CHAPTER 19 ( SICK)

33 1 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 19 ( Sick...)

Tsawa ya daka wa Safwaan dake k'ok'arin kiran sunanta bakinshi a bud'e, rufe bakin yayi ruf jin yana cewa " kar ka sake kayi wata magana a nan, koma motarka ka wuce gida ".

"And you me kika fito yi a nan? Who called you?" Ya juya kan ta kamar wani namijin zaki, duk gajiyar da ya kwaso ma nemanta yayi ya rasa saboda tsabar tsiyar da take cin shi. Da mabanbantan yanayi suka bi shi da idanu, shi Safwaan bai wuce na yanda ya ga yana hak'ilo gira na hayak'i ido na ci da wuta akan abinda bai raba d'ayan biyu kishi ne. Toh abin tambayar a nan shi ne yaushe har ya fara son ta har haka ne da yake mugun kishinta.

Ita kuwa rauni ne ya lullub'eta ganin yadda yake shirin tijarata a gaban k'aninshi, wai me yasa Yaa Islaam yake son nuna wa duniya kalar tsanar da yake mata ne? Me tayi masa da zafi har haka ne?......

Katse musu tunaninsu yayi ta hanyar sakin wata tsawar yana mai cewa " wai ba daku nake magana ba ne kuka tsaya kallon-kallo? You!! Leave this house right now!! ". Tura baki yayi yana cewa " haba Yaa korata fa kake daga gidanka?".

"Tambayata ma ka tsaya yi kenan?" Ya tambaya a hasale, cewa yayi " well zan tafi, Allah ya baka hak'uri sak'o zan amsa yanzu zan wuce ". Kallon Lele da ta juya baya da niyyar komawa ciki yayi yana k'wafa da sakin ajiyar zuciya yace " you wait in the car yanzu zan kawo maka sak'on, fito min da kayana ".

Tunzura baki yayi deep down yana had'iye muguwar dariyar da take taso masa na kishin da ya ga yana yi akan Nadeefah bayan darun da ya gama yi akan aurenta, kayan ya fito masa da su ya ko ja akwatinshi zuwa ciki. A parlor ya ajiye jakar yana kallonta tsaye a dining tana zare idanu, a zafafe ya isa gabanta cikin muguwar masifar dake cin shi yace " ke baki jin magana ko? Me kika fita yi a wajen?".

"I'm sorry....'' Ya katseta da cewa " you can save that for later, just answer me!! What the fuck were you doing outside?!". Cikin b'arin murya da na jiki tace " i'm just there to welcome you".

"Tun da nace miki ina buk'ata ne right?, haven't i warned you to stay off me?" Ya k'arashe yana tsaye a gabanta jikinshi har yana tsuma kamar zai d'auketa da mari, rasa abin cewa tayi and that frustrate him even more. God so kind sai Safwaan ya saki doguwar honk alamun jira.

Tsaki ya saki yana cewa " you better be careful,,,,,now ki fito da abinda zaki ba shi ya tafi ". Da sauri ko ta shige kitchen, buffet d'in da ta had'a abinci ta fito da shi guda biyu ta ajiye. D'auka yayi ba tareda ya tanka ba, ajiyar zuciya ta sauke tana bin bayanshi da kallo.

Har mota ya kai masa ya juya ciki yana cewa ya gaida su Umma, da dariyar da ya danne fitowarshi ya raka shi kana ya ja motarshi a ran shi yana ayyana yau Umma za ta sha labari. Sanda ya shigo ba ta parlorn bai bi ta kan ta ba ya ciro key a gefen trollynsa yana mai bud'e part d'in na shi.

Da sallama ya shiga ciki bayan ya kunna hasken parlorn, d'an ajiyar zuciya ya sauke ganin parlorn ba datti don kafin ya tafi sai da yayi gyaran shi tsaf sai dai k'urar da ya bayyana ba laifi don ma wai ko ina a rufe yake har ma furnitures d'in dake lullub'e da ledoji. Bai ajiye jakar a nan ba ya nufi bedroom, shi ma dai yayi k'ura in ka d'auke gadon da  ya rufe da keda. Duk da ya gaji amma haka ya ajiye kayanshi cikin closet sannan ya fara k'ok'arin gyaran bedroom d'in don yana son ko wurin rab'a kataren shi ne, tas ya share da kayan sharan dake toilet d'in shi yayi mopping har da shimfid'a bedsheets masu taushi farare da duvet.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now