Ya Kura Mata Ido Yana mamakin karyar da ta yanko, yace " ai nayi zaton kema zakiyi dare tunda kusan kullum sai kinyi dare" ta girgiza Kai gami da dawowa kusa dashi ta zauna tana Shan kamkana tace " aah yau sai Alhamdulillah da wuri na dawo".

Ji yayi kamar ya juyo ya makure wuyanta ya Kuma tambayeta waye wannan katon da take tare dashi da wannan tsohon daren.
Kamar anyi masa allura ya Mike zumbir ya shige daki.
Bakin gadon ya zauna Yana maida ajiyar zuciya idanunsa sunyi jajir wani irin kunci ke shiga zuciyarsa.

Sosai yake kokarin ya dorama Kansa zargin mujaheeda, haushinta yake ji, idan har tana da gaskiya me zaisa tayi masa karya?.
  Wannan karyar da tayi masa ta Sanya ayar tambaya akanta.
Har suka zo kwanciya Taufiq Yana cikin damuwa, duk yadda mujaheeda taso ta ja shi da hira yaki sakin jiki, ko da ta tambaye Shi dalilin yin darensa daker ya sanar da ita an kwantar da Àlh Yusuf lamido a asibiti.
Sosai mujaheeda ta Sami damuwa da Jin hakan domin dai har cikin ranta take Jin kaunar surikinta tana jinsa aranta tamkar uban da ya haifeta.
  Dashi ta kwana acikin zuciyarta .tun safe kuwa tasa Masu aiki su dafa ma Alh Yusuf lamido irin abincin daya dace yaci tuwon alkama tasa suyi da miyar kubewa busasshiya wacce aka burge kaza aciki.
  Ta Lura kwarai da canjin yanayin Taufiq, Wanda batasan dalili ba, ta dai Lura ko yaya aka Kira wayarta idonsa na kanta Yana yi Mata wani irin kallo Wanda ta kasa fassara Shi.

    Ya rigata fita gidan Kuma Kai tsaye asibitin ya wuce, ita Kuma mujaheeda saida aka Gama abinci sannan ta dakko ta taho asibitin Wanda kafin ta Karasa saida ta shiga super market tayi siyayya sosai tun daga Kan kayan tea da drinks Amma fa duk na masu ciwon sugar, Kaya ta sayo sosai.

   Isarta asibitin ta tadda Taufiq tare da Haj saratu da Haj Bilkisu, kwata kwata Taufiq bai son Ko da hada Ido da mujaheeda haka zalika duk irin kayan data lofoma mahaifinsa KO kallonsu baiyi ba ballefa ya nuna jindadin sa ko godiya.
    Alh Yusuf lamido da Kansa ya nunama mujaheeda waje kusa dashi ta zauna.ta zauna tana gaidashi tare da nuna damuwarta da kaunarta zuwa gareshi.
   Shima cike da kauna yake amsa Mata tare da yi Mata godiyar hidimar data taho dashi.
   Ita dai Haj saratu idonta nakan yarta tana nazarin meke faruwa tsakaninsa da mujaheeda domin tabbas tasan akwai matsala tunda su basa gajiya da Samun baraka atsakaninsu.

