ALAKAR YARINTA

107 4 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

          Page9️⃣ &🔟


  Wata tsawa da Hajiya Hauwa ta dokawa Safiya ita ta dakatar da ita daga shirin dukan da take ƙoƙarin ta kaiwa Iftihal, wani tsoro ne ya ziyarci Safiya dan sai a lokacin ta ji a ranta cewa lallai da ta kaiwa Iftihal dukan to tabbas da ta yi babban kuskure, dan wataƙila kafin ta rasa aikin nata sai ta fara rasa ranta dan tsaf Hajiya Hauwa za ta mata dukan mutuwa akan Iftihal.

"Wace irin marar hankali ce ke in ban da jakanci da jahilci maimakon ki yi saurin tafiya ɗaukan mopa da ruwa ki zo ki goge wurin shi ne kika tsaya kina kallon Iftihal ɗin sai ka ce wanda ta yi wani abu, ko dan baku san darajar kuɗi ba saboda baku da su shi yasa za ki bar min capet da ruwan shayi a jiki sai ya dafe yaƙi fita" Aunty ta ce tana wani zazzare ido tana bala,i.

"Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Safiya ta ce tana ɗaukan kanukan ta nufi kicin domin ta ajiye su, ga wani zafi da raɗaɗi da fuskarta da ƙirjinta ke yi dan shayin akwai zafi amma saboda rashin imani na Hajiya Hauwa maimakon ta tausaya mata shi ne take mata faɗa bayan Iftihal ya kamata ta yiwa faɗan amma saboda sangarci da kuma ganin suna da kuɗi za su iya taka kowa ma hakan ya sa ta zamar da ƴarta ta sangartacciya.Sai da Safiya ta tsaya ta share ƙwallar da ta zubo mata tana da na sani akan aiki a ƙarƙashin Hajiya Hauwa da bata da mutunci ko kaɗan bare tausayi, bata koyi da sobar zamanta Hajiya Azima mata mai kima da darajanta ɗan adam pan aikinta tamkar ƴaƴanta haka ta ɗaukesu ba kyara ba tsangwama.

Tana ta saƙar zuci ta dawo falon ɗauke da mopa da burket da ta haɗo ruwa mai ɗauke da morning fresh, ta shiga goge wurin, lokacin Auntyn na lallashin Iftihal akan ta yi haƙuri za a haɗa mata wani tea ɗin marar zafi sosai marar madara da yawa.Wani haushi da takaici ne ya turnuƙe Safiya tana Allah wadaran naka ya lalace ace maimakon uwa ta zama turba na gina rayuwar ƴaƴanta akan hanya daidaitacciya mai ɓullewa wajen basu kyakkywar tarbiya amma shi ne ita Aunty ta zama mai bada gudunmuwa wajen taɓarɓarewar tarbiyar ƴarta, babu abin da yarinyar ta sanj sai sangarta.

"Dalla malama ki yi sauri ki gama ki haɗa mata wani tea ɗin"Cewar Auntyn cikin zafin rai.

"To Hajiya" Safiya ta amsa mata, bayan ta ɗakko freshner ta fesa a wurin saboda ƙarnin madarar sannan ta ɗauke kayan da ta yi amfani da su wajen gyara wurin, kicin ta koma ta ɗauki gishiri ta shafa a wurin da aka watsa mata shayin dan da alama ma kamar wurin zai tashi, bayan ta shafa sai kuma ta wanke hannunta ta sake haɗa shayin marar zafi sai dai yana da ɗan ɗumi sannan ta fito ta zo ta durƙusa ta miƙawa Iftihal ɗin, tun da ta ce da kan ta za ta sha.

  Ƙin karɓar shayin ma ta yi tana kallon tv, kamar ma ba ita ake baiwa shayin ba, Auntyn kwa tana kallo ko ta yiwa Iftihal ɗin magana.

"Ga shayin na sake haɗa miki"Safiya ta ce da ta fahimci bata da niyyyar karɓa.

  Banza ta yi da ita, can kuma a shelaƙe ta karɓa, kurɓa ɗaya ta yiwa shayin ta ɗaga ta watsar da shi, ta yi jifa da kofin ya tarwatse dan dai ma akan tiles ne ba akan capet ba.Safiya kai ta sunkuyar tana jin a ranta cewa lallai neman halal da wuya musamman a ƙarƙashin wanda ba su san kima da darajar ɗan adam ba.Hatta Hajiya Hauwa ranta ya matuƙar ɓaci da abin da Iftihal ɗin ta yi amma saboda bata so ta nuna mata hakan duk da cewa ita ce ta ɓata yarinuar gashi bata son kwaɓarta sai kawai ta danne zuciyarta ta ce.

ALAƘAR YARINTAWhere stories live. Discover now