ALAKAR YARINTA

59 3 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

                NA

      

           MMN AFRAH


   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

  Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba  Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

         Page5️⃣2️⃣&5️⃣3️⃣

   "Abba mu je daga ciki ayi magana nan ba wurin magana bane mutane na wucewa" Malam ya katse masa amsar da zai baiwa Afrah.

   Su duka suka juya Malama ta buɗe musu gidan suka shiga, gabaɗaya hankalin Afrah a tashe yake dan tana cike da tsoron kalmar da za ta fito daga bakin Direban dan bata son ya ce abin da ta haifa ya salwanta.Suna shiga ɗakin Malam suka shiga shi kuma direban ta ƙofar zaure ya shiga bayan sun zauna ya fara magana.

   "Shekarun baya da suka wuce kimanin shekaru sha uku zuwa sha huɗu, wata rana na yi lodin ƙauyen Gujungu na kai ranar ana wahalar samun fasinja dan haka gajiya na yi na taho babu kowa a motar sai ni kaɗai.Ina cikin tafiya na samu fasinja  guda ɗaya wani bafulatani dan haka a wata ruga da ke hanyar na tsaya na saukeshi, bayan ya sauka na ɗan yu tafiya kaɗan sai na ji ina son na kama ruwa dan haka na fito da jarkar da nake zuba ruwa saboda irin hakan.Bayan na yi fitsarin na kama ruwa ina cikin rufe jarkar sai kawai na jiyo kukan jariri a take gabana ya shiga bugun uku-uku amma hakan na daure na bi kukan dan ganin mai ke faruwa duk da fargabar da ke cikin raina, ina zuwa kan wurin kamar wata bola ce inda ake tara ƙazanta dan ya zama taki, mace na gani kwance a cikin jini kana ganinta ka san mahaukaciya ce sai kuma jaririya tana gefe tana ta kuka"

"Ina take dan Allah?"  Afrah ta tambaya hawaye na zuba a idanunta.

"Ki barshi ya ƙarasa labarin ai sannu- sannu bata hana zuwa"Malam ya faɗa dan baya so a katse Abba.

"Ka san dole za ta buƙaci ji saboda ruɗanin da take ciki"Malama Zainab ta faɗa cikin tausayawa.

"Cigaba Abba saboda mu san abin yi ka ga tafiya ce a gabanmu"Cewar Malam.

"Wayata da ke cikin aljihu na ɗakko na fara ɗaukansu a hoto saboda shaida, sannan na ɗauki yarinyar  jikinta duk ƙasa ta haɗe da jinin haihuwa rumgumeta amma ina duba uwar na ga bata numfashi hakan ya tabbatar min ta mutu, tafiya na yi in sanya jaririyar a mota dan in dawo in ɗauki uwar idan zan iya saboda babu kowa ko motoci basa gilmawa kamar an yi ruwa an ɗauke.Bayan na saka jaririyar a mota na dawo amma ko sama ko ƙasa na rasa matar nan kuma ko sawun mutum babu wanda zance ko ɗaukanta aka yi itama babu nata sawun tsoro al'ajabi ne suka mamaye zuciyata, dan a take na fara tunanin aljannu ne ba mutane bane, da sauri na dawo motar dan tunanina zan tarar sun ɗauke yarinyar ma amma sai na tarar tana nan ta sanya yatsa a baki tsuru na mata da ido ina jin tsoro mai tsanani har na ɗakkota zan ajiyeta na gudu sai tausayinta ya kamani saboda na yi tunanin aljannun uwar ne suka ɗauketa dan basa so a taimaketa tausayin yarinyar yasa na shiga na tada motar na bar  wajen a 360.

  sai bayan na fara tafiya na fara tunanin inda zani da wannan jaririya domin na san ko karan hauka ne ya cijeni ba zan doshi gidana ba da jaririyar saboda  matata ko sama da ƙasa za ta haɗe ba za ta taɓa yarda cewa tsintar jaririyar na yi ba saboda mace ce mai kishin tsiya.Hakan ne yasa na nufi garin Gumel ban zame ko ina ba sai ofishin ƴan sanda bayan na musu bayani tare da nuna musu hoton da na ɗauka lokacin da na tarar da su yashe, sun ɗaukeni mun koma wurin da na tsincesu domin yin bincike tare da tabbatar da gaskiyata bayan sun tabbatar ina da gaskiya sai D.P.O  ya ce za a cigaba da bincike tare da cigiyar matar nan mahaukaciya haka ya ɗauki yarinyar ya kaiwa matarsa saboda tana goyon jariri lokacin a kan ta shayar da ita kafin a san abin yi amma taƙi a cewarta ba za ta shayar da ƴar da bata san asalinta kuma ma ƴar mahaukaciya haka ya siyawa yarinyar madarar jarirai ake bata domin ma ba ita ce ke kula da ita ba ƴar aikinta ce.Tsawon kwana uku ba a samu wani bayani ba an bi duk garuruwan kusa da kuma ƙauyuka amma ko mai kama da mahaukaciyar ba a gani ba, ni kwa kullum sai na je ofishin ƴan sandan nan daga ƙarshe dai gidan marayu aka kai yarinyar na cikin garin Gumel tare da ni aka kai yarinyar aka mata register da komai da komai aka barta a can"

"Yanzu hakan tana can gidan marayun?" Malam ya jefa masa tambaya dan daga Malama har Afrah kawai kuka suke.

"Gaskiya ba ta can, saboda tun washe garin ranar da na je domin ganin yarinyar na tarar da wasu mata sun zo ɗaukan jaririya kun san akwai wanda ke son ɗaukan yara marayu ko dan su taimakesu ko kuma idan basu taɓa haihuwa ba a gabana suka cike komai aka haɗasu da wanda zai je ganin mazauninsu domin tabbatar da cewa ba cutar da ita za su yi ba"

"A wane gari suke?"

"A garin, wallahi sunan garin ya kwanta min ka san shekarun da yawa"

"Wane suna aka sanya mata?"  Malam ya ƙara tambayarsa.

"Amina"

   Har lokacin Afrah kuka take saboda tausayin ƴarta tilo amma ta rasa duk wani gata da ya kamata ta samu a ranar haihuwarta, tabbas duk wanda ya haukatar da ita ya cuceta duk da ita bata ɗora laifi ko zargi a kan kowa ba.

"Yanzu dai ku tashi mu fara tafiya Gumel ɗin gidan marayun mu fara tabbatar da inda yarinyar take, saboda mu je Dutsen da ƙarfin gwiwa domin ko da mun je dole dai a dawo a nemi inda yarinyar take kuma dai Gumel tafi kusa da nan ɗin"

"To shikenan "Cewar Direban.

"Amma kuma kana ganin zasu yarda da mu ko kuwa sai mun je mun tafi da ƴan sandan da aka kai yarinyar tare da su?"

"Gaskiya ba wai lallai sai da su ba domin sun san da ni aka kai yarinyar na san komai kuma mai gidan marayun ma tana da kirki, yanzu in muka ce sai mun je da su sai sun ɓata mana lokaci sannan sai sun buƙaci a basu wani abun"

  "To shikenan mu yi yadda ka ce ɗin"Malam ɗin ya faɗa yana miƙewa tsaye su duka suka tashi, haka suka fito Malama ta kulle gidan suka shiga motar suka tafi.

   A ƙofar gidan marayun suka tsaya direban ya yi horn aka buɗe musu get suka shiga cikin harabar gidan marayun ya faka motar suka fito suna ƙarewa gidan marayun kallo, ba ƙaramin gida bane har da ajijuwa a cikin gidan da alama makaranta ce da ake musu karatu, sai wurin yin ball da wurin wasanni, lokacin ma duk wasu yaran na cikin ajijuwa ana musu karatu sai dai ƙanana wanda basu isa makaranta ba suna ta wasan su.

  Sun ɗan yi tafiya kaɗan suna ta wuce yara  da kuma wasu mata wasu na shanya kayan wanki kowa dai yana abin da ke gabansa da alama su ne masu kula da kan su.Ofishin shugabar suka nufa domin shi Abba ya sani, suna zuwa sai suka samu ofishin ma a buɗe dan haka kawai suka doshi ciki da sallama kafin a amsa  suka tsinkayi wata murya tana cewa

  "Yanzu ki ce baki san Ruƙayya Afrah ba wacce ke garin Dutse?"

"Wallahi ban santa ba?"

"Ikon Allah wallahi kamar an tsaga kara ke da ita yadda kika gankin nan haka take lokacin muna secondry school, tunanina ma ke ɗiyarta ce"

"Kin ga Mamana nan" Matashiyar yarinyar ta ce tana nuna wata mata.Haba wa tuni cikin matar nan da aka nuna ya ɗuri ruwa a take wani gumi ya fara tsatstsafo mata.

  Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarci Afrah jin ana ambaton sunanta da sunan garinsu da kuma mai kama da ita sak to ko dai ita ce ƴar da suka zo nema.

  "Assalamu alaikum" Malam ya buɗe murya ya ƙarw sallama.

Gabaɗaya suka juyo ƴan cikin office ɗin dan office ɗin babba ne yana da girma.

Idanun shugabar ne suka sauka a kan Afrah, da sauri ta tashi tsaye daga kan tebur ɗinta, idanun Baba Habiba suka sauka a kan Afrah idanu Baba Habiba ta zaro dan zuwa lokacin gabaɗaya tsoro sun bayyana ƙarara a kan fuskarta.Idanun Ruƙayya Afrah suka sauka a kan fuskar  Ridallah da ke kallon Ruƙayyar babu abin da ya rabasu sai shekaru da Ruƙayyar ta fi Ridallah amma babu wani banbanci tsakaninsu...

ALAƘAR YARINTATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang