12

63 8 0
                                    

*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.

*©️Halimahz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(12)*
motarsa ta faka a ma'adanar motoci, ya fito daga cikin motar hannunsa riƙe da leda fara me ɗauke da tambarin gidan abinci. me gadi yay masa sannu zuwa shi kuma ya shige bayan gaisawarsu. da shigarsa falo ya aje ledar akan kujera, ƙarasawa yay ya kunna tv ya dawo ya zauna, can kuma ya miƙe tare da ɗaukar ledar ya shiga kitchen, abincin da ke cikin takeaway ɗin ya juye a plate, duk abin da yake yana yi yana bin kitchen ɗin da kallo, gani yake kamar zai ga Sa'ida ta bayyana da wannan annurin a fuskarta, fuskar da kana gani zaka tsinci zallar so da ƙaunar kyautatawa mijinta, fuskar da bata nuna fushi ko da tana cikin damuwa, ko da ta gaji zaka ga akwai murmushi a fuskarta.

cikin sanyin jiki ya fito daga kitchen ɗin ɗauke da plate a hannunsa, duk cikin kwanaki shida da suka wuce yaune ranar da ya fi jin gidan ya masa mugun girma, haka kuma yau yafi jin yana matuƙar kewar matar gidan. zama yay yana cin abinci sai dai cinsa yake yana jin kamar magani, bai sani ba rashin daɗin daga bakinsa ne ko kuma daga abincin ne, duk da dai yana ɗora hakan ma akan damuwar da yake ciki, don faruwar lamarin su Atika yasa Iyam ta ɗauki fushi da shi, tana faɗa masa lallai sai dai ya zaɓa ko yaran ko kuma muguwar matarsa juya wadda bata san darajar ɗa ba.

shi bai taɓa sanin Sa'ida ce gidan nan ba sai bayan tafiyarta, don ranar da ya dawo jin gidan yay ya zama tamkar kango, ga dai shi ba wai suna good time da ita ba ne, haka ba wuri guda su ke kwanciya ba, amma sai yaji ashe motsinta ma a gidan rahama ne, a washegari kuwa da safiya tayi babu abincin safe babu na rana sai yaji duk kewarta ta cika shi, duk da ko kusa bai nadamar turata gida, haka ya gangara ya tafi gidansu zai ci abinci saboda shi ba mai son na siyarwa ba ne, sai dai yana zuwa Iyam tayi masa gate tace ai yanda ba'a bawa yara abinci a gidansa haka itama abincin gidanta ya daina ci duk da gidan ubansa ne, dole yana ji yana ganin abincin da yake so ya tafi ya barshi, sai ƙanwarsa Basira ya kira ta kai masa office da yake bassu nisa da gidanta.

kasa cin abincin yayi ya ajiye ya kwantar da kansa a jikin kujera, idanuwansa a rufe tamkar mai bacci, ya jima a haka kafin ya buɗe ido yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa. lambarta ya danna sai dai bai latsa kira ya tafi ba, sunan da ke kan screen ɗin kawai yake kallo, shi kam har ga Allah ko da yace ta tafi bai taɓa tsammanin zata yi zuciyar tafiya ba, kamar yanda bai taɓa tsammanin za'a yi kwanaki har bakwai babu kiranta babu saƙonta, saboda shi ya san wace ita akan haƙuri, kuma shi ya san wace Sa'ida akan son Nazifi.

Numfashi ya sauke ya ajiye wayar a gefe yana so ya daure kar ya kirata ɗin amma ya kasa daurewa saboda mugun kewarta da ke addabar zuciyarsa, sai dai yana kira aka shaida masa wayar a kashe. wannan hakan kuma ya taɓa zuciyarsa, kallon agogon falon yayi wanda yake ɗauke da hotonsa da nata, hoton tun na ɗaurin aurensu ne, kuma agogon Yaya ce ta basu gudunmawarsa. ƙarfe huɗu da rabi na yamma, ya sauke numfashi ya rumtse ido gam tare da riƙe kansa, anya yau zai iya kwana shi ɗaya a gidan nan? anya zai iya kwana a koma ina ne babu motsin Sa'ida?

miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara yana isa gaban TV ya kashe, sannan ya dawo ya ɗauki maƙullan mota ya fita ba tare da tunanin ina za shi ba, shi dai kawai zai fita ɗin ne don neman mafitar da zuciyarsa ta bashi.
********
na fito daga wanka na saka kaya, ina tsaye na kasa fita sai saƙa da warwara na ke yi, Sauda ta shigo ɗakin tana cewa,"wai ba ki shirya ba? kin san fa yacca abin hawa yake ga shi har biyar da rabi saura, kar muna bakin titi su Abbaa su dawo mu sha faɗa, naga kamar ma ba ki son tafiyar".

ba tare da ta lura ba na share hawayena, a sanyaye ina murmushin dole nace mata,"ke kin raina gida ne, ni in da za'a barni ma ai shekara zanyi".

tana dariya ta ce,"cabɗi abinda ba zai yiwu ba kenan. bara na ɗauko mayafina". ta faɗa tana juyawa ta fita.

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now