ALAKAR YARINTA

63 1 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

        Page 5️⃣8️⃣&5️⃣9️⃣

   

_IFTIHAL_

 
   Mummy na fita a ɗakin Iftihal ta koma ta zauna a bakin gado tana jin wani takaici na ziyatar zuciyarta ji take tamkar ta fitar da su daga cikin zuciyarta ji take ina ma Aunty ba ita ce ta haifeta ba da tabbas abin ya zo mata da sauƙi, saboda ji take tamkar zuciyarta za ta buga saboda tsananin  zadi da ciwo a ce mahaifiyarka ce sanadin lalacewar rayuwarka ita ce ummul aba'isin jefa rayuwarka wata hanya marar kyau tabbas wannan ba ƙaramin abin baƙinciki bane kuma mugun tabo ne wana zai zauna har abada a zuciyarka zaman da ba zai taɓa ƙanƙaruwa ba!

   Tana rayawa a ranta cewa inama a ce kishiyar mahaifiyarta ce ta mata hakan da hajan ba zai dameta sosai ba domin ta san kishin wasu matan babu abin da ba ya sanya su duk da ita kishiyar mahaifiyarta ta lura tana da kyan hali da na zuciyar. Ita dai Amal tana gefe nan inda zaune ita ɗin ma duk abin duniya ya isheta lallai shirya ta Allah ce gashi dai a baya ko hasashen daina rayuwar da aka sanyasu a ciki basu taɓa yi ba amma kuma gashi rana ɗaya kuma lokaci guda sun ji komai yana neman ya zama tarihi a rai da zuciyarsu tabbas shiriya ce  Allah ya kawo musu ba tare da sun sanya cewa za su daina a kwana kusa ba.Ƙaran buɗe get da aka yi da kuma jin dirin motar Daddy shi ne ya sanya Iftihal miƙewa tsaye daga zaunen da take, itama Amal tsayen ta miƙe tana mai ƙarasowa inda Iftihal ɗin take ta dafa kafaɗarta ta ce.

"Yanzu idan mun tunkari Daddy da wannan maganar me kike so mu faɗa masa? Shin bakya tsoron wani abu ya faru?" Amal ta tambayeta tana kallonta da jajayen idanunta.

"Amal ya kamata mu tunkari matsalarmu kai tsaye ba tare da tsoro ko fargabar faruwar wani abu ba, ko ma mai zai faru sai dai ya faru amma a yau ɗin nan sai Daddy ya san duk abin da ke faruwa"

"To shikenan Allah taimakemu kar su ƙulla mana wata maƙarƙashiyar da makirci kin san girma da hankali da kuma tunaninmu ba ɗaya bane da nasu"

"Allah ya fisu sannan kuma Allah bai barin zalumci babu abin da ya gagareshi" Iftihal ɗin ta faɗi hakan tana sanya hannu ta share hawayeta tana jin ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa tun da ta ambaci Allah ta san kuma lallai zai shige mata gaba.Cikin sauri ta fito daga ɗakin Amal ta take mata baya, lokacin Daddyn har ya nufi part ɗinsa dan haka can suka nufa cikin sauri kamar ana tura su dan so suke kawai su aiwatar da ƙudirinsu tun kafin shaiɗan da shaiɗanin mutane su ci galaba a kan su duk da suna ganin hakan ba abu bane mai yiwuwa.

  A lokacin kuma ita Mummy tana can tana ta faman kiran wayar Hajiya Suwaida bayan ta yi ta kira ba a ɗauka ba dan lokacin ita ma tana cikin tsaka mai wuya dan mai gidan ta ya jefawa mai gadinsu tambaya dan haka hankalinta tashe yake domin matsawar mai  ya gadin ya faɗi gaskiya to kuwa tata ta ƙare.Bayan ta gaji da kiran wayar Hajiya Suwaida sai ta koma kiran wayar Hajiya Hauwa lokacin itama ta bar wayar a ƙasa tana caji ta hau sama sai Safiya a falon tana jinnwayar na ƙara da ta leƙa ta ga mai kiran ta taɓe baki dan bata jin za ta iya ɗaukan wayar ta kaiwa Aunty dan yanzu duk haushinsu take ji dan haka tana jin kiran na ta shigowa ba ƙaƙƙautawa amma ta murɗe kunneta ta cigaba da uzurin gabanta.Haka Mummy ta yi ta kiransu hankali a tashe domin su san abin yi amma babu wanda ta samu ya ɗaga wayar dan haka ta zauna daɓas tana jin mummunar faɗuwar gaba dan yadda ta ga idon yarinyar nan Iftihal wiƙi-wiƙi bata tunaninnakwai wani abu da zai taka mata birki wajen aiwatar da abin da ta yi niyya duk da dai tana tunanin kamar ba za ta iya aiwatarwar ba, tabbas tana ji a jikinta kamar dai dubunta ta kusa cika amma kwa in hakane tana cikin ɓuguwar matsala.

ALAƘAR YARINTATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang