Rabona da shi tun ana sati daya biki, bame zuwa gida, jin nayi shiru Ashiya tace haba Aisha karki ja ma ya'yan ki zama marayu man, kin fa San condition naki, nasan da ciwo amma try to put yourself together, yadda inta zo bazata rena ki ba, ki cigaba da shan hadin nan ki dawo da jikin ki, look good for your husband..

Ashiya sai zuba ta keyi amma sam ni ba jinta na keyi ba, tsabar zurfafa da nayi cikin tunani.

9pm

Aka kawo Amarya, da yake a Gwarimpa suke ba wanni nisa,  duk yadda Al'ada su ya tanadar haka su kayi, nide ina dakina da Ashiya da ya'ya na.

Can wajen sha biyu duk an warwatse ya shigo gidan shi daya ba wanda ya rako shi,

Ina samar khimar kiran wayar sa ya shigo wayata, harda bazan amsa ba, sai na tuna abinda Ummah tace, nayi picking Call, amsawa nayi da toh, ina fadin haka na fito na nufa big parlor idan yace nazo na same su zaune, sallama nayi kafin na zauna nima..

Magana yakeyi amma sam ni hankalina ba ya gun, saida na ji yace Aisha ga Farida nan, ki dauke ta a matsayin Kanwa, kuma abokiyar zaman. Farida ga Aisha nan ki dauke ta a matsayin yaya kuma abokiyar zama, dafatan zaku hade kanku.

Na amsa da in shaa Allah, Allah ya bamu zama lafiya da hakurin zama da juna.

Masha Allah Aisha, zan so na san kwana nawa zaki bamu? Mujaheed yayi maganar yana kallona

Nace wata daya yayi idan beyi ba sai na kara nayi maganar ina murmushi mai wiyar fassara.

Cike da mamaki yake kallona, can yace mai Aisha take nufi da koh wata biyu ne? So take ta nuna ma Farida bata damu dani ba kuma bata kishina? Yayi maganar cikin zuciyar sa, kafin yace sati biyu dai kamar yadda aka tsara.

Shiru nayi ina mamakin ashe dai abinda Ashiya ta fada zai yi aiki? Dariya nayi cikin raina kafin nace to Amarya a kula da mijina  na barku lafiya, ina fadin haka na mike na bar wajen, ina nufa dakina na saka lock, na fashe da kuka mai cin rai, nafi karfin minti goma ina abu daya tsabar kishi da bakin ciki..

Some Months Later.

Muna zaune lafiya lau da Farida, bame shiga harkan kowa, saide ya saka mana dole cin abinci tare.

Na murmure abina kamar banda wata damuwa, bacin ina cike da damuwa kulum sai naga doctor sabida ciwona, duk abinda akace ina kiyayewa dan samu lafiya mai daurewa.

Yau gidan Ashiya na nufa, naje dauko su Abbah, tunda in weekends can nake kaisu sabida lectures na.

Uwargida kuma uwa ga Abbah da Ummi, kece haka kika yi lukub dake? Gaskiya kin birgeni da kike daukar wanka yanzu kike gyara jikin ki Aisha.

Ashiya kenan mai abin dariya, ni ma kosa ki hayhu ranan akwai shagali.

In shaa Allah Aisha saura kiriss na sauka.

Toh bara na koma gida, kinsa yau nice da girki gashi yau zai dawo daga Lagos.

Kisha wando ki da half top, kuma ki gyra Gashi yadda zai rude da kyau Ashiya tayi magana tana murmushi, nima murmushi nayi kafin nace to zanyi yadda kika ce amma kinsa halin sa, sai ya hanaka yin abin gabanka.

Aisha ai abinda ake so kenan, waccen karan tasan da cewa ba wai baya sonki ya aure ki ba.

Dariya nayi kafin nace toh shikenan yar'uwa zanyi yadda kika ce.

10mins yakai mu gida, living room na same ta tare da yar'uwa ta, suna ta yare, gaida su nayi kafin na wuce dakina.

Saida nayi masu wanka kafin nima nayi na fito, bayan na shiriya su nima na shiriya cikin blue jeans and red half top, na gyara gashina na fito rike da ya'ya na zuwa living room na kuna masu Omar and Hannah a TV kafin na nufa big kitchen, na fara shirin daura abinci..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 11, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now