ALAKAR YARINTA

47 3 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

           Page 4️⃣8️⃣&4️⃣9️⃣

     *HIZBULLAH*

     Tun da ya rufe ɗakin nan bai buɗe ba, har sai da aka kira sallar magriba da yake akwai masallaci daga can tsallaken gidan da suke.Duk da bai jin ƙarfin jiki da na zuciyarsa a haka ya daure ya tashi daga kwanciyar da ya yi alwala ya yi ya buɗe ɗakin ya fito, hakan ya yi dai dai da fitowar Abulkairi daga nashi ɗakin amma Hizbu na ganinsa ya haɗe rai tare da ɗauke kai yana jin Abulkairin na masa magana amma ya yi tamkar ma bai jinsa, har suka je masallacin suka dawo ɗaya a gaba ɗaya a baya ko jerawa Hizbu bai bari sun yi ba dan shi yanzu gabaɗaya zuciyarsa ta ɗauki laifi ta ɗorawa Abulkairi dan shi ne ummul aba'isin rashin gananwarsa da Ridallah da ace ya barsa ya bita da yanzu wani batun ake ba wannan ba.

   Ko da suka dawo ma ɗakinsa ya shiga ya banko ƙofar shi na Abulkairin sai ya ƙyaleshi domin ya lura yana cikin damuwa da ɓacin rai gwara ya rabu dashi idan ya sakko ya gama jimamin sa sasanta kan su.Yana shigowa ɗakin ma ya zube a kan kujera yana jin gabaɗaya duniyar ta masa ƙunci da zafi, ashe damm so har ya kai haka? Yana hana sukuni da walwala haka har ya sanya ka ji ka rasa nutsuwar ruhi da zuciya a lokaci guda, lallai sai yau ya ƙara sanin menene soyayya koma dai ya ce ƙauna ta gaskiya dan shi dai yau ya tabbatar a da soyayya yarinta yake yiwa Ridallah yanzu ne yake mata ainihin so duk da dai ya san ALAƘAR TARINTAR ce ta ginu tun daga soyayyar yarinya ta girma a zuciyarsa har ta kawo yanzu, tozalin da ya yi da ita shi ne babban abin da ya tada masa mikin son ta.

   Tashi ya yi a sanyaye dan ba ya jin ƙarfin jikinsa ruwa mai sanyi ya ɗakko ya ɗaga gorar bai sauke ba sai da ya shanye tas dan so yake ya ji ɗa sauƙi-sauƙi  a zuciyarsa ko da acw zafin da yake ji bai fita duka ba, amma yana gama shanye ruwa sai ya ji inda ruwan ya bi da ban inda zafin da zuciyarsa ke masa ma da ban.Dafe gefen zuciyarsa ya yi yana ambaton Innalilllahi wa inna ilaihir raji'un, har ya koma ya zauna yana ƙoƙarin kwantawa ko mai ya tuna sai ya tashi da hanzari wannan flower da ɗankunnen da Ridallah ta bashi tun lokacin suna cike da shaƙuwa, ɗakkowa ya yi yana tsaya yana ƙare musu kallo tamkar a yau ya fara arba da su, yana kallonsu maganganun da ta masa a ranar da ta bashi kowanne suka shiga masa amsa kuwwa a cikin kunnensa, damƙesu ya yi a hannunsa har sai da gabaɗaya jijiyoyin hannunsa suka bayyana raɗo-raɗo.

"Har kin manta da Ya Hizbu ɗinki ne? Kenan nisantar da muka yi har ya sa kin goge shafukana a tarihin rayuwarki, wanda ni kuma a kullum sabon shafi nake buɗewa na ajiye ƙaunarki wacce nake riritawa a ciki, ashe har kin manta dani yau kika ganni kika ce baki sanni ba?" Shi kaɗai ke maganganun nan a fili idanunsa a rufe ruf wasu zafafan hawaye nakwaranyo masa yana mamakin kan sa dan bai taɓa zaton yana da rauni ba sai a kan soyayya, soyayya ce kaɗai rauninsa ita ta bayyana rauninsa da ace da yadda zai yi tabbas da ba zai bar hakan ya faru ba domin shi namiji ne ya kamata a ce ya danne zuciyarsa bai bari soyayya ta bayyana rauninsa ba amma inaa...

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now