ALAKAR YARINTA

195 7 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

       Page7️⃣2️⃣&7️⃣3️⃣
                  👇
     🔚🔚🔚🔚🔚🔚

  "Tun lokacin da na farka daga bacci da ya sace ni sai na ga har ƙarfe huɗu ta yi  ƴar uwata da muke tare tana sallar nafila abu ɗaya ne ya ɗarsu a zuciyata shin mai yasa yaron nan har yanzu bai farka ya nemi nono ba? Da sauri na tashi zaune na leƙa gadonsa abin da na fara gani bargon da aka rufeshi da shi a gefe guda a ajiye na san dai ko da zai iya ture bargon bai fi a ce ya ɗan janyeshi ba amma  sai na ga bargon kwacakwam kamar dai wani ne ya ɗauke a jiye, ban gama mamaki ba sai na ga yaron kamar wanda aka motsishi ya zama ɗan ƙarami amma sai na  tuna ana cewa jarirai ana haifarsu da ƙiba amma suna hucewa wato suna sacewa su zama ƙanana.Cikin sauri na ɗakko yaron amma dai sai na ga ramar tasa ta wuce a ce ya yi ƙanƙanta haka lokaci guda, tsaf na sauke idanuna a kan gabaɗaya ilahirin jikin yaron sai na ga kwata-kwata ba ɗana bane dan lokaci gida na gane hakan, hannunsa na kama na duba yatsunsa dan dama na san da yatsu shida na haifi ɗana amma sai na samu shi wannan yatsu biyar ne da shi, sai kuma zoben da ke yatsan tsakiya an mayar da shi babban yatsa.Kafin in gama mamakin nan sai kawai na lura ma ashe jaririn baya numfashi, na jijjigashi amma a banza dan ya mutu.

   Haka na shiga kuka amma ni kuka biyu nake kukan mutuwar yaron duk da ba nawa bane sai kuma kukan canja min ɗa da aka yi, haka muka haɗu da ƴar uwata muka sha kukan mu kafin a sanar da mahaifin yaron ni kaɗai na san cewa ba ɗana bane dan babu wanda ya kawo waji abu kuma har yau babu wanda na faɗawa ko da kuwa mahaifinsa, sanin da na yi ba ɗana bane ya mutu hakan ne ya sanya nake ajiye masa kaya tun na jarirai har zuwa girmansa dan na san wata rana zan ganshi ina jin haka a jikina" Momma ta faɗa tana sakin kuka a hankali.

"Babu ko tantama Hizbu ba ɗana bane ɗanki ne"Cewar Umma Sadiya tana share nata hawayen dan sai ta ji tausayin Momma sosai saboda ta yi haƙuri da juriya ba n akaɗan ba duk da cewar za ta iya tada hankalinta a asibitin har sai an nemo mata ɗanta amma ta daure lallai hakan ba ƙaramin haƙuri bane.


  Hizbu da zuwa lokacin ya gama jiƙewa da hawaye idanunsa kafe a kan Momma yana jin yadda ƙaunarta ke huda jini da jijiyarsa, ga wani tausayinta da ya mamaye masa zuciya lokaci guda lallai ba kowa bane zai iya abin da Momma ta yi.A hankali ya taso daga inda yake zaune ya nufota ya zauna a gabanta ya sanya hannu ya share mata yawayenta, itam hannunta ta sanya ta shiga share masa nasa hawayen tana hango ƙaunarta tsantsa a cikin idanunsa haɗe da tausayinta, wani daɗi na ratsata ga ta ga ɗanta jininta abin alfahrinta.

"Ki daina kuka komai da ya faru nufin Allah ne Allah ne ya tsara cewa ba a hannunki zan tashi ba dan haka ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddara" Hizbu ya faɗa yana kallon mahaifiyarsa yana hango soyayyarsa a cikin idanunta yana iya hango farinciki a tatare da ita tabbas uwa -uwa ce" Babu komai Hizbu nah ina fatan Allah ya maka albarka, ya sakawa waɗanda suka raineka suka baka tarbiya da gidan aljanna tabbas bani da bakin gode musu" Momma ta faɗa tana shafa fuskarsa.Hajiya Hauwa kai kawai ta sunkuyar tana jin wani nauyi da tausayin Momma da Hizbu na shiga haƙƙinsu da ta yi, a gefe ɗaya tusayin Umma Sadiya da Baba na shiga sashen zuciyarta, ga wani nauyin mai gidanta da ta hango shi ma yana share hawaye shin ita ina za ta kai wannan zunubin idan mutanen nan ba su yafe mata ba bata taɓa jin ta yi nadama ba sai yau tabbas ta yi dana sani a kan abin da ta aikata, musamaman na cutar da rayuwar Iftihal da ta yi babu arabi ba boko sannan  uwa uba lalata rayuwarta da ta yi na bin maza.Wannan kaɗai idan ba a yafe mata ba ya isheta ta shiga wuta domin Allah ba ya gafarta laifin wani a kan wani.

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now