   Ko kafin Haj saratu ta gama zubama Alh Yusuf lamido abincin da mujaheeda tazo dashi Wanda da Kansa yace azuba masa yaci. Tuni Taufiq ya fice daga dakin daga Haj saratu har mujaheedan binshi sukayi da kallo.
  Mujaheeda tana tunanin meya faru ita dai tasan babu wani abu daya faru tsakaninsu Amma ta rasa dalilin da yasa tun jiya Taufiq ya canja Mata, KO yanzu har ta zo asibitin har zuwa yanzu daya fita baiyi Mata magana ba .
   Haka mujaheeda ta cigaba da Zama a asibitin har tsawon wani lokaci kafin tayi sallama dasu adalilin son ta leka office .
  Bayan tafiyarta ne Haj Bilkisu ta dubi Haj saratu tace " umma kina tunanin abinda nake tunani kuwa?" Tace tana kallonta " na mene?" Tace " tamkar tsakanin Taufiq da matarsa akwai matsala, kwata kwata tun zuwanta Taufiq bai karaesamun wani sukuni ba tamkar Yana Kan Kaya , baison Zama inda take".
     Haj saratu tace " nima na fuskanci hakan, to matsala Kuma tsakanin Taufiq da mujaheeda ai idan da sabo yakamata asaba".
  Ahankali cikin muryar ciwo Alh Yusuf lamido yace " Ku Kuma gasa Ido da ràshin son fadan alheri ba" Haj saratu tace " haba Alh ya zakace haka kullum alheri nake nufinsu dashi ".
  Yace " to in dai hakane don Allah ku dinga yi musu fatan arziki, da Kuma addua ta gari". Gaba dayansu shuru sukayi.

      A office mujaheeda aikin kawai take amma tunaninta na ga irin kallon da Taufiq yake Mata Wanda ta rasa gane wane irin kallone , da Kuma irin canjawar da yayi , aiya tunaninta dai bata tuna komai ba da akayi Wanda zai canjama Taufiq yanayi.Alh jibrin ya shigo da takardu ahannu yaja kujerar gabanta ya zauna Yana kallonta yace " GA takardun da mukayi dake jiya cewar Zan kawo Miki yau, Amma ya akayi Baki shigo office din da wuri ba yau ".
   Tadan gyara zamanta tace " eh , surikina aka kwantar baida lafiya sai da na Gama da asibitin sannan na wuto office ".
  Yace " Ayya , Allah ya bashi lafiya" ta amsa da amin.sannan ta dawo da kallonta Kansa tace " duka file dinne" yace " eh komai na ciki duk records din suna ciki sai ki tsaya kibi ahankali ki gane " tace " to ba laifi". Daganan ya tura Mata files din gabanta sannan ya tashi ya fita ransa abace.
   Alh jibrin Yana Shia office dinsa ya fada Kan kujera ya zauna Yana aje numfashin bacin rai, yace a fili , yarinyar nan tabbas tana son wuce gona da iri , tana Kuma son dakkoma kanta dala ba gammo , ta yaya take tunanin zata iya bankado almundahanar da sama da fadin da yayi da kudin kamfani na tsawon shekarun daya kwashe Akan kujerar manajan kamfanin.
  Ya Kara sakin tsaki gami da buga hsnnunsa akan tebur, dai dai lokacin murtala yayi sallama ya shigo yaja kujera ya zauna Yana kallonsa yace , " ya ake ciki ne Ka kaimata files din ne".
Ya dago Yana kallonsa yace , " na kaimata aikin banza don dai babu abinda zata gani aciki" murtala yace " yarinyar nan ma fa ta cika yar rainin wayau".
  Alh jibrin yace " ni Zan gaya Maka haka, wai kasan jiya duk wañnan uban dadewar data sa mukayi a office har dare, wai sai Dana kama hanyar gida ta kirani awaya wai naxo na sameta a babban titi, haka fa na juya naje na sameta , kasan me Muka tattauna " ya girgiza Kai , yace " Aah" Alh jibrin yace " wai tana tambaya ta ko akwai wani acikin maaikata da nake zargin zasu iya sama da fadin kayan kamfani, " murtala yace " to sai kace Mata mene ?" " Me ko Zan ce Mata daya wuce ni Bana zargin kowa, ammafa yarinyar nan idan tace wai zata zauna ta bubbugo sirrinmu ne na rantse maka zatayi babban kuskure arayuwarta domin ni Zan iya yin koma meye domin ganin asirina ya rufu".
Murtala yace " kwarai kuwa , ina Kuma bayanka domin tonuwar asirinka nima tonuwar asirina ne"....
       DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM

NI MA MATARSA CE On viuen les histories. Descobreix ara