Fita tayi zuwa room d'in ta tana mai cigaba da shafa wuyanta da sai yanzu ta sake jin rik'ewar da yayi, wanka ta yi a gurguje ta d'an gasa wuyan a cikin toilet d'in ta lakaci neurogesic ta shafeshi da kyau kana ta fito. Doguwar riga ta zura tana tada sallah ko da ta idar ta d'an d'auki lokaci mai tsayi tana lazumi, sannan ta ajiye hijabin. D'akin ta fara gyarawa ta kimtsa shi thanks to her vacuum cleaner da mop d'in ta, sanna ta fito zuwa parlor shi ma gyarashi tayi ta shiga kitchen.


Ruwan zafi ta fara sakawa ta had'a masa tea da yaji kayan k'amshi, ta lura yana son milk da yawa hakan ya sa ta zuba masa a wasu containers masu kyau da sugar ta nufi d'akin na shi. A parlor ta sameshi kwance dafe da kanshi, jiri yake gani ga kuma yunwa. Sannu tayi masa ta gaisheshi a d'an dake ya amsa, bata ko kula ba ta ajiye masa trayn da ta sako ruwan zafin akai tana mai tambayarshi " what do you want for breakfast?".

Kamar ba zai amsa ba don har sai da ya had'a tean shi dai dai yanda yake so, kafin yace " anything". Gyad'a kai tayi kawai ta tashi komawa kitchen d'in tayi tana lissafin abinda za ta had'a masa, tuno jawabin Dr tayi "banda abu soyayye for now". Sai kawai ta d'ebo irish ta fere ta yayyanka, porridge ta had'a mai wanda ta ji ganye da hanta a ciki.


Bai wani d'auketa time ba ta kammala a cikin bowl ta sanya masa, ta d'aura akan tray ta nufi d'akin nashi. Har yanzu yana a kwancen don sosai bai jin dad'in jikinshi dauriya kawai yake yi, ajiye masa tayi ta nufi cikin d'akinshi. Gyarawa tayi da kyau har da canja masa bedsheet ta wanke masa toilet da kyau, fita tayi ta d'auko burnernta guda d'aya da humidifier ta sanya turare a ciki ta turara masa d'akin. Kana ta dawo parlorn nan ko ta tarda ya ci sosai kam har ya ture, hamdala tayi ga Allah ganin yaci d'in sai dai kuma yana yin na shi ya d'an razanata ba kad'an ba.

Cewa tayi " a sake kiran Yaa Adnan d'in ne ko kawai mu tafi asibiti ne?". Girgiza kai yayi yana cewa " no need, don suna hanya yanzu haka zasu kawo min magani ".  Tace " toh, ko zaka shiga ciki ka kwanta kafin su zo d'in ?" Ok yace, yanzu ma ita ta taimaka masa ya shiga ciki ya kwanta yana lumshe idanun don sosai yanayin d'akin yayi masa dad'i kashe AC tayi ta masa lullub'i ta fita. Gyara masa parlorn tayi ta koma ta ciro burnern da humidifiern shi ma ta sanya masa k'amshi, sake lek'ashi tayi ta tarda yana bacci silenty ta rufe d'akin ta koma tana k'arasa gyaran parlorn. Tana yi tana duba shi har ta kammala, saida ta kammala har da wanke kayan da ya b'ata musu ita da shi a daren jiya da amai babu k'yama ko wani abu.


San da ta kammala komai ne taji wata iriyar gajiya ta sark'afeta ashe aikin gidan ba kad'an ba ne, dole a ce za'a kawo mata 'yar aiki amma kuma ya zata yi tunda mai gidan ba ya so.


Canja kaya tayi zuwa doguwar rigar atamfa mai bud'ad'den k'asa, simple d'aurin d'an kwali tayi ta fito zuwa parlor. Baiwar Allah sai lokacin ta samu sukunin yin breakfast da sauran porridge d'in da ta had'a masa ta sha tea, wayarta ta d'auka tana mai tunanin sanar da gida sai kuma ta kwab'i kanta gudun a samu matsala sanin halin kayanta.


Kiran wayar da ta saba a kowace safiya shi tayi musu, ta kira Ummu sun d'an dad'e suna hira kafin ta katse. Kana ta kira Abbu shi ma sun dad'e da shi yana ta tsokanarta kamar wani kakanta, murmushi tayi kawai tana masa shagwab'a. Kamar yadda ya saba tambayarta ko tana cikin matsala ko damuwa haka yau ma yayi, sai dai amsar d'aya ce ba ta da damuwa nasiha ya sake mata kafin sukayi sallama. Lumshe idanu tayi tana mai jin kewar gidansu na kamata, kamar ta bud'e idanu ta ganta a Abujan haka taji sai dai babu dama.

Hajjah ta kira tana d'agawa tace " 'yar tusa wai da gaske k'auran kika yi ne?'' Cewa tayi " girma dai nayi ina adduarku kenan in girman?". Dariya ta sanya tana cewa " addduar ta mu ta amsu kenan? Ai ko bari in kirawo Tayyib in shaida masa a fara shirin siyan miki shoprite d'in ".


Juya idanu tayi tana cewa " sai kin dawo " dariya ta sanya jin yadda take maganar ba a sake da ta saba ba kamar dai da damuwa a harshen nata, cewa tayi " Lelena, kina lafiya kuwa?".

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now