21

101 8 1
                                    

*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.

*©️Halimahz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(21)*
Na rumtse ido ina jin zuciyata na bala'in matsewa, muryana a hankali kuma a raunane na ce,"ba haka ba ne Hajjo kiyi min alfarmar tsayawa kiji ta bakina kar ki yanke irin hukuncin su Kaka...".

Murya ta ɗaga wajen dakatar da ni,"dalla can rufe min baki, wanne irin iskanci ne da rashin sanin darajar iyaye yasa za ki ƙi dafa abinci ki bawa uwar mijinki, dan ubanki da bata haiifa ba har kya ganshi ki so ki aure, wawiya kawai idan ba ki bi uwar miji ba ta ina za ki kama mijin naki a tafin hannu, ko haka kika ga matan yayyunki na wa mahaifiyarki, ba gida guda su ke ba amma kullum da kwanon abincinta a gidan matar Sa'id. Kishiya kuma akanki a ka soma? kaf cikin mu biyar da mahaifiyarmu ta haifa wa kike gani tana zaune ita ɗaya banda mahaifiyarki? Kuma ƴan uwanki Samira da Husna duk ba kishiyoyin ne da su ba, kin taɓa zuwa kinga wacca kishiyarta ta zauna akanta? Ko kin taɓa jin wata cikinsu mijinta ya kai ƙararta akan kishiya, sai ke saboda sakarci da shashanci za ki ɓata rawarki da tsalle, to ki shiga taitayinki wallahi, kar na ƙara jin makamanciyar magana irin haka ta kin hana uwar mijinki abinci, ita kam ko ce tayi ki kwanta tabi ta kanki ki kwanta biyayya dole, Saboda haka yanzu muna gama wayar da ke ki wuce ki girka abinci ki kai mata tare da bata haƙuri kina jina".

Na ɗaga kai kamar ina gabanta na ce,"zan bi umarninki in yi yacca kika ce in sha Allah".

Sai kuma ta kama yi min faɗa sosai akan rashin bashi hakkinsa da na ke, shi ko kunyar kai mata wannan ƙarar ma bai yi ba. Tana faɗan tana haɗawa da aya da hadisi har ta gama kana mu kai sallama da ita bayan ce min da tayi tana tafe nan da anjima zata zo in gwada mata kalar iskancin da nake yi tunda har an iya akai min akwatuna na watso su waje.
Na miƙa masa wayarsa suka ci gaba da magana da ita, ina ji tana ce masa,"kayi haƙuri Nazifi, na dai yi mata faɗa idan taji ta gyara shikenan, idan kuwa bata gyara ba kanta ta yiwa kuma ba kowa ta wulaƙanta ba sai iyayenta".

Yay mata godiya suka yi sallama, ya fita a ɗakin na raka shi da kallo, kafin na miƙe cikin karaya wasu zafafan hawaye na sauka akan kuncina yayinda a zuciyata na ke faɗin tsakanina da Nazifi sai Allah ya saka min.

Shayi na dafa na zuba a flask daidai cikin mutum guda, kana na ɗora taliya fara dama akwai sauran miya. Don haka abincin da na haɗa na daidai cikin Iyam ne ita kaɗai, na ɗeba na kai mata ɗaki, basu ma san da shigowata ba saboda shewa da hayaniyar da suke yi, can na hango Iyam daga wajen wadrobe ɗinta ƴaƴan jikoki sun sakata gaba tana yi musu wasa, na wuce mutanen kan hanyar da babu wanda ya amsa sallamata a cikinsu, na durƙusa har ƙasa na bata haƙuri bata dai ce da ni komai ba na ta shi na fita bayan na aje mata abincin, ina jin Ummaa na faɗin Allah ya shiryeni yasa kishiya ta koya min hankali, a raina na ce ta dai koya muku.

Da rana ina zaune da waya a hannu, na kunna data na hau whatsapp, da ma ni shi kaɗai na ke dan shi kawai Nazifi ya yarje min in ke yi, babbar wayar ma da ƙaƙa ya bari na riƙe, Ina cikin kallon status na buɗe na Adamu ƙaninsa, nan take na yi karo da hoton da ya zamar min yajin albasa a ido. Hotuna da bidiyo na Nazifi da Amayarsa, irin hotunan nan da ake yi na kafin aure, kasa ɗauke ƙwayar idona nayi akai, kyan da suka yi ko hasidin iza hasadun, shi ya saka yadi me tsada ita kuma cikin wata doguwar riga ta net, kana ganinta ka ga jinin shuwa, hanci kaman tsinin biro ga ido da gashin ido masha'Allah, ba ƙarya tana da kyau iyakar kyau irin kyan da namiji ba zai gani ya ƙyale ba, wataƙila kuma wannan kyan shi ya ruɗe shi domin a rayuwarsa yana matuƙar son kyakykyawar mace. da gani ta girmeni kam zata iya ba ni shekaru uku, idonta kaɗai zai shaida maka a waye take kuma tasha boko kamar yanda ya faɗa, ban san lokacin da na jefar da wayata ba ganin yacca a bidiyon yake faman ruƙota zuwa jikinsa ita kuma har tana kwantar da kai a ƙirjinsa.

Kaina na jinginar jikin gado ina hawaye sosai. Tsawon wani lokaci wayata tayi ƙara na ɗauko, sabuwar lamba na gani a jiki, muryata na saita kana na ɗaga tare da yin sallama.
Daga can ɓangaren aka ce,"Ke Sauna ba hoton mijinki da wata na ke gani ba yana yawo a IG?". Muryar kawai ta shaida min wacece, kuma sosai nayi farin ciki da kiran nata, Safiyya ce ƙawata ta ƙud da ƙud tun aji ɗaya a makarantar boko, ita kaɗai ce wadda yau zan nuna in kirata da sunan ƙawa, ina sonta fiye da yanda take sona kamar yanda itama ke cewa tana sona fiye da yanda na ke sonta, rabona da ita kusan shekara uku da rabi kenan da Babansu Allah ya ɗaga shi gwamnati ta ba shi matsayi suka koma Abuja da zama.

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now