl cewa mun zo?", aka fad'a daga bayan su. A tare suka waigo wani namiji ne ya na matuk'ar kama da Sadeeq Nadeefah ta na mai tale baki a shagwab'e tace " ba ni bane spoilt ". Ware ido yayi yace " sai wa toh?".

Juya idonta tayi tace " wanda ya tsargu", ai ko ya taho a tunzure hakan ya sa ta daka tsalle tana mai sanya ihu kamar an yankata. Da sauri d'ayan da yake fitowa daga kitchen hannun shi d'auke da plate yace " kar ka tab'ata Malam, daga zuwanta zaka ci zalinta ", hararar shi yayi a k'ufule yace " toh ina ruwan ka?, Ummu ki gayawa Ɗalhat ba ruwan shi dani". Ummu ce tace " ya isa haka tohm, ke kuma habibti ba na hanaki yi masa rashin kunya ba?".

Kumbura baki tayi tana harararshi tace " Ummulkhair shine fa yake ce min spoilt and i'm not " ta k'are da murgud'a baki, cewa tayi " thats not what i asked you , now say sorry" a hankali tace " Im sorry brother Ɗayyib ".

Washe baki yayi yana cewa " never mind Lele, i've missed you ". Ya k'are yana janyota, k'in zuwa tayi ta ruga ga Ɗalhat tace " ni wurin Yaya na zan je ". Ai ko da sauri ya biyo su, duk turjewar ta sai da ta saki nan suka sata a tsakiya. Ta tsokani wannan wancan ya tsokaneta, ganin bata ita sukeyi ba ya sa Ummu kwasan k'afarta ta koma kitchen inda take girkin dare.

Ɗayyib da Ɗalhat twins ne daga su sai Lele, Ɗayyib yana da matuk'ar tsokana ga son girma while Ɗalhat yake da sanyi ga shi bai son kwarafniya ko kad'an. Ɗayyib da Lele suna yawan yin fad'an sako musamman in an dad'e ba a had'u ba, da yawa Ɗalhat ke shigan mata fad'an in bata nan kuma sai fad'an sakon ya koma kan shi though bai wani cika biye masa ba. Nevertheless, suna matuk'ar so da k'aunar Lele ko kad'an basu son su ganta a damuwa ko yaya ne akwai shak'uwa da fahimtar juna mai girma a tsakaninsu ba k'arami ba.

Suna wurin har aka kira Magrib, tashi sukayi su suka nufi masjid ita kuma ta nufi room d'inta dake upstairs wanka tayi ta bud'e closet d'in ta. Tsirarun kaya ne a ciki tab'e baki tayi dole ma ta lallashi ko Ɗayyib ne suje ta d'ebo kayanta, wata free gown ta nemo da hijab jin ana shirin tada sallah a masallaci.

Tana kan dadduma aka bud'e d'akin Ummu ce sanye da hijab ta shigo, cewa tayi " in kin idar ki sauka akwai sak'on Hajjah a dining ku kai mata ke da ko Ɗayyib, ku gaisheta kafin gobe mu shiga". Gyad'a kai tayi ba tare da ta tanka ba ta cigaba da abunda takeyi, sai da ta kai ak'alla 15mins kafin ta idar da hijab d'in ta fito tana saukowa Ɗalhat na shigowa. Murmushi tayi tace " yawwa bro, Ummu tace mukaiwa Hajjah ".

Cewa yayi " ki dai jira Ɗayyib ya shigo ni Abbu zan d'auko a gidan Baba Tijjani", ok ta furta ta koma ta zauna a kan kujera. Bata jima da zama ba Ɗayyib d'in ya shigo yana waya, cikeda tsokana ta d'auko buffet basket d'in da Ummu ta jera kyawawan warmers a ciki ta dire a gaban shi. Kallon basket d'in yayi cikin son k'arin bayani cewa tayi " Hajjah za'a kai wa inji Ummu ", tab'e baki yayi ya cigaba da wayar da yakeyi.

NISFU DEENIY.......!Место, где живут истории. Откройте их для себя