09

91 10 0
                                    

*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''

*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
'''for your business advert chartup 09030398006.'''
______________________________
*(9)*
murmushin manyance naji yayi, bana ganinsa amma ina da tabbacin sai da ya gyaɗa kai kafin ya ce,"yaro yaro ne". kana ya ƙara cewa,"na sani soyayyar da kike mana zata iya sawa ki zubar da hawaye musamman idan kika tuna cewa akwai wani tabbataccen lokaci da dole mutuwa zata raba mu. sai dai ba hakan ne musababbin kukan na ki ba, muryarki kawai ta shaida min akwai matsala, haka ne?".

na rumtse ido nace,"haka ne Abbaa".

"to me yasa za ki ɓoye min?".
"kayi haƙuri Abbaa".

yay shiru na ƴan sakanni kafin yay gyaran murya. "saurare ni da kyau Sa'ida. mu iyayenki ne, babu wanda zai tsaya miki tsayin daka a duniyar nan sama da mu bayan mahallicinki. adu'armu a gareki kaɗai ta isa ta magance miki kowacce matsala da kike ciki, kuma ki sani adu'a na canja ƙaddara". yay amfani da kwantaccen lafazi wajen faɗin hakan.

murya na rawa na amasa,"haka ne Abbaa, ba wai na ɓoye muku ba ne saboda tunanin ba zaku iya min komai ba, kawai shiga damuwarku akan hakan yasa Abbaa, amma kayi haƙuri Abbaa, adu'arka kawai na ke so".

nayi maganar da muryar kuka ina me share hawayena.

"Sa'ida ni mahaifinki ne, ba lallai sai kin ɓoye min kina cikin matsala da damuwa ba, muryarki zata bayyana min. ba zan tsaya shiga sha'anin aurenki ba, sai dai ina so na tuna miki duk lokacin da tsananin rayuwa ya dame ki, abu na farko da zai sa ki farin ciki shi ne ki tuna ke musulma ce kuma Masoyiyar Manzon ALLAH [S.A.W]. Duk tsananin da kike ciki ki tuna cewa akwai wanda ya fiki shiga tsanani, Ki tuna cewa kinfi mutane da yawa jin daɗin rayuwa. wannan rayuwar tamu ta duniya da kike gani gaba ɗayanta jarrabawa ce, Sa'ida aure kan saka mutum ya yi farin ciki a rayuwa sai dai duk tsananin farin ciki ba shi zai hana ma’aurata fuskantar matsaloli ba. ba abin mamaki ba ne idan a wasu lokuta anata fuskantar matsaloli a auratayya, domin rayuwar aure gaba ɗayanta haƙuri ce, haka kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan auranta. ko babu komai ki gode Allah da ya baki miji me tsananin sonki da ƙaunarki gami da tausayinki. ni dai abin da na ke so da ke kar da ki dinƙa barin damuwa a ranki, hakan zai cutar da ke. kamata yayi duk san da kika kasance cikin halin tsanani, to ki ɗaura alwala ki fuskanci alƙibla ki gana da ubangijinki, a gaban mahallicinki ya kamata ki zubda tarin hawayenki, ki ƙaskantar da kanki a gabansa kina me roƙonsa cikin kirari da tsarkakewa, shi ya san halin da kike ciki kuma shi zai magance miki. kuma hakan zai sa ki samu rangwamen komai, tun haihuwarki mu ke miki addu'a kuma ba zamu daina ba har mu kai ga kushewa, kuma ina miki alƙawarin ƙara dagewa akan yi miki adu'a Ƴata. Allah bai hanaki don baya sonki ba, bai bawa wasu don yafi sonsu akanki ba, kema yana sonki kuma zai ba ki mafificin alkhairi cikin yardarsa da amincinsa. Allah yay miki albarka, Allah ya shiga dukkan lamuranki, ya yaye miki dukkan ƙunci, ya kawo miki salama da natsuwa. ayi haƙuri a ƙara haƙuri a kuma ci gaba da haƙuri kinji ƴar albarka, ina faɗa miki hakan ba kuma zan fasa faɗa miki ba ko da yaushe; haƙuri, uzuri, kawar da kai da kuma yafiya, ki kamasu tabbas kin kama makaman nasara da farin ciki, Sa'ida wanda ba ya haƙuri ba ya uzuri ba kuma ya yafiya to shi ne ke samun naƙasun farin ciki, amma me haƙuri da tawakkali da fawwalawa Allah komai wallahi ba ya tawaya, bayan tsanani sai daɗi da izinin Allah".

yay shiru, ni kuma kukana ya ƙwace, cikin muryar da ta disashe da majina na ce,"na gode Abbaa nah, na gode sosai, ubangiji Allah ƙara muku lafiya, yaja min da ranku, yasa kuyi kyakykyawan ƙarshe".

"amin ya Allah ƴar albarka. amma ki daina kukan, ki kuma yi min alƙawarin ba za ki ƙara ba".

"in sha Allahu Abbaa".
"zan tura miki kuɗi sai dai kiyi hakuri babu yawa".
"na gode Abbaa Allah ƙara arziƙi da wadata"
"amin ya Rahman, sai gobe kwayi waya da Ummanin, kar taji ki a wannan yanayin ta hana kanta sukuni, Allah ya sadamu da alkhairinsa, ki gaida ɗan nawa".

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now