PROLOGUE ( TEASER)

Start from the beginning
                                    

Ji tayi zafi ya na keto mata Daddy Senator ne yace " Yaya Tijjani Farhan kuma...?". Cikin isa ya d'aga masa hannu alamun yayi shiru hakan yasa ya had'iye kalmomin shi. " Farhan is not a bad choice right?!". Baban ya tambaya ya na kallon ta.

Ji tayi harshen ta yayi mata nauyi, kalmomin kuma sun tsere tamfar bebiya. Matsowa yayi ya kama k'afar Baban cikeda zubda makaman ikon shi yace " Baba kayi hak'uri, kar ka aura mata Farhan don Allah ".

Ture shi yayi yana cewa " I've made my choice, ruwanka ka amince ko akasin hakan. As long as shi ya amince, I know ma ba zai k'i ba". A take kukan Zulfaa ya cika d'akin hakan yasa hankalin kowa ya koma kanta.

Abie yace " Ke wata kalan sakarya ce, zaki sawa mutane ihu haka?". Amsawa tayi da cewa " Haba Abie, ya zaai a had'a Abban Suhail da Bloody?!, Bloody ta fa!!".Cikeda hargowa yace " Haramun ne hakan?" bata iya magana ba sai sake k'ara sautin kukan ta da tayi.  Abbu ne ya amsa da " haba yaya, ai ta mayi k'ok'ari don Allah Yaya Tijjani kar ai wannan had'in".

A take Abba yace " Ba wanda ya isa ya hana wannan had'in ". Nan fa ta mik'e tana cewa " Na shiga uku na, Wayyo Allahna!!". A take Abie ya mik'e yaja hannunta har zuwa k'ofa bud'ewa yayi ya tura ta. Tareda rufewa ya dawo wurin shi ya na zama.

Sake matsawa yayi gaban Abbu yana cewa " Abbu ka sa baki please,,,,this will do more harm than good!!, Don't marry off Jewel to Farhan please". A take Abba yace " sake masa k'afa, sakaran yaro kawai ko ba Jewel ba in banda ma baka da kunya har Yusuf zaka kalla kace masa yasa baki?!, sake mai k'afa nace ".

Sake mai k'afa yayi ya matso gabanta " Jewel ki yafe ni,,, I promise you I'll change, in ma baki so na yanzu naji na amince amma please don't marry Farhan wallahi zan iya mutuwa if you do so!". Kawar da fuska tayi ta na mai jin kamar ta janye kalmominta amma shaidan sai bijiro mata da komai yake yi tamkar yanzu komai yake faruwa.

Cikeda cushewar voice tace " ba ka isa ba!!, Ba zan tab'a bijirewa iyayena saboda kai ba......" A take Farhan da tun d'azu yake zaune kamar mutum-mutumi ya katse ta da cewa " Ashe ko zaki mutu babu aure in dai har ni zaki aura Wallahi.......Guy har abada bazan iya aurenta ba ko da kuwa baka da rai ne balle da rayuwar ka,,tashi daga gabanta in sunga dama su jik'a ta su sha itama in ta ga dama ta auri all the guys in the family.....mtswww kai kake lallab'ata ma......."

''Farhan!!" Mom d'in shi ta furta sai dai bai ko kalleta ba yace " Baba kayi hak'uri, but with due respect I can't marry her a samu wani wanda ke ra'ayi!!" Daga haka ya ja hannun Islam d'in suka fita.

Murmushi Abbu yayi ya na kallonta. Ita ko ji take tamkar k'asa ta tsage ta shige take ji. Yau ita Lelen Yerwa ne ake gwanjonta kamar wata tsohuwar langa?!, wannan wani irin cin mutunci ne. Ba kowa bane ya ja mata sai Islam da banzar zuciyarta da ta sanya har ta sallama kanta gareshi a shekarun baya. Wanda har da k'uruciya a ciki, yanzu kam ba da bane.

Abbu yace " sai ki tashi kema ki b'ace mana da gani shashan banza kawai!". A tsorace ta tashi ta nufi k'ofa ko waiwaye babu. D'akin Hajja ta nufa tana kuka tamkar ance Yasen ya rasu.
Yau ne take jin maraicin rasuwar Hajja ta dawo mata sabuwa fil, ta tabbatar inda Hajja tana nan ba wanda ya isa yai wa lelenta dole.

A can hall d'in kuwa bayan fitan ta Baba Tijjani yace " a yau zan aurar da ita ga wanda nake raayi, na lura cewa kanta ya na kulle da komai wanda ba laifinta bane but laifin shi wanda ni da ku mun san da hakan..but ina son muyi hak'uri ba ya a tsarina yi mata auren dole amma bamu da yanda zamuyi....." Nisawa yayi kafin ya d'aura El-Sadeeq yace " But Baba da hak'ura akayi da maganar auren har zuwa sanda zata sauko da kanta".

Murmushi Baban yayi Abba kuma yace " Tabbas haka maganar ka take Ba'anah, Yaya please a dakatar da auren nan". Kallon su yayi da kyau ya san ba zasu tab'a yarda da abunda zai cutawa lele ba shima kuma hakan ne.

But ya tabbatar za suyi alfahari da zab'in da zai mata. And he's sure that ba zasu taba kaicon zab'in shi ba. Ko da ko bai da rayuwa ne, a take yace " kayyah!, a gaban kowa ta bani zab'i kuma ni zan tabbatar da aurenta a yau d'innan ko don in cika alk'awarin da nayi ga Hajja,,,,,,,,,Ku matan nan ku shiga cikin gida kai kuma Hafeez aje a fiddo kayan d'aurin aure".

A take mata da yara suka fice daga hall d'in. Maza kawai aka bari a ciki inda aka fara shigo da kayan d'aurin aure na al'adar kanuri. Ganin sun gama shigo da komai ne ya sa Baba Tijjani bud'e 'yar jakar hannun shi. A take sisin zinari ya bayyana, duban Abba Adam yayi yace " Ka zama waliyin ango ni ne waliyin Lele ku zaku zama shedu zaa d'aura auren ta a yau in muna numfashi......."

Daga haka yayi shiru, shirun da ya haifar da damuwa da kuma firgici a zuciyoyin mazan da ke wurin. Musamman da ya kasance Abba Adam ne zai d'aura auren. Zaheer a take jikin shi ya fara rawa tunanin shi ko da shi za a d'aura auren, kasancewar tunda Bahaja ta rasu bai sake aure ba. Shiko Safwan kamar ya ruga yake ji don akwai jik'ak'ka tsakanin su da Baba Tijjani akan aure.  Suma haka sauran mazan da suke parlorn kowa yana tsoron ace da shi ne!!.....

A cikin gida kuwa Suliem ce ta shiga wurin ta. Tana zama tace " Lovie ki kwantar da hankalin ki, Baba ya tabbatar da ba zaki auri Yaa Islam ba,,,,and he mean it ". A hankali tace " Mom Aleenah to da wa zai d'aura min auren,,,,,,innalillahi me zai sa ba zaa barni da shi mu sasanta ba". Hannun suliem dake bin ta da kallon you are sick tayi tace " In suka aura min wani ba shi ba mutuwa zan yi wallahi ".

Cewa tayi " me yasa baki sanar da hakan a idanun kowa ba, meyasa kika zab'i zaluntar kan ki akan abunda kike so,,,shin ya zaki bari shaidan yai miki gangi har ki rasa yin tunanin makomar ki,,,,,,shin kina tunanin cewa akwai inda zakije da zai fi nan inda yake ne?".

Hawayen da take faman yi ne ya sake zubar mata a rikice tace " Ya zanyi Mom Aleenah?" Kafin ta bata amsa message ya shigo wayarta " Babe me yasa kika zab'i cutar mana da zukata a dai-dai lokacin nan?!, shin yaushe kika zama mara tausayi har haka?!, me yasa ba zaki iya yafe min laifukan da na aikata a bisa rashin sani ba?, well gashi kin ja mana one word could have change everything but kin zab'i wahal da zukatan mu,,,,,  yanzu kuma bakin alk'alami ya bushe ni dake mun rabu da juna rabuwa ta har abada............"

Kuka ta saka tana cewa " Na shiga uku,,,,barin je wurin Baba Tijjani...." a dai dai lokacin ne Mommy Hafsah ta shigo d'akin da bag da kuma kud'i tace " ga shi nan an d'aura aurenki,,,,,ruwanki kiyi biyayya da hakan ruwanki ki bijire sai dai ina miki bushara da cewa duk abunda kika gani toh da kanki zaki koka ba wani ba......" Daga haka ta juya ta fice ba tare da lura da halin da ta shiga ba.

Suliem ce ta sanya ihu tana cewa " Leleeeee!!" Sakamakon kifawar da tayi babu ko alamun rai tare da ita. Hakan ne ya jawo hankalin mutanen da ke parlorn kusa da su har suka shigo ciki. Sai dai duk wanda ya ganta sai firgicin halin da suka shiga ya kama su, a take drs dake wurin suka fara bata kulawar da ta dace da ita har akai nasarar samo numfashin ta da k'yar............

Nisfu Deeniy!!!.....littafine da ya ginu akan soyayya, rikitacciyar soyayya mai cikeda chakwakiyar zumunci... Kar ku yadda ayi babu ku.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now