ALAKAR YARINTA

57 3 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

     Page 5️⃣4️⃣&5️⃣5️⃣

"Ruƙayya Sunusi ashe rai kan ga rai" Shugabar ta ambaci sunan Afrah cike da farinciki.

"Na'am Aisha Abubakar" Afrah ta ce  hankalinta har lokacin a kan Ridallah.

"Ku zazzauna mana ga wuri" Shubagar ta faɗa tana nuna musu  kujeru.

  Gabaɗaya suka zazzauna amma Baba Habiba har lokacin cike take da tashin hankali saboda ta san yau ba makawa asirinta zai tonu tun da har ga mahaifiyar Ridalla, kenan dama tana raye ba mutuwa ta yi ba kamar yadda ta zata a lokacin da ta tsinci Ridallah.Ta faɗi hakan a cikin zuciyarta.

"Wato Hajiya tun da an gama yiwa yaron register za mu iya tafiya?" Baba Habiba ta faɗa cike da rashin gaskiya ƙarara a tattare da ita.

"A'a ku dakata tukuna ai sai mun haɗa alaƙa da yarinyar nan taki baki ga yadda suke kama da ƙawata ba ai sai an ji ko suna da haɗi.Shugabar ta faɗa tana washe baki, gaban Baba Habiba ne ya faɗi.

"Waya ta ɗaga ta kira sakatariyarta ta mata umarni ta kira mata wata mata ɗaya daga cikin masu kula da yaran, tana zuwa ta mata umarni da ta karɓi yaron nan na hannun Mama Rahma wanda aka sanyawa suna Aliyu haka aka tafi dashi mai unguwa ma da ƙaninsa suka musu sallama suka bar su Ridallah a nan.

   "Aisha dama maganar da ta kawo mu a kan wannan yarinyar ne, ɗiyata ce to tun da gashi ma Allah ya sa ke ce shugabar gidan nan komai na san zai zo da sauƙi" Cewar Ruƙayya tana nuna Ridallah. Gaban Ridallah ne ya yi mugun faɗuwa, Baba Habiba kuma ta sanya hannu ta dafe ƙirjinta sauran mutanen wurin kuma sai suka shiga kallon-kallo.

"Ikon Allah daga zuwa ko hutawa baki yi ba ƙawata, kuma ta yaya yarinyar da yau ta taɓa zuwa gidan nan amma kika zo magana a kanta kuma ma ga mahaifiyarta a wurin, su ma yaro suka kawo fa"Cewar shugaba.

Kawai dai ta ga mai kama da ita ne amma tana magana ne fa a kan Amina, yarinyar da kika ce kamar daga ƙasar larabawa aka kawota ko baki shaidani ba" Abba ya faɗa yana kallon shugabar.

"Ikon Allah hankali shi ne gani in ji hausawa, wallahi ban kula da kai ba Abba ka san hankalina a kan ƙawata ban ganka ba, kana nufin Iftihal ita ce yarinyar da take magana akai taɓɗi lallai dan dai tana jaririya na na ganta shi sa ban yi gaggawar shaidata ba sai yanzu na gane tsananin kamar  da kuke da Amina" Cewer shugaba tana kallon Ruƙayyar, wani yawu Baba Habiba ta haɗiye saboda jin wata yarinyar mai kama da matar nan.

  Tsaye Ruƙayyar ta yi jin wai yarinyar nan da ta gani ba ɗiyarta ba ce ita duk tunaninta ko yarinyar ce suka zo gidan marayun tun da ta ga gabaɗaya dai bata fi sa'ar shekarun da aka faɗa ta haihu ba sannan ita abin da ya sa ma bata kawo komai ba da aka ce ga mahaifiyarta ta ɗauka uwar goyon ƴartata ce wacce ta ɗauketa amma idan aka ce waccan tana wani wuri to wannan kuma wacece?Ta yiwa kan ta wannan tamabayar.


"Aisha dan Allah ki taimaka ki yi komai cikin gaggawa saboda a matse nakenda son ganin ƴata wallahi ban taɓa ganinta ba wannan mutumin ne ya tsinceta" Ruƙayya ta faɗa tana muna Abba.

