CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)

Start from the beginning
                                    

A k'asan mak'oshi ta furta barka da safiya jin wata tashar da ya kama bayan ya zame mata d'ankwalin da ta b'ata lokaci wurin d'aurashi, bai ko amsa gaisuwar da tayi masa ba sai ma maidata kan sofa da yayi yana cigaba da abunda ya fara. Wankan dai sai sake shi sukayi ita da shi wanda da so yayi su yi a tare ta k'i don zai b'aro jirginta ne farar d'aya, bai wani matsa mata ba don bai son takura ya zame ya je yayi wankanshi.

Ta san d'ad'ewarshi a wanka sai kawai ta tattara kayan da suka yasar a k'asan, da yake ta gyara d'akin tun safe lokacin yana gym kana ta wuce can nata room d'in a gaggauce ta sake wanka ta shirya cikin  black Lebanese abaya kawai. Hijab d'in da ta so sakawa saboda kayan jikinta sai fasawa tayi tunda an canja shiri dole, sanda ta fito parlorn har ya fito sanye da regular shigarshi ta kullum suit da plain trouser bak'ak'e while shirt d'in yake fari mai stripes bak'ake na burbery.


Dining kawai suka nufa ba tareda yace mata ko uffan ba,and a haka kuma sukayi breakfast d'in ba wanda yayi wa d'ayansu magana sai da suka kammala. Mik'ewa yayi yana kallonta a hankali ya furta "ni zan wuce". A dawo lafiya ta yi masa da adduoin tsari sai da ya sunkuyo ya sake kissing d'in ta kafin ya wuce, da idanu ta rakashi tana mai k'ara jin girma da k'imar son shi na dad'uwa a rai da zuciyarta.


Kusan 30 mins bayan fitarshi ita ma ta fito, office ta wuce yau kam ba ta yi wani aiki ba face gyaran jikinta da tayi. Lips therapy da face therapy aka mata, sannan aka d'umama mata jiki, sai halawa da pedicure and manicure. Lalle aka mata na zane ja zallah na red chili ba tayi kitso sai sake setting da aka mata, sosai jikinta yayi kyau ya sake murjewa haka lips d'in ta ya sake yin pink sosai looking so luscious. Sannan ta lek'a Suliem sabbin tips na sake kama miji a hannu ta bata, a can ta k'arasa zamanta kafin ta fito zuwa gida.

Ko da ta dawo girki kawai tayi ta kwanta tana mai jiran dawowarshi, yau da wuri ya dawo sai dai bai shiga gidan ba sai bayan ishai don ya tsaya can wurinsu Farhaan da ElSadeeq da ya dawo yau. Da kuma ya shigo bai ko nemi in da take ba sai da ya fito neman abinci, nan ya tarda ta kwance tana kallo a African Magic. Barka da dawowa tayi masa tana binshi table ganin can ya nufa, serving d'in shi tayi iya cikinshi ita ma ta sa na ta. Suna gama ci ya goge baki ya tashi daga kan dining d'in, sai da safe yayi mata yayi wucewarshi shiyyarsa.

Da idanu ta bishi tana sauke ajiyar zuciya don duk da dai ta amince in ya sake buk'ata ba zata hanashi ba, amma kuma akwai tsoro fal ran ta ga kuma was-wasi don ma Suliem tana bata assurance mai k'arfi akan hakan. Shi ko yayi hakan ne gudun sake sa kan shi a wata matsalar, don ya san yadda daren yake zama masa so unbearable in ya tab'ata. Shi yasa yau ya rufa ma kanshi asiri bai takaleta ko neman tayin kwana ba tunda for sure ba iya k'yaleta zai yi tana gefenshi bai tab'a ta ban ba.


Washe gari ma haka suka bar gidan bai ko rik'e hannayenta ba, duk da rai da zuciyarshi suna ta azazzalarshi kan hakan don daren nan har nadama sai da yayi. Hakan ya sa ya lallab'a ya bar gidan, zuwa yanzu kam ta fara zargin da akwai matsala don tun daga ranar ta ya fara kai hannu gareta bai tab'a barinta haka nan ba tareda ya rab'i jikinta ba. A take tayi tunanin ko fushi yake yi ko kuma wata matsalar ce, a take ta yanke hukuncin yi wa tufkar hanci kafin yayi rimi ya gagareta.

Yau ma kamar jiya bai dawo da wuri ba, ya shigo a na sallahr isha. Kamar yadda ya saba in dai ya dawo ana sallah sai ya gabatar da ita kafin ya shiga gida, hakan ya sa ya gabatar kawai sa'annan ya k'arasa. Yau ko tsayawa wurinsu Farhaan bai yi ba don da damuwarshi ya dawo fal zuciya, ko da ya shigo gidan yana parking briefcase d'in shi ya d'auka da ledar da ya jido tsirenshi a ciki ya shiga ta main parlor. Ba ta ciki sai mayataccen k'amshin turaren d'aki da na jikinta da ya jima da kama d'akin yake shigar masa hanci.

Har yayi niyyar wucewa kawai sai wata zuciyar ta raya masa ya lek'a ta kawai, wannan ne karo na biyu da ya shiga cikin d'akin nata. Kamar wancan karon yau ma sai da ya tsaya ya sake k'arewa parlorn kallon tsaf, sai kuma ya nufi corridorn da rooms d'in ta suke.


NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now