CHAPTER 9 ( THE RIDE)

Start from the beginning
                                    

"Hala kin manta da tafiyar kune ko?" Ta tambaya tana kallonta cikeda mamaki, tab'e baki tayi cikin kasala sai dai bata tanka ba don bata iya magana immediately in ta farka daga bacci ba. Instead sai toilet ta nufa bayan ta had'e hannunta alamun sorry, ruwa ta sakar ma kanta bayan ta sa shower cap for like 5minutes.

Sai da taji jikinta ya saki kafin ta sanya shower gel na rose gold na Hemani ta wanke sak'o da lungun jikinta tas ta d'auraye jikinta ta d'auro alwala kafin ta fito, har lokacin tana d'akin.


Mirror ta nufa tana goge jikinta tana mai cewa " I'm sorry Ummulkhair! I thought sai after 4 zamu tafi shiyasa ma nayi baccin". Girgiza kai tayi tana cewa " Allah ya shirya ki dai, duk salon kar ku tafi tare ne ai na ganoki. Kiyi sauri ki shirya ki fito kar ki b'ata masa lokaci". Toh tace ita kuma ta fita kar ta bar shi shiru.

Suncream ta shafa sai oil na snail da yake signaturen ta, shi ma duk na Hemani. Free gown  spindrift colored na Giorgio Armani ta sa sai veil salmon bata samu damar waxing kan ba but ta shafe shi da cream d'in shi mai matuk'ar k'amshi da sa taushi na Yerwa Cosmetics sai tayi spraying kawai. Handbag d'inta ta d'auko salmon sai takalma palms su kuma black, duba dak'in tayi sai da ta tabbatar da ba abinda ta manta kafin ta tofe d'akin da addua ta rufe tana sauka k'asa daman trolleyn ta already yana butt d'in motarshi.


Zuwa time d'in ya k'ulu iya k'uluwa shi fa a duniyar shi ya tsani jira, jirar ma na abinda ba zai amfane shi ba. Sake kallon agogo yayi a kaikaice yana mai tsoki a k'asan ran shi time sai tafiya yake yi, ko sanda Ummu tace masa " yanzu zata sauko tana wanka" kawai yaji ta ne ya amsa da toh amma ji yayi kamar yayi tafiyar shi babu ita.

Saukowa ta fara yi wanda kafin ma ta k'araso turaren ya riga da ya fallasa fitowar tata, hararar gefenta yayi yana nufar waje. Warming motar yayi kafin suka k'araso ita da Ummu dake rik'e da handbag d'in ta.


Shagwab'ar da take yi ba k'aramin tunzura shi yakeyi ba dama ga haushi goma da ashirin nata da yake ji, nan abu ya taru yayi masa yawa. Yana jin tab'ararta har ta gama ta shiga motar a hankali yace " toh Ummu zamu wuce" da murmushi tace " Allah ya tsare hanya Burhaan ya sauke ku lafiya" Ameen ya amsa, ta maida akalan maganarta ga Lelen tana cewa " Bibtie Allah ya tsare, ki kula".


A hankali tace " I'll in shaa Allah, I'll miss you ". Ta furta a karo na barkatai tun fitowar su, kanta ta shafa tace " I'll miss you too". Daga haka ta cire hannunta tana d'aga musu ganin ya tada motar, itama hannun ta d'ago mata alamun bye. Tana tsaye a wurin har ya ja motar suka fita daga gidan, komawa ciki tayi  tana jin kewa na kamata. Duk da ba zama take yi a gidan sosai ba, amma duk sanda zata bar gidan sai taji kamar kar ta tafi.


Sai da suka hau titi da kyau kafin ta dube shi cikin k'asa da murya tace " ina wuni Ya..." Wani kallon da ya jefa mata ya sanyata had'iyar yawu, tana mai kasa k'arasawa daga wannan kallon shi ma bai tanka ba sai maida kan shi da yayi a kan titi.



Lumshe idanu tayi kawai yayinda taji har ta gundura da tafiyar tun ba a fara ba ma, sai kuma ta bud'e tana kallon hanya. Instead of ya kama hanya kai tsaye sai taga yabi ta Maitama roundabout A ya shiga ta cikin Maitama inda sai da suka sha fama da hold up kafin ya isa inda zashi, a Cilantro yayi parking.


Shiga ciki yayi ya barta a nan bai ce mata uffan ba, kallon agogonta tayi tana fiddo wayarta. Sai da yayi more than 40 mins a ciki don har an fara kiran Asr kafin ya fito, da ledoji a hannunshi back door ya bud'e ya zuba su a ciki kafin shi ma ya shigo.

Tada motar yayi yana mai mak'ala iPod a kunne, ta baya ya sake bi sai gasu sun b'ullo Alvan Ikoku way a lokacin har an soma sallah a masallatai. Tsayawa a wani masallaci yayi ya sallaci Asr, shima sai da ya d'auki time bayan idar da sallahn kamar ma ya manta da wata a mota. Ita dai tana zaune jingine da kujera, ya shigo yana gyatsina kamar yaga kashi.



NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now