03

102 8 0
                                    

*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''

*©️Halimahz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
________________________
'''for your business advert chartup 09030398006.'''
_______________________
*(3)*
Washegari ban farka ba sai wajen ƙarfe tara da rabi na safe dalilin bacci da wuri da ban samu nayi ba, sai dai Alhamdulillahi isassan baccin da na samu yau ɗin da ya kaini har wannan lokacin sai ya zamana ban tashi da ciwon kai da zazzaɓi kamar yanda na saba tashi da su ba a ƴan kwanakin nan. Sai da na gyara ɗakinsa tukunna na fita na wuce ɗakina, kafin na haura saman kuma sai da na tsaya na buɗe ƙofa saboda zuwan mai yi min wanke wanke da share share.

Ko da nayi wanka na ke shiryawa zuciyata cike take fal da matuƙar mamaki gami da saƙe-saƙe daban daban akan al'ammarin nan mai girman gaske, yo mai girman gaske mana tunda miji bai kwana a gida ba bayan ba tafiya yayi ba, kuma abin da bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru. Har yanzu ƙarfe goma sha ɗaya da na ke muku wannan maganar banga alamun Hubbi ya dawo gidan ba, na leƙa farfajiyar gidan babu motar da ya fita da ita. Nauyayyan numfashi na sauke, tarin tambayoyin da ke kaina a game da inda ya kwana da rashin dawowarsa da abin da ya tsaresa suna da yawan da har suke neman fasa min kai.

Wayata da ke ajiye kan madubi na ɗauka zan kira wayarsa, ina buɗeta kuwa na fara cin karo da saƙonsa na jiya da yake faɗa min ba ya son damu. Da sauri kuwa na dire wayar ina kulle idona kafin na buɗe bayan wucewar daƙiƙa ɗaya. zuciyata cike da ƙunci na fita a ɗaki na sauka ƙasa, a falo na tarar da mai aiki tana goge gogen gilasai, wanda tuni ta gama shara, ko'ina ya ɗau ƙamshi, dama ni ɗin gwanar ƙamshi baka taɓa zuwa ka riski gidana ba ya tashin ƙamashi tun daga harabar waje.
Muka gaisa da ita na wuce kitchen, ruwan shayi na dafa na soya ƙwai, na zubo nawa na barwa mai aiki nata, falon na dawo na zauna na kunna tv, ina shan shayin ina kallo hankali da tunanina kuma na can wani wajen.

Motsin buɗe ƙofa yasa na juya kaina wurin, Hubbi na gani ya shigo yanayinsa kamar tashin bom, ko inda na ke zaune bai kalla ba yay wucewarsa sama fuuuu kai kace tashin iska, ni kuwa nabi bayansa da kallo zuciyata na zullo, kamar in share shi amma sai naji ba zan iya ba, lokaci ɗaya naji abin da nake ci ya fita akaina, hakan yasa na dire na miƙe nabi bayansa da sassarfa. Ina shiga ɗakin na tarar har ya shiga banɗaki, nayi tsaye bakin wadrobe kamar munafuka ƙirjina sai bugawa yake saboda bala'in tsoron da ban san ta ina ya zo ba, wucewar wasu mintuna na dawo hayyacina na buɗe wadrobe ɗin na kwaso masa kayan da zai saka na zaman gida, na ajiye anan gefen gado, duk wani abu da na san zai buƙata na ɗauko na ajiye masa.

Mutumin da ba ya jimawa a banɗaki shi ne yau sai da na fara fidda tsammanin zai fito tukunna sai ga shi ya fito, ƙugunsa ɗaure da towel sai wani ƙarami kuma a hannunsa yana goge ruwan kansa da jikinsa. Ta gabana ya wuce ya isa wajen mudubi, yaja stool ya zauna ya shiga shafa mai, ni dai kallonsa kawai nake yi, wallahi kamar sabon mutum ba mijina ba, maganar da na ke ta so nayi ta gagara fitowa, na rasa tantance abin da nake ji a ƙirjina, tsoro ne ko kuwa shakka. haka ya gama shafa mai da oil perfumes na oud ya taso, yana niyyar buɗe wadrobe idonsa ya kai kan kayan da na ajiye, idonsa ya ɗauke akansu ya ɗago yana kallona, kamar me shirin faɗar wani abun amma sai bai ce komai ba. Kayan ya ɗauka ya saka, jallabiya ce milk ƙirar dubai.

Gado ya haye ya jingina bayansa da filo, sai a sannan na sami zarafin yin magana nace,"Hubbi wai lafiya?".

Shiru bai amsa min ba kamar ma ba da shi nayi maganar ba. Na danne abin da na ke ji a zuciyata cikin raunin murya na ƙara cewa,"Hubbi wai me yake faruwa?, in da akwai wata matsalar ka faɗa min don Allah, jiya fa baka kwana a gidan nan ba, kuma yanzu ka dawo ka ƙi ce min komai, gaba ɗaya fa ka sani cikin damuwa da tashin hankali, idan laifi na maka bisa rashin sani ka faɗa min na gyara in kuma nemi afuwarka, kai ɗin fa shugabana ne".

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now