CHAPTER 14 ( DAY ONE)

Start from the beginning
                                    

Farhan ne yace " da alamu wani yana buk'atar privacy, go ahead and cut the line" lumshe idanu yayi yana mai cewa " ai ba sai an ce min ba, kuma dai ku tafi wurin matayenku ba ku tsaya k'ananun iskanci ba". Daga haka ya katse yana mai jin yanayin jiya na dawo masa, runtse idanu yayi ya na kwantar da kanshi a jikin couch d'in da yake zaune.

"Nda watu" ta furta a d'an tsorace bayan ta ajiye turaren hannunta, a harzuk'e ya taso yana kallonta. Sai kuma ya yafito ta kamar abun arziki, tahowa tayi cikin sanyin jiki. A kujerar gefenshi ta zauna kan ta a k'asa, shi ko har time d'in idonshi na kanta.

K'wafa yayi yana cewa " you!! Didn't i warned you about talking to me? Ehhh?". Kasa magana tayi sai kawai ta girgiza kan ta, ya cigaba da cewa " ohh saboda kin raina ni shi ne kika yi ko? I've told you ba ruwanki dani just live your live here, kamar kina zaman kanki like no one exist in this house sai ke and you'll be absolutely in peace with me".

"I'm sorry Yaa Islaam" ta furta hawaye yana taruwa a idanunta, tsaki yaja yana cewa " you are not sorry, but you'll be sorry. Ki sake zuwa inda nake you'll see, now get the hell outta ma sight mayya!!!". A guje ta ruga izuwa room d'in ta a parlor ta kwanta kan rug ta sa kuka, duk yadda ta so daure maganganunshi ta kasa yanzu kam ta yards da cewa ba k'aramin aiki ba ne a gabanta a ce mijinka bai son ko ganinka? Ya rabb!!.

Kukanta tayi ma'ishi ta godewa Allah, ita da kanta ta bawa kanta hak'uri ta share hawayenta. Kana ta lallab'a zuwa bedroom d'inta ta kwanta, tana mai jin nauyi a zuciyarta a haka wani wahalallen bacci ya d'auketa.

A parlorn tana wucewa shi ma ya tashi, part d'in shi ya koma. Gyaran d'akin yayi ya sa turaren wuta shi ma, kafin yayi wanka. Tsayawa yayi a gaban mirror yana mai kallon kanshi a zahirance, but a bad'ini tunani ya tafi. Girgiza kai yayi kawai yana mai lissafin inda ya kamata yaje, ba zai iya zama a gidan nan ba gwara kawai yaje clinic dukda an bashi 2 weeks amma shi dai bai amsa ba don bai ga amfaninsu ba.

Shiryawa yayi tsaf cikin Teal colored tuxedos suit da wando sai white shirt da tie shi ma teal d'in, briefcase d'in shi ya rik'e bayan ya sa bak'ak'en single monk straps k'irar milano. Kan nan yana ta shek'in hair cream na ga k'amshinshi na dindindin da ya game room d'in, ta k'ofar baya ya fita hakan ya sanya bata san da fitar ta shi ba ga shi dama bacci takeyi.

Ita ko baccinta takeyi hanian ko san da Safwaan ya kawo musu breakfast a waiting room ya ajiye don k'ofar living room is locked, ya kuma kira ta bata d'aga ba gudun kar ya takura musu ya sa shi k'in knocking sai ma komawar da yayi gida with a heavy heart. Don tunanikan da k'wak'walshi ta bashi is not that healthy, a wahalce ya koma gida cikeda alhini a yau kam ya hak'ura da Nadeefah har abada don ya tabbatar da ba zata tab'a zama tashi ba.

Yana shiga clinic d'in haka aka bishi da idanu, don kowa ya san da labarin d'aurin aurenshi shekaran jiya amma sai ga shi yau a office. Sai dai ba wanda ya tanka saboda kowa ya san halinshi na rashin wasa da mutane, and bai entertaining shisshigi shiyasa kowa yake d'ari-d'ari da shi tun daga kan Soldiers, Doctors, Nurses, Lab workers, Radiographers har zuwa department d'in su wato physiotherapy.

Ba wai tsoronshi suke ji ba aa kwarjini yake dashi and he's among the best workers da ake ji dasu a asibitin. Kai baa ma asibitin ba a Kaduna baki d'aya, last year har award aka bashi as NO.1 practicing physiotherapist a Nigeria a NPS banda sauran awards da yake samu. Ya na da nashi clinic d'in mai suna BAY physio clinic amma yafi zuwa asibitin sojoji na 44, na shin kuma sai time-time yake zuwa. Suma 44 d'in ba k'aramin ji dashi sukeyi ba, ko dan baiwar da Allah ya zuba na ilhama da ilimi a k'walwarshi ga iya aiki kamar machine. Wasu da yawa ma gani sukeyi abunda ya sa yake girman kai kenan, abinda basu sani ba shi ne haka halittarshi take ko san da yana d'alibi har kuma a gida.

Direct office d'in shi ya wuce, zama yayi bayan ya rataye suit d'in na shi a hanger. Wayarshi ya d'auko yana placing order na breakfast a eateryn da ya saba breakfast. Yana ajiye wayar Adnan yana fad'owa cikin office d'in , tsayawa yayi yana kallonshi cikeda mamaki.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now