ALAKAR YARINTA

71 3 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

       
Page3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣


   "Ridallah ni za ki mara?" Hizbu ya ce cikin mamaki yana ƙanƙance idanu, dan shi ganin abin yake kamar almara, yana gani wai Ridallah ɗinsa ce ke nuna bata san shi ba har tana ɗaga hannu za ta mareshi taɓɗi lallai akwai lauje cikin naɗi kenan dama ba son shi take ba? Kenan dama so ne na yarinta yanzu ta girma idanunta sun buɗe ta manta da shi ta barshi shi yana fama da tunaninta kullum cikin kallon ɗankunne da flower da ta bashi yake ba ya son ko kaɗan ya manta da ita ko da na second ɗaya ne dan yana ganin ya ci amana ya ci amanar ƙaunar da take masa da ma wacce yake mata baki ɗaya.

  Kallon shi ta yi a raine tare da buga wani uban tsaki, ta fido wayarta da ke ta faman ƙara daga kiran ya katse sai wani ya shigo, tana dubawa ta ga Alhajin nan ranta ya ƙara ɓaci dan tana ganin duk shi ya jaza mata wannan bala'in da sun wucewarsu Hotel da duk haka bata faru ba yanzu gashi nan ya sanya wannan mai kama da mahaukatan yana kiranta da wani suna da bata ma taɓa jin mai irinsa ba.

"Ina jinka" Shi ne kawai abin da ta ce.

"Ya na jiki shiru ko dama baki taho ba?" Alhajin ya tambayeta daga ɗaya ɓangaren.

"Ka taho wajen hanyar fita ina wurin wani ya hanani tafiya" Ta ce dan bayan ta ɗaga wayar ma ta yi ƙoƙarin tafiya amma Hizbu ya janye Abulkairi daga gabansa ya je ya sha gabanta zai cigaba da jefa mata tambayoyi marar kai da ƙafafu.Tana kashe wayar ta kalli Hizbu cikin takaici ta ce

"Za ka gane shayi ruwa ne dan sai nasa an kulleka an koya maka karatun da baka da ilimi a kan sa  tun da baka da hankali" Ta ce tana ɗauke idanunta daga kallonsa.

"Shikenan Rida na ji baki sanni ba kamar yadda kika nuna amma inaso ki faɗa min ina Baba take shin tana raye? a nan ƙasar take ko tana Nigeri'a?" Wani kallon baka da hankali ta masa ta ɗauke kai dai dai nan Alhajin ya ƙaraso dan ta tura masa hotonta yana hangota ya ganeta.

    Babban mutum ne dan da ganinsa ma ya haifi Iftihal ɗin sanya yake da wandon jeans da riga  mai dogon hannu sai wani uban ƙaton tunbinsa tari guda yana reto kana ganinsa kasan kuɗi sun sami wuri sun tare.

"Baby Iftee menene hakan me ke faruwaa ne?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta dan yana ganinta ya ji wata kasala ta baibayeshi, ganin irin shigar da ta yi mai bayyana surorin jikinta.

"Kalli wannan baƙauyen ne yake kirana da wani suna ya kafe dole ya sanni bayan ni ko a mafarki ban taɓa ganin ko da mai kama da shi ba" Ta kai ƙarshen maganar tana wani karkaɗa jiki dan Alhajin ya ji daɗin ɗaukan mataki.

  Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe zuciyar Alhajin lokaci guda ya kalli Hizbu da ya babbake a gaban Iftihal ya ce

"Malam halan daga turu ka fito ko? Ka taɓa ganin yadda ake niƙe mutum a maidashi dambun nama? To akan wannan yarinyar zan sanya a dandaƙa ka har sai cikinka ya haɗe da bayanka, dan haka ka fita harkarta ko a mafarki babu kai babu ita" Yana kai ƙarshen maganar yasa hannu ya hankaɗa Hizbu gefe guda sannan ya kama hannun Iftihal suka juya suka fara tafiya dan maimakon su shiga ciki hanyar fita suka nufa, ya maida hankalinsa kwacakwam kan ta ita kwa sai wani rausaya jiki take dan ƙara ɗauke masa hankali dan tana so ta samu kuɗaɗe masu yawa daga wurinsa dan Auntynta ta faɗa mata cewa ta tabbatar ta yi iya yinta dan ta wanki gara.

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now