CHAPTER 18 ( HER EFFECT)

Start from the beginning
                                    

Suna dawowa ne aka fara cin abinci, nan Suleim ta tab'e baki tana kawar da kai gefe. Kallonta Aunty Fadwah tayi tana mai cewa " ke kuma fa? Lafiya dai ko?". Yatsina fuska tayi tana cewa " lafiya lau, yawwa gender reveal party d'in mu is next weekend". Zare idanu tayi tana cewa " you don't mean it". Lumshe idanunta tayi tace " seriously oo, da cikin week muka so but things came up had to shift it to weekend".

"Can't wait " ta furta cikeda d'oki Aunty Ainah dake gefensu ne ta kalleta tace " Ku kuma hala har yanzu amarcin ku ke ci", shiyasa har yanzu shiru sai walk'iya da kike yi kamar tarwad'a". Tsit wurin ya d'auka kamar anyi ruwa an d'auke, yayinda hankalin kowa ya dawo kanta murmushi ta sanya tana had'iye shinkafar da ta kai bakinta ba tareda ta iya furta ko kalma d'aya ba. Ya Budu ce tace " yoh me yafi ran ta mijinta na kulawa da ita? Wa ma ya sani k'ila ma cikin ne a jikinta ?".

Tab'e baki tayi tana cewa " babu wani alamun ciki a nan, kina ganinta kin san amarci ake kan ci ". Aunty Hafizah tace "toh Allah ya basu mai amfani, ai amarci ba k'arya ba ne kowa ya ci iya cinshi lokaci ne". Ya Budu tace " ai kuwa". Daga haka ta maida kan ta ga masu maganar gender reveal, ita ma bata tanka ba sai kawai taci gaba da cin abincinta amma deepdown ta d'an ji maganar ta dake ta. Ita ma tana son haihuwa amma ta tabbatar ba dai a nan kusa ba, don har yanzu zamanta bai d'au saiti da Burhaan ba balle har a fara maganar samun ciki wa lakin fadlu rabbaniy.

A haka aka k'are zaman aka tashi, kamar yadda ta saba kowani meeting yau ma gidan Ummu ta wuce. A can ta k'arashe sauran yinin na ta sai bayan ishai kafin Islaam d'in ya zo, yau kam har da cin abinci kafin suka fito zuwa gida.

Kamar yadda suka tafi silenty haka yanzu ma suka dawo, ba ka jin sautin komai a motar sai na saukar numfashinsu haka har suka isa gidan.

Washe garin ranar after 2 ta fita zuwa sunan wata Sahla da suke abun arziki sosai, client d'in ta ce for about 3 years hatta gyaran biki da makeup a wurinsu tayi. Hakan ya sa zumuncinsu ya k'arfafa sosai, haihuwar fari da tayi d'an ya mutu ba kuma ta je mata ba kuma da ita aka yi biki tundaga ranar farko har aka kawota gida kai har bayan bikin ma ta zo. Wannan kam tun cikin yana k'arami ake jaddada mata, ta kuma yi alk'awarin zuwar mata. Tun last 2 days ta shaidawa Islaam as always cewa yayi " sai kin dawo " yayi wucewarshi zuwa ciki, dama a parlor ta tarda shi yana shan tea.

Abaya ta sanya kawai da gyalenta, ta d'auko jakarta da car key ta fito. A hankali ta ja motar zuwa hall d'in da aka shirya taron sunan a Mogadishu dake Kaduna. Sanda ta isa har hidimar sunan ya kankama, mai jego an cakare wuri ya d'auki harama. Barka tayi mata ta d'auki Babyn mai kyau da ita, mai suna Nihal gift d'inta ta ajiye musu kafin ta samu wuri ta zauna.

A na gabatar da taro rabin hankalinta yana kai while rabin ke kan matan dake zaune gefenta dake hirar halayen maza ( damuwar mata a gidan biki da suna ). Maganar tasu akwai tausayi amma kuma abun dariya yafi yawa, ko dan yanda d'aya ta dage wajen fad'in " ga su shegen sai masifar shiga rai, kunamu ne fa ga zak'i ga harbi yanzu a kunna ki amma kuma you can't survive a day without them". D'ayan ta cab'e wurin cewa " ke dai bari, nan zan ji na tsani Honey but the next minute ni ke neman kayana kafin ma ya bani hak'uri na sauka". Dariya suka kwashe da shi d'ayar ta dafa Nadeefah tana mai cewa " wallahi sis ni fa tausayin 'yan mata nake yi, ki ga a waje kamar a cinye mace amma da ta shiga ciki ki ga ana mata abu kamar ba a sonta ". Ta k'arashe da alamun son sa ta a hirar ta su, shiru tayi tana jujjuya maganar kafin ta kai ga amsawa d'ayar tace.

"Nan fa soyayyar take Umm Ismat, ni fa da kafin aure Miji nagari nake kiran Abban Saif amma yanzu cab'din". Sake dariya suka yi har da Nadeefahr da tayi murmushi, sai time d'in tace " amma fa ba laifin su mazan ba ne ba kuma an daina soyayyar ba ne, ina ganin har da zaman tare da kuma dad'in responsibility yake sa mazan mu su canja daga yanda muka sansu. Ba kuma sun canja bane Aa fahimtar su da mukayi ne ke sa hakan".

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now