"Amma ta yaya aka yi har kika rasa ɗiyarki ta cikinki tana jaririya har aka kawota gidan marayu kuma m sama da shekaru masu yawa?"

"Labari ne mai tsawo" Ta bata amsa waau hawaye na zubowa daga idanunta.

"Hajiya ki taimaka muna so mu san inda yarinyar take ne a yau ma inda hali muna son ganinta saboda ta haifeta ne a cikin yanayi na hauka" Malam Idi ya faɗa.

"Subhanallahi hauka kuma?" Shugabar ta tambaya cikin tashin hankali.

"Eh mana"Abba direba ya bata amsa.

"Ikon Allah babu yadda ubangiji ba ya yi da bawansa, insha Allah yanzu zan kira muku matar a waya a sanar da ita kafin mu je ku ganta"

"Kar ki sanar da ita kawai gwara mu je kin san sun saba da yarinyar kar ta ji babu daɗi gwara dai kawai ta gan
mu"Cewar Malama Zainab.

"To ba damuwa" Cewar Shugaba

"Dan Allah zo nan"Ruƙayya ta faɗa tana miƙawa Ridallah hannu, shiru Ridallah ɗin ta yi sai kuma ta maida kallonta ga Baba Habiba, kai Baba Habiba ta gyaɗa mata alamar ta je, a hankali Ridallah ta tashi ta nufi wurin Ruƙayya da ke ta kallonta gani take tamkar fuskarta ce a jikin yarinyar ba dan an faɗa mata cewa ƴarta na wani waje ba da babu dalilin da zai sanya ta ce ba wannan bace ƴarta.Tana ƙarasowa Ruƙayya ta sanya hannu ta riƙota sai kawai ta rungumera kawai ji take sai ta rumgumi yarinyar ko ta daina jin abin da take ji, tana rungumeta ta fara zubar da wasu hawaye masu ɗankaren zafi dan ji take kamar ta rungumi ƴarta ta cikinta tamkar jininta ta runguma.

   A ɓangaren Ridallah ma ta tsinci kan ta a halin da Ruƙayyar ta tsinci kanta itama bata san dalilin da yasa ta ji wani daɗi da sanyi ba wanda bata taɓa jin makamancinsa ba idan ta raɓi wani, lokaci guda kuma ta ji hawaye na bin kumatunra hawayen da bata san dalilinsu ba.

"Baku ganku ba kamar ƴa da uwa" Shugabar ta faɗa tana murmushi.


"Wallahi ni ma hakan na  gani" Malama Zainab ta faɗa tana kallonsu dan babu wanda ba zai ce Ridallah ba ɗiyar Ruƙayya ba ce.

"Ni ma hakan na ji a cikin raina tamkar ɗiyar dana haifa"Ruƙayya ta faɗa tana juyo fuskar Ridallah gabanta suka fuskanci juna.

"Ni ma hakan ne ya ziyarceni wani yananyi marar misaltuwa, kamar dai muna da wani haɗi" Ridallah ta faɗi hakan jin ta kasa riƙe hakan a zuciyarta.Kowa kallonsu yake abin sha'awa kuma abin tausayi.Su duka hawayen suke har yanzu Ruƙauua ce ta sanya hannu take sharewa Ridallah hawayen, itama Ridallah hannu t sanya tana sharewa Ruƙayyar.


  "Duk ku dakata yau dai zan buɗe rufaffen sirrin da na daɗe ina boyewa wanda babu wanda ya sani daga ni sai Allah, yau zan warware ƙullin da babu wanda ya san da shi sai ni sai Allah, a baya ban yi niyyar tonawa ba amma yanzu an zo lokacin da ba zan iya cigaba da boyewa ba doɓin idan na cigaba da hakan Allah ba zai barni ba!  Tabbas yau kowa zai san wacece Ridallah!!!"Baba Habiba da ta tashi tsaye ta faɗa tana share hawayen da ke ta kwaranya daga idanunta ko tsayawa basa yi, dan ba a son ranta ba za ta faɗa...




   MMN AFRAH😍🥰😘

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now