ALAKAR YARINTA

56 2 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

         Page5️⃣0️⃣&5️⃣1️⃣

    
    *RIDALLAH*

  Misalin ƙarfe shida na yamma ne bayan ta kammala aikinta sai ta shiga wanka, dan har yanzu ba su cinye hutun nasu ba, ɗaure take da zani sai ƙaramin hijabi da ta ɗora a kan zanin.Tun da ta fito ra ƙarasa wurin murhu domin iza wutar miyar daren da take ta tafasa, so take sai ta sanya kaya ta zo ta kaɗa miyar bayan ta tura itacen tana ƙoƙari fifitawa sai ta ga wutar ta kama da yake ana iska.Ƙoƙarin juyawa take domin shiga ɗaki sai take jiyo kukan yaro a zauren gidan nasu da yake su Baba basa nan su je gidan gaisuwa nan bayan layin da aka yi rashi, kuma dai ta san ƙofar a rufe take amma dai bata sa sakata ba, jin kukan yaron na tsawaita yasa ta taho da ɗan sauri tana zuwa ta ga ƙofar gidan a buɗe shi kuma yaron jingine da jikin ƙofar yana kuka ƙaramin yaro ne mai kimanin shekara uku wani iri Ridallah ta ji a ranta tausayin yaron ne ya kamata ganin ko takalmi babu a ƙafarsa fuskar gabaɗaya ta jiƙe da hawaye.

   Ƙofar gidan ta fita ko za ta ga wani amma babu kowa sai wasu samari a can tsallake da ke zaune kan benci wasu na hira wasu na alwala, har ta gama waige- amma babu wanda ta gani cikin sauri ta dawo ta ɗauki yaron ta fito wajen da shi har lokacin kuka yake tun ƙarfinsa sai jijjigashi take a haka ta nufi wajen samarin tana zuwa ta fara magana.

"Assalamu alaikum, dan Allah kun ga wanda ya taho da yaron nan ko kuma kun ga shigarshi gidanmu? Ta haɗa sallamar da tambayar dan ko sallamar bata jira sun amsa dan a rikice take kukan yaron duk ya gigita ta ya sanya zuciyarta yin rauni.

"Wa alaikumus salam, gaskiya dai babu wanda muka gani hasalima bamu ga yaron nan ba sai yanzu a hannunki"Ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana kallon yaron da ke tsallara ihu har shiɗewa yake sai kiram Umma yake.

"Ya ilahi ya zanyi da yaron nan"

"A ina kika ganshi?"

"Wallahi fitowata daga wanka kenan na jiyo kukansa  a zaure gashi babu kowa a gidan sai ni kaɗai shi ne fa na leƙo na ganshi yana kuka"

"Wataƙila ɓata ya yi"Wani da ke alwala yana ƙoƙarin shafar kai ya faɗa.

"Wayyo Allah na ya zanyi da shi gashi sai kuka yake yi yaƙi shiru "

"Kawai kije ki bashi abinci ko yana jin yunwa sai ki goyeshi idan ƴan gidan sun dawo sai ku kaishi gidan mai unguwa"

"To shikenan nagode"Ta ce kamar za ta yi kuka ta juya ɗauke da yaron yana ta kuka da kiran Umma.

  Tana shiga gidan ta rasa mai za ta yi kawai sai ta ji hawaye na bin kumatunta saboda tausayin yaron, tana ganin ba abin da ya fi buƙata sama da mahaifiyarsa.Sauran abincin rana sa suka yi taliya da miya ta zubo masa da yake ba wani cika attaruhu suke yi ba dan haka miyar babu yaji, yana ganin abincin yake ɗaga hannu alamar yana so ya ci haka ta shiga bashi abincin amma bai fi uku ya karɓa ba ya daina karɓa ya sanya hannunsa yana ci sosai yake cika bakinsa da alam akwai yunwa a tare da shi, ruwa ta ɗakko masa bayan ya gama ci ta bashi ruwan dan da kansa ya ture kwanon da ya ƙoshi.Ɗaukansa ta yi suka tafi ɗaki dan zuwa lokacin ya yi shiru sai dai ajiyar zuciya da yake ta faman yi alamar kukan da ya yi, a kan katifa ta ajiyeshi ta sanya kaya dan ko mai bata samu damar shafawa dan gabaɗaya a ruɗe take bayan ta sanya kayan ta ɗakko zani ta goyashi dan so take ta yi alwala saboda har an kira sallar magriba, tana cikin wankin ƙafa su Mama Rahma suka shigo ɗauke d sallama, daker ta iya amsa musu su kuwa sa basu san abin da ke faruwa ba kowacce ta fara shirin zuwa ta gabatar da sallah.Mama Rahma ɗakint t shiga itam Baba Habiba hijabinta ta cire ta miƙa cikin ɗakinsu tana ƙoƙarin fitowa ita kuma Ridallah na ƙoƙarin shiga ɗakin aikuw idanun Baba Habiba suka a kan goyon yaron da ke goye a bayan Ridallah dan yaron har ya kwantar da kansa ya fara bacci baki sake Baba ke kallon yaron ita kuma Ridallah sai ta tsaya cak ta kasa tafiya.

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now